1 Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin samartakarka kafin mugayen kwanaki da shekaru su zo, da za ka ce, “Ba na jin daɗinsu.”
2 Wato lokacin da rana, da haske, da wata, da taurari za su duhunta, gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙar da ruwa.
3 A lokacin nan hannuwanka da suke kāre ka, za su yi makyarkyata, ƙafafunka za su rasa ƙarfi. Haƙora kaɗan za su ragu a bakinka. Idanunka za su duhunta.
4 Bakinka a rufe yake, haƙora ba su tauna abinci. Muryar tsuntsu za ta farkar da kai. Ba za ka iya jin muryar mawaƙa ba.
5 Sa’an nan za ka ji tsoron hawan tudu, tafiya kuma za ta yi maka wuya. Gashin kanka zai furfurce. Za ka ja jikinka. Ba sauran sha’awar mace.
Daga nan sai kabari, masu makoki kuwa su yi ta kai da kawowa a kan tituna.
6 Hakika, ka tuna da Mahaliccinka kafin igiyar azurfa ta katse, ko tasar zinariya ta fashe, ko tulu ya fashe a bakin rijiya, ko igiya ta tsinke a bakin tafki,
7 sa’an nan turɓaya ta koma ƙasa kamar a dā, ruhu kuma ya koma wurin Allah wanda ya ba da shi.
8 Banza a banza, duk banza ne, in ji Mai Hadishi. Duk a banza ne.
Abin da ake Bukata wajen Mutum
9 Saboda hikimar Mai Hadishi ya koya wa mutane ilimi. Ya auna, ya bincika, ya tsara karin magana da lura sosai.
10 Ya nemi kalmomi, ya rubuta su daidai.
11 Kalmomin mutane masu hikima kamar sanduna suke da makiyaya suke amfani da su, su bi da tumaki.
12 Ya ɗana, ka yi hankali, kada ka zarce waɗannan, gama wallafa littattafai ba shi da iyaka, yawan karatu kuma gajiyar da kai ne!
13 Bayan wannan duka, makasudin maganar shi ne, ka yi tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa, gama wannan shi ne wajibi ga mutum.
14 Allah zai shara’anta kowane irin aiki, ko a ɓoye aka yi shi, ko nagari ne, ko mugu.