M. HAD 11

Abin da Mai Hikima Yakan Yi

1 Ka jefa kyautarka a baya, ka tsince ta a gaba.

2 Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.

3 Idan gizagizai sun cika da ruwa sukan sheƙar da shi ƙasa. A inda itace ya faɗi, a nan zai kwanta, ko wajen kudu ko arewa.

4 Wanda yake la’akari da iska, ba zai yi shuka ba, wanda kuma yake la’akari da gizagizai, ba zai yi girbi ba.

5 Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda ƙasusuwan jariri suke girma a mahaifar uwarsa, haka nan kuma ba ka san aikin Allah ba, wato wanda ya yi abu duka.

6 Ka shuka iri da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.

7 Haske yana da daɗi, abu mai kyau kuma idanu su dubi hasken rana.

8 Idan mutum ya rayu har shekaru da yawa, bari ya yi murna a cikinsu duka. Sai dai kuma ya tuna da kwanakin duhu, gama sun fi yawa. Duk abin da ya faru banza ne.

Shawara ga Matasa

9 Ya saurayi! Ka yi murna a lokacin ƙuruciyarka, ka bar zuciyarka ta yi farin ciki a kwanakin samartakarka. Ka bi nufin zuciyarka da sha’awar idanunka. Amma ka sani fa, a cikin al’amuran nan duka Allah zai shara’anta ka.

10 Kada ka bar kome ya dame ka, ko ya yi maka zafi a rai, gama ƙuruciya da samartaka ba za su dawwama ba.