1 Kun shiga uku! Kuna kafa dokokin rashin gaskiya don ku zalunci jama’ata.
2 Ta haka kuke hana wa talakawa hakkinsu, kuna kuma ƙin yi musu shari’ar gaskiya. Ta haka kuke ƙwace dukiyar gwauraye, wato matan da mazansu suka rasu, da ta marayu.
3 Me za ku yi sa’ad Allah zai hukunta ku? Me za ku yi kuma sa’ad da ya kawo muku masifa daga wata ƙasa mai nisa? Ina za ku sheƙa neman taimako? A ina kuma za ku ɓoye dukiyarku?
4 Za a kashe ku a yaƙi, ko a kwashe ku, kamammun yaƙi. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.
Allah Zai Sarrafa Sarkin Assuriya
5 Ubangiji ya ce, “Assuriya! Ina yin amfani da Assuriya kamar kulki don in hukunta waɗanda nake fushi da su.
6 Na aiki Assuriya ta faɗa wa al’ummar da ba ta tsoron Allah, da yaƙi, wato jama’ar da ta sa na yi fushi. Na aike su su yi waso su yi sata, su tattake jama’a kamar ƙura a tituna.”
7 Amma Sarkin Assuriya yana da nasa mugayen shirye-shirye da zai yi. Ya yi niyya ya hallaka al’ummai masu yawa.
8 Ya yi kurari, ya ce, “Kowane shugaban mayaƙana sarki ne!
9 Na ci biranen Kalno da na Karkemish. Na ci biranen Hamat da na Arfad. Na kuma ci Samariya da Dimashƙu.
10 Na miƙa hannuna don in hukunta wa waɗannan mulkoki masu bauta wa gumaka, wato gumakan sun yi yawa fiye da na Urushalima, da na Samariya.
11 Na hallaka Samariya da dukan gumakanta, haka ma zan yi wa Urushalima da siffofin da suke yi wa sujada a can.”
12 Ubangiji ya ce, “Sa’ad da na gama abin da nake yi a kan Dutsen Sihiyona da cikin Urushalima, zan hukunta Sarkin Assuriya saboda dukan kurarinsa da girmankansa.”
13 Sarkin Assuriya ya yi kurari ya ce, “Dukan waɗannan ni da kaina na yi su. Ni ƙaƙƙarfa ne, mai hikima, mai wayo. Na kawar da kan iyakokin da suke tsakanin ƙasashen sauran al’umma, na kwashe dukan abin da suka tattara suka adana. Kamar bijimi, haka na tattake mutanen da suke zaune a can.
14 Al’umman duniya kamar sheƙar tsuntsaye suke. Na tattara dukiyarsu, a sawwaƙe kamar yadda ake tattara ƙwai, ba tsuntsun da ya buɗe baki don ya yi mini kuka!”
15 Amma Ubangiji ya ce, “Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma? Ko zarto ya fi wanda yake amfani da shi muhimmanci? Ba kulki yake riƙe da mutum ba, amma mutum yake riƙe da kulki.”
16 Ubangiji Mai Runduna zai aukar da cuta don ya hukunta waɗanda suke ƙosassu yanzu. Za su ji jikinsu na ta ƙuna kamar wuta.
17 Allah da yake hasken Isra’ila, zai zama wuta. Allah, Mai Tsarki na Isra’ila, zai zama harshen wuta, wanda zai ƙone kowane abu rana ɗaya, har da ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya.
18 Jeji mai dausayi da ƙasar noma za a lalatar da su ƙaƙaf, kamar yadda ciwon ajali yake hallaka mutum.
19 Sai ‘yan itatuwa kaɗan za su ragu, ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.
Mutanen Isra’ila Kima ne Za Su Komo
20 Lokaci zai yi sa’ad da jama’ar Isra’ila da suka ragu ba za su ƙara dogara ga al’ummar da ta kusa hallaka su ba. Hakika za su dogara ga Ubangiji Allah, Mai Tsarki na Isra’ila.
21 Kaɗan daga cikin jama’ar Isra’ila za su koma wurin Allahnsu Mai Iko Dukka.
22 Ko da yake yanzu akwai jama’ar Isra’ila da yawa, yawansu kuwa kamar yashin teku, duk da haka, sai kaɗan ne za su komo. An tanada wa jama’a hallaka, sun kuwa cancanci hallakar.
23 Hakika a ƙasar duka, Ubangiji Allah Mai Runduna zai kawo hallaka kamar yadda ya ce zai yi.
Ubangiji Zai Hukunta Assuriya
24 Ubangiji Mai Runduna ya ce wa jama’arsa da suke Sihiyona, “Kada ku ji tsoron Assuriyawa, ko da yake suna wahalshe ku kamar yadda Masarawa suka yi.
25 Saura kaɗan in gama hukuncin da nake yi muku, sa’an nan in hallaka su.
26 Ni, Ubangiji Mai Runduna, zan bulale su da bulalata, kamar yadda na bugi mutanen Madayana a dutsen Oreb. Zan sa Assuriyawa su sha wahala kamar yadda Masarawa suka sha.
27 A lokacin nan zan ‘yantar da ku daga mulkin Assuriya, karkiyarsu ba za ta ƙara zama kaya mai nauyi a wuyanku ba.”
Mahara Sun Faɗa Musu da Yaƙi
28 Magabta suna cikin Ayiyat! Sun bi ta Migron! Sun bar kayayyakinsu a Mikmash!
29 Sun ƙetare hanya suka kwana a Geba! Mutanen Rama suka firgita. Mutanen da suke cikin Gibeya, garin sarki Saul, sun gudu.
30 Ku yi ihu, ku mutanen Gallim! Ku kasa kunne, ku mutanen Layish! Ku amsa, ku mutanen Anatot!
31 Jama’ar Madmena da na Gebim suna gudu su tsira da rayukansu.
32 Yau abokan gāba suna cikin Nob, daga can suke nuna wa Dutsen Sihiyona yatsa, wato wanda yake cikin Urushalima.
33 Ubangiji Mai Runduna zai sa su ragargaje har ƙasa, kamar rassan da aka sassare daga itace. Masu girmankai da manyansu za a datse su ƙasa, a ƙasƙantar da su.
34 Ubangiji zai sassare su har ƙasa kamar yadda ake sassare itatuwa da gatari a tsakiyar kurmi, kamar yadda itatuwa mafi kyau na Lebanon za su fāɗi.