1 Kada ka yi fāriya a kan abin da za ka yi gobe domin ba ka san abin da zai faru daga yanzu zuwa gobe ba.
2 Bari waɗansu su yabe ka ko da baƙi ne, faufau kada ka yabi kanka.
3 Dutse da yashi suna da nauyi ƙwarai, amma nauyin wahalar da wawa zai haddasa ya fi nasu duka.
4 Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma duk da haka bai kai ga kishi ba.
5 Gara ka tsauta wa mutum a fili da ka bar shi ya zaci ba ka kula da shi ba sam.
6 Aboki aboki ne ko da ya cuce ka, amma maƙiyi ko ya rungume ka kada ka sake!
7 Wanda ya ƙoshi ba zai ko kula da zuma ba, amma wanda yake jin yunwa abinci mai ɗaci zaƙinsa yake ji.
8 Mutumin da ya bar gida yana kama da tsuntsun da ya bar sheƙarsa.
9 Turare da man ƙanshi sukan sa ka ji daɗi, haka abuta ta ainihi takan ƙara maka ƙarfi.
10 Kada ka manta da abokanka, ko abokan mahaifinka. Idan kana shan wahala kada ka nemi taimako wurin ɗan’uwanka. Maƙwabci na kusa yana iya taimakonka fiye da ɗan’uwan da yake nesa.
11 Ɗana, ka zama mai hikima, ni kuwa zan yi farin ciki, zan iya amsa kowace irin sūkar da wani zai yi mini.
12 Mutum mai hankali yakan hango hatsari ya kauce masa, amma mutumin da ba shi da kula, yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
13 Ka karɓe tufar wanda ya zamar wa baƙo lamuni, da kuma wanda ya zama lamunin karuwa.
14 In ka farkar da abokinka da babbar murya tun da sassafe, daidai ne da zaginsa.
15 Mace mai mita kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa.
16 Kaƙa za ka iya sa ta ta kame bakinta? Ka taɓa ƙoƙarin tsai da iska? Ko kuwa ka taɓa ƙoƙarin dintsi mai a tafin hannunka?
17 Daga wurin mutane mutane suke koyo, kamar yadda a kan wasa ƙarfe da ƙarfe.
18 Ka lura da itacen ɓaure, zai yi ‘ya’ya ka ci. Baran da ya lura da maigidansa za a girmama shi.
19 Yadda kake ganin fuskarka a ruwa, haka kake ganin kanka a zuciyarka.
20 Muradin mutum kamar lahira yake, a kullum ba ya ƙoshi.
21 Da wuta ake gwada azurfa da zinariya, amma yabon da ake yi wa mutum shi ne magwajinsa.
22 Ko da za ka doki wawa ka bar shi tsakanin rai da mutuwa, duk da haka yana nan da wautarsa kamar yadda yake.
23 Ka lura da garkunan tumakinka da na shanunka da kyau iyakar iyawarka,
24 domin dukiya ba ta tabbata har abada, al’ummai ma haka ne.
25 Ka yanki ingirici, lokacin da yake toho kana iya yankar ciyawa a gefen tuddai.
26 Kana iya yin tufafi da ulun tumakinka, kana iya sayen gona da kuɗin awakinka.
27 Madarar awakinka za ta zama abincinka kai da iyalinka, da kuma barorinka ‘yan mata.