EZRA 3

An Komo da Yin Sujada

1 Da tsayawar watan bakwai, sai mutanen Isra’ila waɗanda suka riga suka koma garuruwansu, suka taru gaba ɗaya a Urushalima.

2 Sai Yeshuwa ɗan Yehozadak tare da ‘yan’uwansa, firistoci, da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel tare da ‘yan’uwansu, suka tashi suka gina bagaden Allah na Isra’ila domin a miƙa hadayu na ƙonawa kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, mutumin Allah.

3 Suka ta da bagaden a wurinsa domin suna jin tsoron mutanen ƙasar. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa safe da yamma.

4 Suka kuma kiyaye Idin Bukkoki kamar yadda aka rubuta, suna miƙa hadayu na ƙonawa kowace rana bisa ga yawan adadin hadayun da ake bukata.

5 Daga baya kuma suka miƙa hadayun ƙonawa na yau da kullum, da hadayu na amaryar wata, da ƙayyadaddun hadayu na idodin Ubangiji, da hadayu na amaryar wata, da ƙayyadaddun Ubangiji.

6 Tun daga rana ta fari ga watan bakwai, suka fara miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa, amma ba a riga an aza harsashin Haikalin Ubangiji ba.

An Fara Gina Haikali

7 Sai suka ba magina da masassaƙa kuɗin, suka kuma ba Sidoniyawa da mutanen Taya abinci, da abin sha, da mai don su kawo itacen al’ul daga Lebanon zuwa teku a Yafa bisa ga izinin da suka samu daga wurin sarki Sairus.

8 A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran ‘yan’uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa ‘yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.

9 Sai Yeshuwa da ‘ya’yansa da danginsa, da Kadmiyel da ‘ya’yansa, da ‘ya’yan Hodawiya, da ‘ya’yan Henadad, duk Lawiyawa ne, suka yi shugabancin aikin ginin Haikalin Allah.

10 Sa’ad da maginan suka aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji, firistoci suna nan tsaye saye da rigunansu, suna riƙe da ƙahoni, Lawiyawa kuma ‘ya’yan Asaf, suna riƙe da kuge domin su yabi Ubangiji, bisa ga umarnin Dawuda, Sarkin Isra’ila.

11 Da bangirma suka raira waƙa ta yabo da godiya ga ubangiji, suna cewa,

“Ubangiji nagari ne,

Gama ƙaunarsa marar matuƙa ce,

Ta tabbata har abada ga Isra’ila.”

Sai mutane duka suka ɗaga murya da ƙarfi suka yabi Ubangiji, saboda an aza harsashin ginin Haikalin Ubangiji.

12 Amma da yawa daga cikin firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin gidajen kakanni, wato tsofaffi waɗanda suka ga Haikali na farko, suka yi kuka da babbar murya a sa’ad da suka ga an aza harsashin ginin wannan Haikali. Waɗansu kuwa suka yi sowa don farin ciki.

13 Saboda haka mutane ba su iya rarrabe amon muryar murna da ta kuka ba, gama mutanen suka ɗaga murya da ƙarfi har aka ji su daga nesa.