1 Yabo bai dace da wawa ba, kamar yadda dusar ƙanƙara ba ta dace da lokacin zafi ba, ko ruwan sama a lokacin girbi.
2 La’ana ba za ta kama ka ba, sai dai in ka cancance ta. Tana kamar tsuntsayen da suke firiya da dare ba za su sauka ba.
3 Sai ka fyaɗi doki, ka sa wa jaki linzami, wawa kuma sai ka doke shi.
4 Idan ka amsa tambayar wauta, ka zama wawa daidai da mutumin da ya yi tambayar.
5 Ka amsa wauta ga tambayar wauta, wanda ya yi tambayar zai gane wawancinsa.
6 Mutumin da ya sa wawa ya isar masa da saƙo ya datse ƙafafunsa, yana nemar wa kansa wahala.
7 Wawa yakan yi amfani da karin magana kamar yadda tauyayyen mutum yake amfani da ƙafafunsa.
8 Wanda ya yabi wawa yana kama da wanda ya ɗaura dutse a majajjawa.
9 Karin magana a bakin wawa kamar sukar ƙaya ce a hannun mai maye.
10 Wanda ya ɗauki wawa aiki yana cutar duk wanda aikin ya shafa.
11 Wawan da yake maimaita aikin wautarsa yana kama da kare mai yin amai ya koma ya tanɗe.
12 Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.
13 Don me malalaci yakan kasa fita daga gida? Zaki yake tsoro?
14 Malalaci yana ta jujjuyawa a gadonsa kamar yadda ƙyauren ƙofa take juyawa.
15 Malalaci yana sa hannu cikin ƙwaryar abinci, amma ya kāsa kaiwa bakinsa.
16 Malalaci yana ganin kansa mai hikima ne fiye da mutum bakwai waɗanda suke da dalilai a kan ra’ayinsu.
17 Mutumin da ya tsoma baki cikin jayayyar da ba ta shafe shi ba sa’ad da yake wucewa, yana kama da mutum wanda yake kama kare a kunne.
18-19 Mutum wanda yakan ruɗi maƙwabcinsa sa’an nan ya ce, wasa yake yi kawai, yana kama da mahaukaci wanda yake wasa da wuta, da kibau, da mutuwa.
20 Idan ba itace wuta takan mutu, haka kuma idan ba mai gulma ba za a yi jayayya ba.
21 Kamar yadda gawayi yake ga garwashin wuta, itace kuma ga wuta, haka mai gardama yake ga jayayya.
22 Kamar yadda lomar abinci mai daɗi takan gangara can cikin ciki haka maganar mai gulma take.
23 Bakin da ba ya faɗar gaskiya, da zuciya mai ƙiyayya suna kama da kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba.
24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye ta da maganar bakinsa, yana kuma ƙunshe da munafunci.
25 Sa’ad da yake magana mai kyau kada ka gaskata shi, domin zuciyarsa tana cike da mugunta.
26 Ko da yake kila zai ɓoye ƙiyayyarsa, duk da haka muguntarsa za ta bayyana ga mutane.
27 Wanda ya haƙa ramin mugunta shi zai faɗa ciki, wanda kuma ya mirgino dutse, zai fāɗo a kansa.
28 Maƙaryaci yana ƙin wanda ya yi wa ƙarya, mai daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.