DAN 1

Tarbiyyar Daniyel da Abokansa

1 A shekara ta uku ta mulkin Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya zo Urushalima ya kewaye ta da yaƙi.

2 Ubangiji kuwa ya ba Nebukadnezzar nasara a kan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai ya kwashe waɗansu kayayyakin Haikalin Allah, ya kawo su ƙasar Shinar a gidan gunkinsu, ya ajiye kayayyakin a baitulmalin gunkinsa.

3 Sa’an nan Sarkin Babila ya umarci sarkin fādarsa, Ashfenaz, ya zaɓo masa waɗansu samari daga cikin Yahudawa, waɗanda suke daga gidan sarauta, da kuma daga gidan manya,

4 su kasance samari ne kyawawa, waɗanda ba su da wata naƙasa, masu fasaha cikin kowane abu, masu fahimta, da masu saurin ganewa, waɗanda suke da halin iya hidima a fādar sarki. Nebukadnezzar ya umarci Ashfenaz ya koya musu littattafan Kaldiyawa da harshen Kaldiyawa.

5 Sarki kuwa ya sa a riƙa ba su abinci da ruwan inabi irin nasa kowace rana. A kuma koyar da su har shekara uku. Bayan shekara uku za su shiga yi wa sarki hidima.

6 A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, daga kabilar Yahuza.

7 Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa’an nan ya kira Azariya, Abed-nego.

8 Daniyel kuwa ya ƙudura a ransa, ba zai ƙazantar da kansa da cin abinci iri na sarki da shan ruwan inabinsa ba, don haka ya roƙi sarkin fāda, kada ya ba shi wannan abincin da zai ƙazantar da shi.

9 Allah kuwa ya sa Daniyel ya sami farin jini da soyayya a wurin sarkin fāda.

10 Sa’an nan sarkin fāda ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoro kada shugaban sarki wanda ya umarta a riƙa ba ku wannan abinci da ruwan inabi ya ga jikinku ba su yi kyau kamar na samarin tsaranku ba, ta haka za ku sa in shiga uku a wurin sarki.”

11 Sai Daniyel ya ce wa baran da sarkin fāda ya sa ya lura da su Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya,

12 “Ka jarraba barorinku har kwana goma. A riƙa ba mu kayan lambu mu ci, a kuma riƙa ba mu baƙin ruwa mu sha.

13 Sa’an nan ka duba fuskokinmu da na samari waɗanda suke cin abinci irin na sarki. Ka yi da barorinku gwargwadon yadda ka gan mu.”

14 Ya yarda da abin da Daniyel ya ce, ya kuwa jarraba su har kwana goma ɗin.

15 A ƙarshen kwana goma ɗin, sai aka ga fuskokinsu suna sheƙi, sun kuma yi ƙiba fiye da samarin da suke cin abinci irin na sarki.

16 Don haka baran ya janye shirin ba su abinci da ruwan inabi irin na sarki, ya ci gaba da ba su kayan lambu.

17 Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.

18 Sa’ad da lokacin da sarki ya ƙayyade ya ƙare, sarkin fāda ya gabatar da su a gaban Nebukadnezzar.

19 Da sarki ya yi magana da su, sai ya tarar a cikinsu duka, ba wani kamar Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya. Don haka aka maishe su ‘yan majalisar sarki.

20 A cikin dukan abin da ya shafi hikima da ganewa wanda sarki ya nemi shawararsu, sai ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa har sau goma.

21 Daniyel kuwa ya ci gaba har shekarar farko ta sarki Sairas.