Takama Gāba da Sarkin Babila
1 Ubangiji zai sāke yi wa jama’arsa Isra’ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su.
2 Al’ummai da yawa za su taimaki jama’ar Isra’ila su koma ƙasarsu wadda Ubangiji ya ba su. A can sauran al’umma za su yi wa Isra’ila hidima kamar bayi. Waɗanda suka kama Isra’ilawa a dā yanzu Isra’ilawa za su kama su. Jama’ar Isra’ila za ta mallaki waɗanda suka taɓa zaluntarsu.
3 Ubangiji Allah kuwa zai sawwaƙe wa jama’ar Isra’ila azaba da wahala da suke sha, daga kuma aikin da aka tilasta su su yi.
4 Sa’ad da ya aikata wannan za su yi wa Sarkin Babila ba’a.
Za su ce, “Mugun sarkin ya fāɗi, ba zai ƙara zaluntar kowa ba!
5 Ubangiji ya ƙare mulkin mugun,
6 wanda yake zaluntar jama’a a husace, bai taɓa daina tsananta wa al’ummai ba, wanda ya ci da yaƙi.
7 Yanzu magana ta ƙare, duniya duka tana jin daɗin hutawa da salama. Kowa na ta raira waƙar murna.
8 Itatuwan fir da itatuwan al’ul na Lebanon suna murna da faɗuwar sarkin! Ba wanda zai tasar musu da sara!
9 “Lahira tana shirye-shiryen yi wa Sarkin Babila maraba. Fatalwan waɗanda suka yi iko a duniya suna kaiwa suna komowa a hargitse. Fatalwan sarakuna suna tashi daga gadajen sarautarsu.
10 Dukansu suka yi kira gare shi, suka ce, ‘Ashe, kai ma rarrauna ne kamarmu! Ka zama ɗaya daga cikinmu.
11 Dā ana ɗaukaka ka da kaɗe-kaɗen garaya, amma yanzu ga ka a lahira! Kana kwance a kan tsutsotsi. Kana rufe da tsutsotsi!’ ”
12 Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al’ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa.
13 Ka yi niyyar hawan sama, ka sa gadon sarautarka a kan taurari mafi nisa. Ka zaci za ka zauna kamar sarki a kan dutsen nan na arewa, inda alloli suke tattare.
14 Kai ka ce za ka hau can bisa kan taurari, ka zama kamar Mai Iko Dukka.
15 Amma a maimakon haka an saukar da kai a sashe mafi zurfi a lahira.
16 Matattu za su zura maka ido su yi mamaki. Za su yi tambaya su ce, “Ashe, ba wannan mutum ba ne ya girgiza duniya, ya sa mulkoki suka jijjigu?
17 Wannan shi ne wanda ya hallaka birane, ya mai da duniya hamada, wanda bai taɓa sakin ɗaurarru ko ya bar su su koma gida ba?”
18 Dukan sarakunan duniya suna kwance a cikin manya manyan kaburburansu,
19 amma kai ba ka sami kabari ba, jefar da gawarka aka yi don ta ruɓe. Aka hautsuna gawarka da gawawwakin mayaƙan da aka kashe cikin yaƙi. Tare da su aka jefa ka gangaren dutse, aka tattake.
20 Ba za a binne ka kamar sauran sarakuna ba, saboda ka lalata da ƙasarka, ka karkashe mutanenka. Daga cikin mugayen iyalinka ba wanda zai ragu.
21 A fara yanyanka su! ‘Ya’ya maza na sarkin nan za su mutu saboda zunuban kakanninsu. Daga cikinsu ba wanda zai taɓa mallakar duniya, ko ya cika ta da birane.
Allah Zai Hallaka Babila
22 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan fāɗa wa Babila da yaƙi, in lalata ta, ba abin da zan bari, ko yara, ba wanda zai ragu. Ni, Ubangiji, na faɗi wannan.
23 Zan su Babila ta zama fadama, mujiyoyi za su zauna a can. Zan kuwa share Babila da tsintsiyar da za ta share kome. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.”
Allah Zai Hallaka Assuriya
24 Ubangiji Mai Runduna ya rantse, ya ce, “Abin da na riga na shirya, haka zai faru. Abin da na yi niyyar yi, za a yi.
25 Zan hallaka Assuriyawa a ƙasata ta Isra’ila, in tattake su a kan duwatsuna. Zan ‘yantar da jama’ata daga karkiyar Assuriyawa, daga nauyin da suka tilasta musu su ɗauka.
26 Abin da na shirya zan yi wa duniya, shi ne in miƙa hannuna domin in hukunta wa al’ummai.”
27 Ubangiji Mai Runduna ne ya ƙudura ya yi wannan, ya miƙa dantsensa don ya yi hukunci, ba kuwa mai iya hana shi.
Annabci a kan Filistiya
28 Wannan shi ne jawabin da aka yi shelarsa a shekarar da sarki Ahaz ya rasu.
29 Ku mutanen Filistiya, sandan da ake dūkanku da shi ya karye, amma kada wannan ya zamar muku dalilin murna. Gama idan wani maciji ya mutu, wani mafi mugunta zai maye gurbinsa. Ƙwan maciji yake ƙyanƙyashe maciji mai tashi sama!
30 Ubangiji zai zama makiyayin jama’arsa wadda take talauce, zai kuma sa su zauna lafiya. Amma ku Filistiyawa, zai aukar muku da matsananciyar yunwa, wadda ba za ta bar ko ɗayanku da rai ba.
31 Ku yi kururuwa, ku yi kuka na neman taimako, dukanku biranen Filistiya! Ku razana dukanku! Ƙurar da ta murtuke tana zuwa daga arewa, mayaƙa ne, ba kuwa matsorata a cikinsu.
32 Ƙaƙa za mu amsa wa manzannin da suka zo gare mu daga Filistiya? Za mu faɗa musu, cewa Ubangiji ya tabbatar da Sihiyona, jama’arsa da suke shan wahala kuwa za su sami zaman lafiya a can.