M. HAD 9

Rashin Daidaitawa

1 Na daɗe ina tunani ƙwarai a kan wannan abu duka, yadda Allah yake sarrafa ayyukan masu hikima da na adalai, har da ƙaunarsu da ƙiyayyarsu. Ba wanda ya san abin da zai faru nan gaba.

2 Ba wani bambanci. Makoma ɗaya ce, ta adali da ta mugu, da ta mutumin kirki da ta marar kirki, da ta tsattsarka da ta marar tsarki, da ta masu yin sujada da ta marasa yi. Mutumin kirki bai fi mai zunubi ba. Wanda ya yi rantsuwa bai fi wanda bai yi ba.

3 Duk makomarsu ɗaya ce, wannan ita ce ɓarnar da take faruwa a duniya. Muddin mutane suna da rai tunaninsu cike yake da mugunta da rashin hankali. Bayan haka sukan mutu.

4 Amma dukan wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki.

5 Hakika rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba. Ba su da wani sauran lada nan gaba, an manta da su ke nan sam.

6 Ƙaunarsu, da ƙiyayyarsu, da kishinsu sun mutu tare da su. Ba za su ƙara yin wani abu da ake yi a duniya ba.

7 Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara’a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.

8 Ka yi farin ciki da fara’a kullum.

9 Ka yi nishaɗi da matar da kake ƙauna, dukan kwanakin ranka na banza waɗanda Allah ya ba ka a wannan duniya, ka more kowace rana, wannan ne kaɗai rabonka na wahalar aikinka a duniya.

10 Duk abin da kake iya yi, ka yi shi da iyakar iyawarka, domin ba aiki, ko tunani, ko ilimi, ko hikima a lahira, gama can za ka.

11 Na gane wani abu kuma, ashe, a duniyan nan ba kullum maguji ne yake cin tsere ba, ba kullum jarumi ne yake cin nasara ba. Ba kullum mai hikima ne da abinci ba, ba kullum mai basira ne yake da wadata ba, ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba. Amma sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.

12 Gama mutum bai san lokacinsa ba, kamar kifayen da akan kama da taru, kamar kuma tsuntsayen da akan kama da tarko, haka nan mugun lokaci yakan auko wa ‘yan adam farat ɗaya.

Hikima ta Fi Iko

13 A duniyar nan na ga wani babban al’amari game da hikima.

14 Dā akwai wani ɗan ƙaramin gari, mutane kuma suke ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani.

15 Akwai wani matalauci, mai hikima, a garin, sai ya ceci garin ta wurin hikimarsa. Duk da haka ba wanda ya tuna da wannan matalauci.

16 Na ce hikima ta fi ƙarfe ƙarfi, ko da yake an raina hikimar matalauci da maganarsa.

17 Gara a kasa kunne ga tattausar maganar mai hikima, da a kasa kunne ga hargagin mai mulki a tsakanin wawaye.

18 Hikima ta fi makaman yaƙi, amma mai zunubi ɗaya yakan yi ɓarna mai yawa.