Waƙar Dogara ga Kiyayewar Ubangiji
1 Rana tana zuwa da jama’a za su raira wannan waƙa a ƙasar Yahuza.
Birni ƙaƙƙarfa ne,
Allah kansa yake tsare garukansa!
2 A buɗe ƙofofin birnin,
A bar amintacciyar al’umma ta shiga,
Al’ummar da jama’arta take aikata abin da yake daidai.
3 Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji,
Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi,
Waɗanda suke dogara gare ka.
4 Ku dogara ga Ubangiji har abada.
Zai kiyaye mu kullayaumin.
5 Ya ƙasƙantar da masu girmankai,
Ya hallaka ƙaƙƙarfan birnin da suke zaune ciki,
Ya rusa garunsa ƙasa.
6 Waɗanda aka zalunta, a kansa suke tafiya yanzu,
Suna tattaka shi da ƙafafunsu.
7 Ka sa hanyar mutanen kirki ta yi sumul,
Hanyar da suke bi ta yi bai ɗaya,
8 Muna bin nufinka, muna sa zuciya gare ka.
Kai kaɗai ne bukatarmu.
9 Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya.
Sa’ad da kake yi wa duniya da jama’arta shari’a
Dukansu za su san yadda adalci yake.
10 Ko da yake kana yi wa mugaye alheri,
Duk da haka ba su taɓa koyon abin da yake na kirki ba.
Har a nan ma, a ƙasar adalai,
Suna ta aikata kuskure,
Sun ƙi ganin girmanka.
11 Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba.
Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala,
Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya.
Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama’arka.
12 Kai za ka wadata mu, ya Ubangiji,
Duk abin da muka iya yi daga gare ka ne.
13 Ya Ubangiji Allahnmu, waɗansu sun mallake mu,
Amma kai kaɗai ne Ubangijinmu.
14 Yanzu kuwa sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba,
Kurwarsu ba za ta tashi ba,
Domin ka hukunta su, ka hallaka su.
Ba wanda zai ƙara tunawa da su.
15 Ya Ubangiji, ka sa al’ummarmu ta yi ƙarfi,
Ka faɗaɗa karkararta a kowane gefe,
Wannan kuwa ya sa ana girmama ka.
16 Ka hukunta jama’arka, ya Ubangiji,
A cikin azaba sun yi addu’a gare ka.
17 Kai ne, ya Ubangiji, ka sa muka yi kuka,
Kamar macen da take naƙuda tana kuka da azaba.
18 Muna shan azaba da wahala,
Amma ba abin da muka haifa.
Ba mu ciwo wa ƙasarmu nasara ba,
Ba abin da muka kammala!
19 Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa!
Jikunansu za su sāke rayuwa!
Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu
Za su farka, su yi waƙa don farin ciki!
Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya,
Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.
20 Jama’ata, ku shiga gidajenku, ku kukkulle ƙofofi, ku ɓoye kanku ɗan lokaci, kafin Allah ya huce daga fushinsa.
21 Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama’arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.