1 Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki ‘yar kwalabar mai, ya zuba wa Saul a kā, ya yi masa sumba, ya ce, “Ubangjiji ne ya keɓe ka, ya naɗa ka sarki a kan jama’arsa.
2 Yau, sa’ad da ka rabu da ni, za ka gamu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a karkarar Biliyaminu a Zelza. Za su ce maka, jakunan da ka tafi nema an same su, yanzu mahaifinka ya daina damuwa saboda jakunan, sai a kanku, yana cewa, ‘Ina zan gane ɗana?’
3 Sa’ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da ‘yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi.
4 Za su gaishe ka, su ba ka malmala biyu, kai kuwa sai ka karɓa.
5 Sa’ad da ka isa Gibeya, wato tudun Allah, inda sansanin sojojin Filistiyawa yake, a nan kuma sa’ad da kake shiga garin, za ka tarar da ƙungiyar annabawa suna gangarowa daga wurin bagaden a kan tudu suna kaɗa garaya, da kuwaru, da sarewa, da molo, suna rawa suna sowa.
6 Sa’an nan Ruhun Ubangiji zai sauko maka, za ka kuwa yi rawa da sowa tare da su, za ka zama wani mutum dabam.
7 Sa’ad da waɗannan alamu suka cika, sai ka yi abin da hali ya nuna maka, gama Ubangiji yana tare da kai.
8 Za ka riga ni zuwa Gilgal inda zan zo in miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ka jira ni kwana bakwai, har in zo in sanar da kai abin da za ka yi.”
9 Da Saul ya juya zai tashi daga wurin Sama’ila, sai Ubangiji ya ba shi sabuwar zuciya. Alamun nan kuma suka cika a ranar.
10 Sa’ad da suka iso Gileyad, sai suka tarar da ƙungiyar annabawa. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga rawa da sowa tare da su.
11 Sa’ad da dukan waɗanda suka san shi, suka gan shi yana yin wannan tare da annabawa, suka ce wa junansu, “Me ya faru da ɗan Kish? Saul kuma yana cikin annabawa ne?”
12 Sai wani mutumin da yake wurin ya ce, “Sauran fa, su ma, iyayensu annabawa ne?” Wannan kuwa ya zama karin magana, “Har Saul kuma yana cikin annabawa?”
13 Da ya gama rawa da sowa sai ya tafi wurin bagaden a kan tudu.
14 Kawun Saul kuwa ya tambaye shi, shi da baransa, “Ina ne kuka tafi?”
Saul ya ce, “Mun je neman jakuna, da ba mu same su ba, sai muka tafi wurin Sama’ila.”
15 Kawunsa kuma ya ce, “In ka yarda ka faɗa mini abin da Sama’ila ya faɗa maka.”
16 Saul kuwa ya ce wa kawunsa, “Ya faɗa mana a fili an gane jakunan.” Amma bai faɗa wa kawunsa zancen sarautar da Sama’ila ya faɗa masa ba.
An yi Na’am da Zaman Saul Sarki
17 Sama’ila kuwa ya tara mutanen Isra’ila a gaban Ubangiji a Mizfa.
18 Ya ce musu, “In ji Ubangiji Allah na Isra’ila, ‘Ni na fito da Isra’ilawa daga Masar, na cece ku daga Masarawa da kuma daga hannun mulkokin da suka wahalshe ku.
19 Ni ne Allahnku wanda yake cetonku daga dukan masifu da wahalai, amma ga shi yau, kun ƙi ni kuna roƙona in ba ku sarki. To, da kyau, yanzu fa sai ku kusato gaban Ubangiji kabila kabila da iyali iyali.’ ”
20 Sa’an nan Sama’ila ya ce wa kabilan Isra’ila su guso, kuri’a kuwa ta faɗa a kan kabilar Biliyaminu.
21 Sai kuma ya sa kabilar Biliyaminu ta guso iyali iyali, kuri’a kuwa ta faɗa a kan iyalin Matri. Sa’an nan kuma ya guso da iyalin Matri mutum mutum, kuri’a ta faɗa a kan Saul, ɗan Kish. Amma sa’ad da suka neme shi, ba a same shi ba.
22 Suka yi tambaya a wurin Ubangiji, suka ce, “Ko akwai wani dabam?”
Ubangiji ya ce, “Ai, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”
23 Sai suka sheƙa, suka fito da shi daga wurin da ya ɓuya, ya tsaya cikin mutane, ya fi kowa tsayi da misalin ƙafa guda.
24 Sama’ila ya ce wa dukan jama’a, “Kun gan shi? Shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa, babu wani kamarsa a cikin dukan jama’a.”
Jama’a duka kuwa suka yi sowa suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”
25 Sa’an nan Sama’ila ya faɗa wa jama’a ka’idodin sarautar. Ya rubuta su cikin littafi, ya ajiye a wuri mai tsarki. Sa’an nan ya sallami jama’a duka kowa ya koma gidansa.
26 Saul kuma ya koma gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawa da Allah ya taɓa zuciyarsu.
27 Amma waɗansu shashashan mutane suka ce, “Ƙaƙa wannan yaro zai iya cetonmu?” Suka raina shi, ba su kawo masa gaisuwa ba. Amma bai ce kome ba.