Mulkin Adalci na Ɗan Yesse
1 Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.
2 Ikon Ubangiji zai ba shi hikima,
Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa.
Zai kuwa san nufin Ubangiji, ya kuma yi tsoronsa,
3 Zai ji daɗin yin hidimarsa.
Ba zai yi shari’ar ganin ido ko ta waiwai ba.
4 Zai yi wa matalauta shari’a daidai.
Zai kuma kāre hakkin masu tawali’u.
Bisa ga umarninsa za a hukunta ƙasar,
Mugaye za su mutu.
5 Zai yi mulkin mutanensa da adalci da mutunci.
6 Kyarketai da tumaki za su zauna tare lafiya.
Damisoshi za su kwanta tare da ‘yan awaki.
‘Yan maruƙa da kwiyakwiyan zaki za su yi kiwo tare,
Ƙananan yara ne za su lura da su.
7 Shanu da beyar za su yi kiwo tare,
‘Yan maruƙansu da kwiyakwiyansu za su kwanta lafiya.
Zaki zai ci ciyawa kamar sā.
8 Jariri zai yi wasa kusa da maciji mai mugun dafi
Amma ba zai cuta ba.
9 A kan Sihiyona, dutse tsattsarka,
Ba wani macuci ko mugu.
Ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji
Kamar yadda tekuna suke cike da ruwa.
Masu Zaman Dole Sun Komo da Nasara
10 Rana tana zuwa sa’ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al’umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.
11 A wannan rana Ubangiji zai sāke zuwa, ya nuna ikonsa. Zai komo da mutanensa gida waɗanda suka ragu a Assuriya, da Masar, da ƙasashen Fatros, da Habasha, da Elam, da Babila, da Hamat, da kuma ƙasashen bakin gāɓa da na tsibiran teku.
12 Ubangiji zai ɗaga tuta, alama ce ta nuna wa sauran al’umma, ya sāke tattara jama’ar Isra’ila da ta Yahuza waɗanda aka warwatsa, ya sāke komo da su daga kusurwoyi huɗu na duniya.
13 Masarautar Isra’ila ba za ta ƙara jin kishin Yahuza ba, Yahuza kuma ba za ta zama abokiyar gābar Isra’ila ba.
14 Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma, su washe mutanen da suke wajen gabas. Za su ci nasara a kan mutanen Edom da na Mowab, jama’ar Ammon kuwa za su yi musu biyayya.
15 Ubangiji zai kawo iska mai zafi wadda za ta busar da Kogin Nilu, da na Yufiretis. Zai bar ƙananan rafuffuka bakwai ne kaɗai, don kowa da kowa ya taka ya haye.
16 Za a yi babbar karauka daga Assuriya domin sauran mutanen Isra’ila da suka ragu a can, kamar yadda aka yi wa kakanninsu sa’ad da suka bar Masar.