Waɗansu sauran Karin Magana na Sulemanu
1 Ga waɗansu sauran karin maganar Sulemanu waɗanda magatakardan Hezekiya Sarkin Yahuza suka juya.
2 Muna girmama Allah saboda abin da ya rufe, muna girmama sarakuna saboda abin da suka ba da bayaninsa.
3 Ba ku taɓa sanin abin da sarki yake tunani ba, gama tunaninsa sun fi ƙarfinmu. Kamar nisan sararin sama suke ko zurfafan teku.
4 Ka tace azurfa, gwani kuwa zai yi wani kyakkyawan abu da ita.
5 A kawar da mugayen mashawarta daga gaban sarki, hukumarsa za ta shahara a kan adalci.
6 Sa’ad da kake tsaye a gaban sarki, kada ka nuna kai wani abu ne, kana kai kanka inda Allah bai kai ka ba.
7 Gara a roƙe ka ka hau zuwa babban matsayi, da a faɗa maka ka ba da wurin da kake ga wanda ya fi ka maƙami.
8 Kada ka yi garajen kai ƙara a majalisa. Idan wani mashaidi ya nuna kai kake da kuskure, me za ka yi?
9 Idan kai da maƙwabcinka kun saɓa, ku daidaita a tsakaninku, kada a tona asiri.
10 Mai yiwuwa ne wani ya ji ya zarge ku, ba za ku taɓa rabuwa da wannan kunya ba.
11 Manufar da aka bayyana sosai kamar zubin zinariya take wanda aka yi a kan azurfa.
12 Faɗakarwar da mutumin da ya gogu da al’amuran duniya ya yi ga wanda yake da niyya ya kasa kunne, tamaninta ya fi na zoben zinariya, ko kayan ado da aka yi da zinariya tsantsa.
13 Amintaccen manzo yakan wartsakar da wanda ya aike shi, kamar ruwan sanyi yake a lokacin zafi.
14 Mutanen da suke yin alkawari, ba su cikawa, kamar holoƙo suke, hadirin kaka.
15 Rinjayen da aka yi cikin haƙuri yakan rushe ƙaƙƙarfar tsayayya, har ma yakan i wa masu ƙarfin gaske.
16 Kada ka kuskura ka sha zuma gaba da kima, in ya yi maka yawa za ka yi hararwa.
17 Kada ka cika ziyartar maƙwabcinka, ko zai gaji da kai har ya ƙi ka.
18 Mutumin da yakan faɗi ƙarairayi a kan maƙwabcinsa, shi kamar kakkaifan takobi ne, ko kulki, ko kibiya mai tsini.
19 Dogara ga marar aminci a lokacin hargitsi, kamar ƙoƙarin yin tauna da ruɓaɓɓun haƙora ne, ko yin tafiya da mai gurguwar ƙafa,
20 ko kuma ka yi ƙoƙarin jin ɗumi ta wurin tuɓe tufafinka a ranar da ake sanyi.
Raira waƙa ga mai baƙin ciki kamar marmasa gishiri a kan rauni ne.
21 Idan maƙiyinka yana jin yunwa ka cishe shi, idan yana jin ƙishi ka ba shi abin sha.
22 Za ka sa ya sha kunya, Ubangiji kuma zai sāka maka.
23 Iskar arewa takan kawo ruwan sama, haka kuma jita-jita takan kawo fushi.
24 Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mata mai mita.
25 Jin labari mai daɗi wanda ba ka zato, yana kamar shan ruwan sanyi ne a sa’ad da ka sha rana kana jin ƙishi.
26 Mutumin kirki wanda yakan yarda da mugun yana tunasshe ka da ƙazantattun maɓuɓɓuga ko rijiya mai dafi.
27 Kamar yadda shan zuma da yawa ba shi da kyau a gare ka, haka kuma ƙoƙarin neman yabo mai yawa yake.
28 Idan ba ka iya danne fushinka ba, ka zama mai kasala kamar birnin da ba shi da garuka, yana buɗe don a faɗa masa.