K. MAG 24

1 Kada ka ji ƙyashin mugaye, kada ka yi ƙoƙarin yin abuta da su.

2 Duk tunaninsu na yin mugunta ne, a duk lokacin da suka buɗe bakinsu sai sun cuci wani.

3 An gina gidaje a kan harsashin hikima da fahimi.

4 Ta wurin ilimi a kan ƙawata ɗakuna da kyawawan kayayyaki masu tamani.

5 Mai hikima ƙaƙƙarfa ne, i, mai ilimi yana daɗa ƙarfi.

6 Banda wannan ma, dole ne ka shisshirya a natse kafin ka kama yaƙi. Bisa ga shawarwarin da za ka samu ne za ka yi nasara.

7 Kalmomi masu hikima sun yi wa wawa zurfin ganewa ƙwarai, ba shi da ta cewa sa’ad da ake magana a kan muhimman abubuwa.

8 Idan a ko yaushe shirye-shiryen mugunta kake, za ka yi suna a kan kuta tashin hankali.

9 Kowace irin dabarar da wawa yake tunani a kanta zunubi ne. Jama’a suna ƙin mutum mai rainako.

10 Idan ba ka da ƙarfi a lokacin hargitsi, hakika ka tabbata marar ƙarfi.

11 Kada ka ji nauyin ceton wanda ake janye da shi zuwa inda za a kashe shi.

12 Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.

13 Ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau. Kamar yadda kakin zuma yake da zaƙi a harshenka,

14 haka ilimi da hikima suke da amfani ga ranka. Ka same su, a gaba za ka yi farin ciki.

15 Kada ka shirya dabarun yi wa amintacce ƙwace, ko ka ƙwace masa gidansa, wannan mugunta ce.

16 Ko sau nawa amintaccen mutum ya faɗi, ba abin damuwa ba ne, gama a ko yaushe zai sāke tashi, amma masifa takan hallaka mugaye.

17 Kada ka yi murna sa’ad da bala’i ya aukar wa maƙiyinka.

18 Ubangiji zai sani in kana murna, ba kuwa zai so haka ba, mai yiwuwa ne ba zai hukunta shi ba.

19 Kada ka damu saboda mugaye, kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba.

20 Gama mugun mutum ba shi da sa zuciya, ba abin da zai sa zuciya a kansa nan gaba.

21 Ɗana, ka yi tsoron Ubangiji, ka kuma ji tsoron sarki, kada ka yi harkar kome da mutanen da suka tayar musu.

22 Irin waɗannan mutane sukan hallaka farat ɗaya. Ka taɓa yin tunani a kan bala’in da Allah ko sarki sukan aukar?

Waɗansu sauran Karin Magana na Hikima

23 Masu hikima kuma sun faɗi waɗannan abu.

Kuskure ne alƙali ya yi son zuciya.

24 Idan ya kuɓutar da mugu, kowane mutum da yake a duniya zai la’anta shi ya ƙi shi.

25 Alƙalan da suke hukunta wa mai laifi kuwa, za su arzuta, su ji daɗin kyakkyawan suna.

26 Amsar gaskiya ita ce alamar abuta ta ainihi.

27 Kada ka gina gidanka ka kafa shi, sai ka gyara gonakinka, ka tabbata za ka sami abin zaman gari.

28 Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isasshen dalili ba, ko ka faɗi ƙarya a kansa.

29 Kada ka ce, “Zan yi masa daidai da yadda ya yi mini, zan rama masa!”

30 Na ratsa ta gonakin inabin wani malalaci, dakiki,

31 suna cike da ƙayayuwa, ciyayi sun sha kansu, katangar dutse da take kewaye da su ta faɗi.

32 Da na dubi wannan, na yi tunani a kansa, ya zamar mini ishara.

33 “Yi ta ruruminka, ci gaba da barcinka, rungume hannuwanka don ka shaƙata.”

34 Amma sa’ad da kake ta sharar barci fatara za ta auka maka kamar ƙungiyar ‘yan fashi.