Tashin Yesu daga Matattu
1 To, bayan Asabar, da asussuba a ranar farko ta mako, sai Maryamu Magadaliya da ɗaya Maryamun, suka je ganin kabarin.
2 Sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, domin wani mala’ikan Ubangiji ne ya sauko daga Sama, ya zo ya mirgine dutsen, ya zauna a kai.
3 Kamanninsa suna haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kamar dusar ƙanƙara.
4 Saboda tsoronsa sai masu tsaro suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu.
5 Amma sai mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye.
6 Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi.
7 Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa, cewa, ya tashi daga matattu. Ga shi kuma, zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. Ga shi, na gaya muku.”
8 Sai suka tashi daga kabarin da gaggawa da tsoro, game da matuƙar farin ciki, suka ruga a guje su kai wa almajiransa labari.
9 Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama alaikun!” Suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada.
10 Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa ‘yan’uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”
Rahoton Masu Tsaron Kabarin
11 Suna tafiya ke nan, sai waɗansu daga cikin sojan nan suka shiga birni, suka ba manyan firistoci labarin da ya auku.
12 Su kuwa da suka taru da shugabannin jama’a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka,
13 suka ce, “Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo da daddare suka sace shi kuna barci.
14 In kuwa labarin nan ya kai ga kunnen mai mulki, mā rarrashe shi, mu tsare ku daga wahala.”
15 Sai suka karɓi kuɗin, suka yi yadda aka koya musu. Wannan magana kuwa, ta bazu cikin Yahudawa har ya zuwa yau.
Umarnin Yesu ga Goma Sha Ɗayan
16 To, almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su.
17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka.
18 Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.
19 Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al’ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,
20 kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”