K. MAG 8

Yabon Hikima

1 Ku kasa kunne! Hikima tana kira.

Tana so a ji ta.

2 Tana tsaye bisa kan tuddai a bakin hanya

Da a mararraban hanyoyi.

3 A ƙofofin shiga birni, tana kira,

4 “Ina roƙonku, ya ku, ‘yan adam,

Ina kiran kowane mutum da yake a duniya.

5 Ba ku balaga ba? To, ku balaga.

Ku wawaye ne? Ku koyi hankali.

6 Ku kasa kunne ga jawabina mafi kyau,

Dukan abin da na faɗa muku daidai ne.

7 Abin da na faɗa gaskiya ne,

Ƙarairayi abin ƙi ne a gare ni.

8 Kowane abu da na faɗa gaskiya ne,

Ba wani abu da yake na laifi ko na ruɗawa.

9 Ga mutum mai basira, dukan abu ne a sarari,

Ga wanda aka sanar da shi sosai, abu ne a sawwaƙe.

10 Ka zaɓi koyarwata fiye da azurfa,

Ka zaɓi ilimi fiye da zinariya tsantsa.

11 “Ni ce hikima, na fi lu’ulu’ai,

Cikin dukan abin da kake so, ba kamata.

12 Ni ce hikima, ina da basira,

Ina da ilimi da faɗar daidai.

13 Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji,

Na ƙi girmankai, da fāriya, da mugayen hanyoyi,

Da maganganu na ƙarya.

14 Nakan shirya abin da zan yi, in kuwa yi shi.

Ina da fahimi, ina da ƙarfi.

15 Nakan taimaki sarakuna su yi mulki,

Mahukunta kuma su tsara dokoki masu kyau.

16 Kowane mai mulki a duniya, da taimakona yake mulki,

Ƙusoshin hukumomi da dattawan gari duka ɗaya.

17 Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,

Dukan wanda yake nemana kuma zai same ni.

18 Ina da dukiya da daraja da zan bayar,

Da wadata da nasara kuma.

19 Abin da za ka samu daga gare ni

Ya fi zinariya kyau, da azurfa tsantsa.

20 A kan hanyar adalci nake tafiya,

Rankai a kan hanyoyin gaskiya.

21 Ina ba da dukiya ga waɗanda suke ƙaunata,

Ina kuma cika gidajensu da wadata.

22 “Ni ce halittar farko da Ubangiji

Ya fara halittawa daga cikin ayyukansa tuntuni.

23 Da farkon farawa ni aka fara halittawa

Kafin a yi duniya.

24 Ni aka fara yi kafin tekuna,

A sa’ad da ba maɓuɓɓugan ruwa.

25 Ni aka fara yi kafin a yi duwatsu,

Kafin a kafa tuddai a wurarensu,

26 Kafin Allah ya halicci duniya da filayenta,

Ko ɗan ɓarɓashin ƙasa.

27 A can nake sa’ad da ya shata sararin sama,

Da sa’ad da ya shimfiɗa al’arshi a hayin tekuna,

28 Da sa’ad da ya sa gizagizai a sararin sama,

Ya buɗe maɓuɓɓugan teku,

29 Ya kuma umarci ruwan teku, kada ya zarce wurin da ya sa.

Ina can sa’ad da ya kafa harsashin ginin duniya.

30 Ina kusa da shi kamar mai tsara fasalin gini,

Ni ce abar murnarsa kowace rana,

A ko yaushe ina farin ciki a gabansa.

31 Ina farin ciki da duniya,

Ina murna da ‘yan adam.

32 “Yanzu ku matasa, ku kasa kunne gare ni,

Ku yi abin da na ce, za ku yi farin ciki.

33 Ku saurari abin da aka koya muku,

Ku zama masu hikima, kada ku yi sakaci da ita.

34 Mutumin da ya kasa kunne gare ni, zai yi farin ciki haka nan,

Wato yakan tsaya a ƙofata ko yaushe,

Yana kuma jira a ƙofar shiga gidana.

35 Mutumin da ya same ni ya sami rai,

Ubangiji zai ji daɗinsa.

36 Mutumin da bai same ni ba ya cuci kansa,

Duk wanda yake ƙina mutuwa yake ƙauna.”