K. MAG 31

Shawara ga Sarki

1 Wannan ita ce maganar sarki Lamuwel wadda uwarsa ta koya masa.

2 “Mene ne, ɗana? Mene ne, ya ɗana ne cikina? Mene ne, ɗana na wa’adi?

3 Kada ka ba da ƙarfinka ga mata, kada kuwa ka mai da hankali gare su, waɗanda suke hallaka sarakuna.

4 Bai dace ba, ya Lamuwel, bai dace ba ko kaɗan, sarakuna su sha ruwan inabi, ko masu mulki su yi marmarin barasa,

5 don kada su sha su manta da doka, su kuma kauce wa gaskiya a shari’ar waɗanda aka zalunta.

6 A ba da barasa ga wanda yake cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi kuma ga waɗanda suke cikin ɓacin rai.

7 Bari ya sha don ya manta da talaucinsa, don kada kuma ya ƙara tunawa da ɓacin ransa.

8 “Ka yi magana domin bebaye, domin kuma hakkin dukan waɗanda ba su da wani mataimaki.(1Sam 19.4; Ayu 29.12-17)

9 Ka yi magana dominsu, ka yi shari’ar adalci, ka kiyaye hakkin matalauta da masu bukata.”

Yabon Macen Kirki

10 Wa yake iya samun cikakkiyar mace? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.

11 Mijinta yakan amince da ita, ba kuwa zai yi hasara ba.

12 Takan yi masa alheri ba mugunta ba, dukan kwanakinta.

13 Takan samo ulu da lilin, ta yi saƙa da hannuwanta da farin ciki.

14 Takan kawo abincinta daga nesa, kamar fatake.

15 Takan yi asubanci ta shirya wa iyalinta abinci, ta kuma shirya wa ‘yan matan gidanta aike-aiken da za su yi.

16 Takan lura da gona sosai kafin ta saya, da ribar da ta ci take dasa gonar inabi.

17 Takan himmantu ta yi aiki tuƙuru.

18 Ta sani akwai riba a cikin kasuwancinta. Fitilarta na ci dare farai.

19 Da hannunta take kaɗi, tana kuma saƙa da hannuwanta.

20 Takan yi wa matalauta da masu fatara karamci.

21 Ba ta jin tsoron lokacin sanyi gama ‘ya’yanta duka suna da tufafi masu ƙauri.

22 Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa, tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.

23 Mijinta sananne ne a dandali, sa’ad da yake zaune tare da dattawan gari.

24 Takan yi riguna na lilin ta sayar, takan kuma sayar wa fatake da abin ɗamara.

25 Wadata da mutunci su ne suturarta. Ba ta jin tsoron tsufa.

26 Tana magana da hikima. Koyarwarta ta alheri ce.

27 Tana lura da al’amuran ‘ya’yanta da kyau. Ba ruwanta da ƙyuya.

28 ‘Ya’yanta sukan tashi su gode mata, mijinta kuma yana yabonta.

29 Ya ce, “Mata da yawa sun yi abin yabo, amma ke kin fi su duka.”

30 Kayan tsari da jamali duk banza ne, amma mace mai tsoron Ubangiji, ita ce abar yabo.

31 A yi mata cikakken yabo saboda ayyukanta, za a yabi ayyukanta a dandali.