Annabci a kan Taya da Sidon
1 Wannan shi ne jawabi a kan Taya.
Ku yi hargowa ta baƙin ciki, ku matuƙan jiragen ruwan teku! An lalatar da tashar jiragen ruwan garinku na Taya. Gidajenta da gaɓarta sun rurrushe. Sa’ad da jiragen ruwanku suka komo daga Kubrus za ku ji labarin.
2 Ku yi kuka ku fataken Sidon! Kun aika da mutane
3 a hayin teku don su yi muku saye da sayarwa na hatsin da ake nomawa a Masar, su yi hulɗa da dukan sauran al’umma.
4 Birnin Sidon, ke abar kunya ce! Teku da manyan zurfafan ruwaye sun yanke hulɗa da ke, sun ce, “Ban taɓa haihuwar ‘ya’ya ba, ban taɓa goyon ‘ya’ya mata ko maza ba.”
5 Har Masarawa ma za su firgita su razana, sa’ad da suka ji, cewa an hallakar da Taya.
6 Ku yi ruri da baƙin ciki, ku jama’ar bakin teku, ku yi ƙoƙari ku tsere zuwa Tarshish!
7 Ya yiwu kuwa a ce wannan Taya ce birnin farin ciki, wadda aka kafa ta tuntuni? Wannan kuwa ita ce birnin da yake aikawa da mutane hayin teku su kafa nahiyoyi?
8 Wane ne wannan wanda ya shirya ya aukar wa Taya da wannan duka, wannan muhimmiyar alkarya, wadda fatakenta hakimai ne, waɗanda ake ɗaukaka su fiye da sauran mutane a duniya?
9 Ubangiji Mai Runduna ne ya shirya wannan! Ya shirya haka ne don ya kawo ƙarshen girmankanta saboda abin da suka aikata, don ya ƙasƙantar da manyan mutanenta.
10 Ku je ku nomi ƙasarku jama’ar nahiyoyin Tarshish! Ba wanda zai ƙara kiyaye ku.
11 Ubangiji ya miƙa dantsensa a kan tekun, ya hamɓarar da mulkoki. Ya umarta a lalatar da manyan biranen ciniki na Taya.
12 Birnin Sidon, farin cikinki ya ƙare. Ana zaluntar jama’arki, ko da za su tsere zuwa Kubrus duk da haka ba za su zauna lafiya ba.
13 (Mutanen Babila ne, ba na Assuriya ba, waɗanda suka bar namomin jeji su murƙushe Taya. Mutanen Babila ne suka gina hasumiya, suka ragargaza kagarar Taya suka bar birnin kango.)
14 Ku yi hargowar baƙin ciki ku matuƙan jiragen teku! An hallaka birnin da kuke dogara gare shi.
15 Lokaci yana zuwa da za a manta da Taya har shekara saba’in, gwargwadon kwanakin sarki. Bayan waɗannan shekaru kuma, Taya za ta yi waƙa irin ta karuwa, cewa
16 “Ɗauki garayarki, kewaya cikin gari,
Ayya, an manta da karuwa!
Yi kiɗa, sāke raira waƙoƙinki,
Don ki komo da masoyanki.”
17 Bayan shekara saba’in ɗin, Ubangiji zai bar Taya ta koma a kan cinikinta na dā, za ta ba da kanta ijara ga dukan mulkokin duniya.
18 Kuɗin da ta samu ta kasuwanci za a keɓe wa Ubangiji. Ba za ta tara wa kanta ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada su za su yi amfani da kuɗinta don su saya wa kansu abinci da sutura da suke bukata.