Annabci a kan Dimashƙu
1 Wannan shi ne jawabi a kan Dimashƙu.
Ubangiji ye ce, “Dimashƙu ba za ta ƙara zama birni ba, za ta zama tsibin kufai ne kawai.
2 Za a watse a bar biranen Suriya har abada. Za su zama makiyayar tumaki da shanu. Ba wanda zai tsoratar da su.
3 Ba za a kāre Isra’ila ba, Dimashƙu kuma za ta rasa ‘yancinta. Suriyawan da suka ragu za su sha wulakanci kamar mutanen Isra’ila. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”
Hukunci a kan Isra’ila
4 Ubangiji ya ce, “Rana taba zuwa, ran da girman Isra’ila zai ƙāre, fatara za ta gāje gurbin dukiyarsu.
5 Isra’ila za ta zama kamar gonar da aka girbe, aka yanke amfaninta, ta zama marar kome kamar gona a kwarin Refayawa sa’ad da aka ɗebe amfaninta. Mutane kima ne kurum za su ragu.
6 Isra’ila kuma za ta zama kamar itacen zaitun wanda aka karkaɗe ‘ya’yansa, aka bar biyu ko uku kawai a ƙwanƙolin itacen, ko kuma aka bar huɗu ko biyar a rassansa. Ni Ubangiji Allah na Isra’ila, na faɗa.”
7 A wannan rana, mutane za su juyo neman taimako ga Mahaliccinsu, Allah Mai Tsarki na Isra’ila.
8 Ba za su ƙara dogara ga bagaden da suka yi da hannuwansu ba, ko kuwa su dogara ga ayyukan hannuwansu, ko keɓaɓɓun wuraren da suke wa gumaka sujada, ko bagadai don ƙona turare.
9 A wannan rana, za a watse a bar birane masu ƙaƙƙarfar kagara su zama kufai a jeji kuwa kamar rassan da aka watsar a gaban jama’ar Isra’ila.
10 Isra’ila, kin manta da Allah wanda ya kuɓutar da ke, wanda ya kāre ki kamar babban dutse. Kin dasa wa kanki lambuna masu ni’ima don ki yi wa gumaka sujada.
11 Amma ko da za su toho su yi fure a safiyar da kuka dasa su, duk da haka ba za a girbe kome ba. Wahala ce kaɗai da azabar da ba ta warkuwa.
An Ci Al’ummai, Abokan Gāba
12 Al’ummai masu iko sun hargitse suna ta rugugi kamar rurin teku, kamar karon manyan raƙuman ruwa.
13 Al’ummai sun ci gaba kamar sukuwar raƙuman ruwa, amma Allah ya tsauta musu suka kuwa janye, aka kora su kamar ƙura a gefen dutse, kamar kuma tattaka a cikin guguwa.
14 Da maraice sukan ba da tsoro, amma da safe ba su! Wannan ita ce ƙaddarar duk wanda ya washe ƙasarmu!