M. HAD 3

Kowane Abu da Lokacinsa

1 Dukan abin da yake faruwa a duniyan nan yakan faru ne a cikin lokacin da Allah ya so.

2 Shi yake sa lokacin haihuwa, da lokacin mutuwa,

Da lokacin dashe, da lokacin tumɓuke abin da aka dasa,

3 Da lokacin kisa, da lokacin rayarwa,

Da lokacin rushewa, da lokacin ginawa.

4 Shi ne kuma yake sa lokacin yin kuka, da lokacin yin dariya,

Da lokacin yin makoki, da lokacin yin murna,

5 Da lokacin warwatsa duwatsu, da lokacin tattarawa,

Da lokacin rungumewa, da lokacin da ba a yi.

6 Shi ne kuma yake sa lokacin nema, da lokacin rashi,

Da lokacin adanawa, da lokacin zubarwa,

7 Da lokacin ketawa, da lokacin gyarawa,

Da lokacin yin shiru, da lokacin magana.

8 Shi ne kuma yake sa lokacin ƙauna, da lokacin ƙiyayya,

Da lokacin yaƙi, da lokacin salama.

9 Wace riba mutum zai ci a kan dukan aikinsa?

10 Na san hukuncin da Allah ya ɗora mana mu yi ta fama da shi.

11 Shi ya sa wa kowane abu lokacinsa. Shi ne kuma ya sa mana buri mu san abin da yake nan gaba, amma fa bai ba mu cikakken sanin ayyukan da yake yi ba, tun daga farko har zuwa ƙarshe.

12 Na gane iyakar abin da mutum zai yi, shi ne ya yi farin ciki, ya yi abin kirki tun yana da rai.

13 Dukanmu mu ci, mu sha, mu yi murna da abin da muka yi aikinsa, gama wannan kyautar Allah ce.

14 Na sani dukan abin da Allah ya yi zai dawwama, ba abin da za a ƙara, ko a rage. Allah ya yi haka kuwa domin mutane su zama masu tsoronsa.

15 Dukan abin da ya faru, ya riga ya faru a dā. Allah ya sa abin da ya faru ya yi ta faruwa. Allah yana hukunta abin da ya riga ya faru.

Rashin Adalcin da yake a Duniya

16 Banda wannan kuma, na gane a duniyar nan mugunta ta gāje matsayin adalci da na abin da yake daidai.

17 Sai na ce a zuciyata, “Da adali, da mugu, Allah zai shara’anta su, domin an ƙayyade lokaci na yin kowane abu da na yin kowane aiki.”

18 Na dai ce Allah yana jarraba mutum ne domin ya nuna masa bai ɗara dabba ba.

19 Gama makomar ‘yan adam da ta dabbobi ɗaya ce, yadda ɗayan yake mutuwa haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne. Mutum bai fi dabba ba, gama rai ba shi da wata ma’ana ga kowannensu.

20 Dukansu wuri ɗaya za su tafi, gama dukansu biyu daga turɓaya suka fito, dukansu biyu kuma za su koma cikinta.

21 Wa zai iya tabbatarwa, cewa ruhun mutum zai tafi sama, ruhun dabba kuwa zai tafi ƙasa?

22 Na gane abin da ya fi wa mutum, shi ne ya more wahalar aikinsa, gama ba wani abu da zai iya yi. Ba wata hanya da zai san abin da zai faru bayan mutuwarsa.