EZRA 7

Ezra da Ƙungiyarsa Sun Iso Urushalima

1 Bayan wannan a zamanin Artashate Sarkin Farisa, sai Ezra ya gane da asalinsa, wato shi na ɗan Seraiya, da Azariya, da Hilkiya,

2 da Shallum, da Zadok, da Ahitub,

3 da Amariya, da Azariya, da Merayot,

4 da Zarahiya, da Uzzi, da Bukki,

5 da Abishuwa da Finehas, da Ele’azara, da Haruna babban firist.

6 Ezra ɗin ya taho daga Babila. Shi malami ne, masanin shari’ar Musa, wadda Ubangiji Allah na Isra’ila ya bayar. Sarki kuwa ya ba shi dukan abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.

7 A shekara ta bakwai kuma ta sarautar sarki Artashate, waɗansu mutanen Isra’ila, da waɗansu firistoci, da Lawiyawa,da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da ma’aikatan Haikali, suka taho Urushalima.

8 Ezra kuma tare da su, suka iso Urushalima a watan biyar na shekara ta bakwai ta sarautar sarkin.

9 Suka taso daga Babila a rana ta fari ga watan fari, suka iso Urushalima a rana ta fari ga watan biyar, Allah kuwa yana tare da su.

10 Gama Ezra ya ba da kansa ga yin nazarin dokokin Allah, ya kiyaye su, ya kuma koyar wa Isra’ilawa dokoki da farillan Allah.

Takardar da Sarki Artashate Ya Ba Ezra

11 Wannan ita ce takardar doka da sarki Artashate ya ba Ezra, wanda yake firist da magatakarda, ƙwararre cikin sha’anin dokoki da umarnan Ubangiji a cikin Isra’ilawa.

12 Ta ce, “Daga Artashate, sarkin sarakuna, zuwa ga Ezra firist, masanin shari’ar Allah na Sama.

13 “Yanzu na yi doka, cewa kowane mutum daga cikin mutanen Isra’ila, da firistocinsu, da Lawiyawansu da suke cikin mulkina wanda yake so ya koma Urushalima, sai ya tafi tare da kai.

14 Gama sarki ne da ‘yan majalisarsa guda bakwai suka aike ka don ka san irin zaman mutanen Yahuza da na Urushalima game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka,

15 domin kuma ka ba da azurfa da zinariya waɗanda sarki da ‘yan majalisarsa suka ba Allah na Isra’ila da yardar ransu, wato Allah wanda Haikalinsa yake a Urushalima,

16 da kuma azurfa da zinariya da za ka samu a dukan lardin Babila tare da hadayu na yardar rai daga mutane da firistoci, hadayun da suka yi wa’adi su bayar da yardar ransu domin Haikalin Allahnsu, da yake a Urushalima.

17 “Da wannan kuɗi ne za ka himmatu, ka sayi bijimai, da raguna, da ‘yan raguna, da hadayunsu na gari, da na sha. Za ka miƙa su a bisa bagaden Haikalin Allah da yake a Urushalima.

18 Duk abin da kai da ‘yan’uwanka kuka ga ya dace ku yi, sai ku yi shi da sauran azurfa da zinariya bisa ga nufin Allahnku.

19 Kwanonin da aka ba ka domin hidima a Haikalin Allah, sai ka ajiye su a gaban Allah a Urushalima.

20 Dukan abin da ake bukata domin Haikalin Allah, abin nan kuwa ya kamata a yi shi, sai ka yi shi da kuɗin baitulmalin sarki.

21 “Ni, sarki Artashate, ina umartar kowane ma’aji na Yammacin Kogin Yufiretis, cewa duk abin da Ezra, firist, masanin dokokin Allah na Sama, zai bukata a gare ka, sai ka himmatu ka yi.

22 Sai ku ba shi abin da ya kai talanti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari ta ruwan inabi, mai kuma garwa ɗari. Gishiri kuwa a bayar da yawa, kada a iyakance.

23 Dukan abin da Allah na Sama ya umarta, sai a yi shi sosai domin Haikalin Allah na Sama, domin kada ya yi fushi da mulkin sarki da ‘ya’yansa.

24 Muna kuma sanar da ku, cewa ba daidai ba ne ku karɓi haraji, da kuɗin shiga da fita, daga wurin firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da masu lura da Haikali, da ma’aikatan wannan Haikali na Allah.

25 “Kai kuma, Ezra, bisa ga hikimar da Allahnka ya ba ka, sai ka naɗa mahukunta da alƙalai waɗanda za su yi wa mutanen da suke a lardin Yammacin Kogi shari’a, wato dukan waɗanda suka san shari’a. Waɗanda ba su san shari’a ba kuwa, sai ka koya musu.

26 Duk wanda bai yi biyayya da shari’ar Allahnka ba, ko shari’ar sarki, sai a yi masa hukunci mai tsanani, ko na mutuwa, ko na kora, ko na ƙwace dukiyarsa, ko na kurkuku.”

Ezra Ya Yi Yabon Allah

27 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na kakanninmu, wanda ya sa a zuciyar sarki ya ƙawata Haikalin Ubangijin da yake a Urushalima.

28 Wanda kuma ya sa na sami tagomashi a wurin sarki, da ‘yan majalisarsa, da manyan ma’aikatansa. Na sami ƙarfin hali, gama Ubangiji Allahna yana tare da ni. Sai na tattara manyan mutane na Isra’ila don mu tafi tare.