Masarawa Mutane ne, ba Allah Ba
1 Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra’ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.
2 Ya san abin da yake yi! Zai aika da bala’i. Zai ci gaba da niyyarsa ta hukunta wa mugaye duk da masu kiyaye su.
3 Masarawa su ba Allah ba ne, mutane ne kurum! Dawakansu ba su wuce ikon ɗan adam ba! Sa’ad da Ubangiji zai matsa, ƙaƙƙarfar al’umma za ta marmashe, al’ummar da aka yi wa taimako kuma za ta fāɗi. Dukansu za su hallaka.
4 Ubangiji ya ce mini, “Kamar dai makiyaya ba za su iya tsoratar da zakin da ya kashe dabba ba, kome irin tsawa da ihun da suka yi, haka ni ma, ba abin da zai iya hana ni, ni Ubangiji Mai Runduna, in kiyaye Dutsen Sihiyona.
5 Kamar yadda tsuntsu yake shawagi a kan sheƙarsa don ya kiyaye ‘ya’yansa, haka ni, Ubangiji Mai Runduna, zan kiyaye Urushalima in kāre ta kuma.”
6 Allah ya ce, “Jama’ar Isra’ila, kun yi mini zunubi, kuna kuwa yin gāba da ni. Amma yanzu ku komo wurina!
7 Lokaci zai yi da dukanku za ku watsar da gumakan da kuka yi na azurfa da na zinariya.
8 Assuriya za ta hallaka cikin yaƙi, amma ba ta wurin ikon mutum ba. Assuriyawa za su gudu daga bakin dāga, za a mai da majiya ƙarfinsu bayi.
9 Sarkinsu zai tsere saboda razana, shugabannin sojojinsu kuwa za su firgita, har su watsar da tutocinsu na yaƙi.” Ubangiji ne ya faɗa, Ubangiji da ake yi wa sujada a Urushalima, wanda kuma wutarsa tana ci a can domin hadayu.