K. MAG 28

Mugaye da Adalai

1 Mugun mutum yakan gudu, alhali kuwa ba mai korarsa, amma amintaccen mutum kamar zaki yake, ba shi da tsoro.

2 Al’umma za ta ƙarfafa ta jure idan shugabanninta masu basira ne, masu hankali. Amma idan ƙasar mai aikata zunubi ce za ta sami shugabanni da yawa.

3 Mai mulki wanda yake zaluntar talakawa, ya zama kamar ruwa mai lalatar da amfanin gona.

4 Wanda ba ya bin doka tare da mugaye yake, amma idan kana bin doka kai abokin gāban mugaye ne.

5 Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada sun san ta sosai.

6 Gara ka zama matalauci mai aminci da ka zama mawadaci, marar aminci.

7 Saurayi wanda ya kiyaye doka mai basira ne shi, amma wanda yake abuta da ‘yan iska zai zama mai jawo wa mahaifinsa kunya.

8 Idan kana tara dukiya ta wurin ba da bashi da ruwa kana kuma ƙwarar jama’a, dukiyarka za ta koma ga wanda yake yi wa talakawa alheri.

9 Idan ka ƙi biyayya ga doka, Allah zai ƙi jin addu’o’inka.

10 Idan ka yaudari mutumin kirki don ya faɗa cikin mugunta, kai kanka ne za ka fāɗa cikin tarkon da ka haƙa. Marar laifi kuwa zai sami babban sakamako.

11 Attajirai, a ko yaushe, zato suke su masu hikima ne, amma matalauci mai tunani ya fi sanin abin da yake daidai.

12 Sa’ad da mutanen kirki suke sarauta, kowa da kowa yakan yi biki, amma sa’ad da mugaye suka kama mulki mutane sukan riƙa ɓuya.

13 Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa’an nan Allah zai yi maka jinƙai.

14 Mutumin da yake tsoron Ubangiji ko yaushe, zai yi farin ciki, amma idan ya taurare zai lalace.

15 Talakawa ba su da wani taimako sa’ad da suke ƙarƙashin mulkin mugun. Abin tsoro ne shi kamar zaki mai ruri, ko beyar mai sanɗa.

16 Mai mulki wanda ba shi da basira yakan zama mai mugun tsanani. Amma wanda yake ƙin rashin aminci, ko ta ƙaƙa zai daɗe yana mulki.

17 Mutumin da yake da laifin kisankai, yana haƙa wa kansa kabari da gaggawa. Kada ka yi ƙoƙarin hana shi.

18 Ka yi aminci za ka zauna lafiya, idan kuwa ka yi rashin aminci za ka fāɗi.

19 Manomin da yake aiki sosai, zai sami wadataccen abinci, amma mutanen da suke zaman banza ko yaushe, za su zama matalauta.

20 Amintaccen mutum zai cika kwanakinsa lafiya, amma idan kana so ka sami dukiya dare ɗaya, za a hukunta ka.

21 Nuna sonkai mugun abu ne, waɗansu alƙalai sukan aikata mugunta saboda ‘yar ƙaramar rashawa.

22 Mutum mai haɗama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.

23 Wanda ya tsauta wa mutum zai sami yabo daga baya, fiye da wanda ya yi masa daɗin baki.

24 Wanda yake yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa sata, yana kuwa tsammani ba laifi ba ne, daidai da ɓarawo yake.

25 Mutum mai haɗama yana haddasa tashin hankali, amma wanda ya dogara ga Ubangiji zai sami wadar zuci.

26 Wanda yake dogara ga son zuciyarsa, wawa ne, amma wanda yake tafiya cikin hikima zai kuɓuta.

27 Wanda yake bayarwa ga matalauta, ba zai talauce ba, amma wanda bai kula da su ba, mutane da yawa za su la’ance shi.

28 Mutane sukan ɓuya sa’ad da mugaye suka sami iko, amma sa’ad da iko ya fita daga hannunsu adalai sukan ƙaru.