Annabci a kan Babila
1 Wannan shi ne saƙo a kan Babila, wanda Ishaya ɗan Amoz ya karɓa daga wurin Allah.
2 A kan tudun da yake faƙo ka kafa tutar yaƙi, ka ta da murya ka ba mayaƙa umarni, ka ɗaga hannu, ka ba su alamar kama yaƙi a ƙofofin birni mai alfarma.
3 Ubangiji ya kira mayaƙansa masu jin kansu, masu ƙarfin zuciya, domin su yi jahadi, su hukunta wa waɗanda suke fushi da su.
4 Ji hayaniyar da ake yi a duwatsu da amon babban taron jama’a. Amon al’ummai da mulkoki suna tattaruwa. Ubangiji Mai Runduna yana shirya mayaƙansa domin yaƙi.
5 Suna zuwa daga manisantan ƙasashe, daga kan iyakokin duniya. Ubangiji yana zuwa da fushinsa, ya lalatar da dukan ƙasar.
6 Ku yi ihu saboda shan azaba, ranar Ubangiji ta yi kusa. Ranar da Mai Iko Dukka zai kawo hallaka.
7 Hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.
8 Dukansu za su firgita, azaba za ta ci ƙarfinsu kamar mace wadda take shan azabar naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu za su cika da kunya.
9 Ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana ce ta zafin fushinsa. Za a mai da duniya jeji, a hallaka kowane mai zunubi.
10 Kowane tauraro, da kowace ƙungiyar taurari za su daina ba da haske. Rana za ta yi duhu lokacin da ta fito, wata kuwa ba zai ba da haske ba.
11 Ubangiji ya ce, “Zan kawo masifa a duniya. Zan hukunta dukan mugaye saboda zunubansu. Zan ƙasƙantar da kowane mai girmankai. Zan hukunta kowane mai izgili da mai mugunta.
12 Sauran da suka ragu za su fi zinariya wuyar samuwa.
13 Zan sa sammai su yi rawar jiki, duniya kuwa za a girgiza ta a inda take, a wannan rana sa’ad da ni, Ubangiji Mai Runduna, na nuna fushina.
14 “Baƙin da yake zaune a Babila za su gudu zuwa ƙasashensu, suna a warwatse kamar bareyin da suke tsere wa maharbansu, kamar tumakin da ba su da makiyayi.
15 Duk wanda aka kama za a soke shi ya mutu.
16 Sa’ad da suke cikin halin ƙaƙa naka yi, za a fyaɗa ‘ya’yansu ƙasa, su mutu. Za a washe gidajensu, a yi wa matansu faɗe.”
17 Ubangiji ya ce “Ina zuga mutanen Mediya, don su faɗa wa Babila da yaƙi. Ba su kula da azurfa ba, ba kuwa za a jarabce su da zinariya ba.
18 Da bakkuna da kibansu, za su karkashe samari. Ba za su nuna jinƙai ga jarirai ba, ba kuwa za su ji tausayin ‘yan yara ba.
19 Daular Babila ita ce mafi kyau duka, abin fāriya ce ga jama’arta. Amma ni Ubangiji, zan kaɓantar da ita kamar yadda na yi da Saduma da Gwamrata!
20 Ba wanda zai ƙara zama a cikinta. Ba wani Balaraben da yake yawo da zai kafa alfarwarsa a can. Ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.
21 Za ta zama wurin zaman namomin jejin hamada, inda mujiyoyi za su yi sheƙarsu. Jiminai za su zauna a can, awakin jeji za su yi ta warnuwa a cikin kufanta.
22 A hasumiyarta da fādodinta za a ji amsar ihun koke-koken kuraye da na diloli. Lokacin Babila ya yi! Kwanakinta sun kusa ƙarewa!”