Annabci a kan Babila
1 Wannan shi ne jawabi a kan Babila.
Kamar yadda guguwa take tasowa daga hamada, haka masifa za ta auko daga wata ƙasa mai razanarwa.
2 Na ga wahayi na waɗansu mugayen abubuwa, wato na cin amana da hallakarwa.
Rundunar sojojin Elam, ku kama yaƙi! Rundunar sojojin Mediya ku kewaye birane da yaƙi. Allah zai kawar da wahalar da Babila ta haddasa.
3 Abin da na gani, da abin da na ji a wahayin, ya razanar da ni, ya sa ni cikin azaba kamar ta mace mai naƙuda.
4 Kaina ya yi yum, ina ta rawar jiki saboda tsoro. Ina ta marmarin maraice ya yi, amma bai kawo mini kome ba, sai razana.
5 A wahayin na ga an shirya biki, an shisshimfiɗa darduma inda waɗanda aka gayyata za su zauna. Suna ci suna sha. Farat ɗaya sai aka ji umarni cewa, “Jarumawa! Ku shirya garkuwoyinku.”
6 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sa mai tsaro, ka faɗa masa ya riƙa ba da labarin abin da ya gani.
7 Idan ya ga mutane biyu biyu suna zuwa a kan dawakai, waɗansu kuma a kan raƙuma da jakuna, ka faɗa masa ya lura da su sosai.”
8 Mai tsaro ya ce, “Ya mai girma, ina ta tsaro dare da rana a wurin da aka sa ni.”
9 Farat ɗaya sai ga su sun zo! Suna tafe a kan dawakai biyu biyu. Sai mai tsaro ya ba da labari cewa, “Babila ta fāɗi! Dukan gumakan da suke yi wa sujada an ragargaza su har ƙasa.”
10 Ya jama’ata, an buga ku kamar yadda ake bugun alkama a masussuka. Amma yanzu na kawo muku albishir wanda na ji daga wurin Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila.
Annabci a kan Edom
11 Wannan shi ne jawabi a kan Edom.
Wani daga Edom ya kira ni ya ce, “Ya mai tsaro, gari ya kusa wayewa? Ka gaya mini har sai yaushe zai waye?”
12 Sai na amsa na ce, “Gari zai waye, amma za a sāke yin dare! Idan kana so ka sāke yin tambaya, sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”
Annabci a kan Arabiya
13 Wannan shi ne jawabi a kan Arabiya.
Ya ku jama’ar Dedan, waɗanda ayarorinku suka yi zango a ƙasar Arabiya wadda take faƙo,
14 ku ba jama’a waɗanda suka zo gare ku masu jin ƙishi ruwa su sha. Ya ku jama’ar ƙasar Tema, ku ba ‘yan gudun hijira abinci.
15 Mutane suna gudu don su tsere wa takuban da za su kashe su, da bakkunan da za su harbe su, su kuma tsere wa dukan hatsarorin yaƙi.
16 Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Saura shekara ɗaya tak girman kabilar Kedar zai ƙare.
17 Jarumawan Kedar su ne maharba, amma sai kaɗan za su ragu daga cikinsu, ni, Ubangiji Allah na Isra’ila, na faɗa.”