Tunanin Amarya
1 Ina kwance a gadona dukan dare,
Ina mafarki da ƙaunataccena,
Na neme shi, amma ban same shi ba.
Na kira shi, amma ba amsa.
2 Bari in tashi yanzu in shiga birni,
In bi titi-titi, in bi dandali-dandali,
In nemi wanda raina yake ƙauna.
Na neme shi, amma ban same shi ba.
3 Da matsaran da suke kai da kawowa cikin birni suka gan ni,
Sai na tambaye su ko sun ga ƙaunataccena.
4 Rabuwata da matsaran ke nan,
Sai na yi kaciɓis da ƙaunataccena.
Na riƙe shi, ban sake shi ba,
Na kai shi gidanmu, har ɗakin mahaifiyata.
5 Ku ‘yan matan Urushalima,
Ku rantse da bareyi da batsiyoyi,
Ba za ka shiga tsakaninmu ba,
Ku bar ta kurum.
Waƙar Aure
6 Wane ne wannan da yake fitowa daga cikin jeji,
Kamar tunnuƙewar hayaƙi cike da kayan ƙanshi iri iri na fatake?
7 Ai, duba suna ɗauke da karaga wadda aka shirya domin Sulemanu,
Dakarai sittin na kewaye da karagar,
Zaɓaɓɓun sojoji daga cikin Isra’ila.
8 Dukansu gwanayen yaƙi da takobi ne, gogaggu ne na aikin soja,
Kowannensu yana da takobi,
Suna tsaro don kada a hume su da dare.
9 Ana ɗauke da sarki Sulemanu a karagar da aka shirya da itace mafi kyau.
10 An dalaye ginshiƙanta da azurfa,
An rufe ta da zane da aka yi wa ado da zinariya.
An lulluɓe wurin zama da zanen shunayya.
Matan Urushalima sun yi mata irin yayin da ake yi na ƙauna.
11 Matan Sihiyona, ku fito ku ga sarki Sulemanu
Ya sa kambin sarauta,
Wanda uwarsa ta sa masa, a ranar aurensa,
A ranarsa ta murna da farin ciki.