Yaƙi da Filistiyawa
1 Saul yana da shekara talatin sa’ad da ya ci sarauta, ya yi shekara arba’in da biyu yana sarautar Isra’ila.
2 Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000) daga Isra’ila, dubu biyu (2,000) su zauna tare da shi a Mikmash da ƙasar tuddai ta Betel, dubu ɗaya (1,000) kuma su zauna tare da Jonatan a Gibeya ta Biliyaminu, sauran jama’a kuwa ya sallame su, su koma gida, kowa zuwa alfarwarsa.
3 Jonatan kuwa ya kashe wani shugaban yaƙi na Filistiyawa a Geba, Filistiyawa kuwa suka ji labarin abin da ya faru. Sai Saul ya sa aka busa ƙaho ko’ina a ƙasar, na kiran Ibraniyawa su zo yaƙi.
4 Isra’ilawa duka kuwa suka ji wai Saul ya kashe shugaban yaƙi na Filistiyawa, da kuma, Isra’ilawa sun zama abin ƙi ga Filistiyawa, sai jama’a suka amsa kiran, suka tafi wurin Saul a Gilgal.
5 Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Suka fito da karusa dubu talatin (30,000), da mahayan dawakai dubu shida (6,000), da sojoji da yawa kamar yashi a bakin teku, suka kafa sansani a Mikmash, a wajen gabashin Bet-awen.
6 Sa’ad da Isra’ilawa suka ga sun ƙuntata, gama an matsa su ƙwarai, sai suka ɓuya cikin kogwanni, da cikin ruƙaƙe, da duwatsu, da ramummuka, da kwazazzabai.
7 Waɗansu kuwa suka haye Kogin Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad.
Saul kuwa yana can a Gilgal. Dukan mutanen da suka bi shi suka yi ta rawar jiki.
8 Ya dakata kwana bakwai bisa ga adadin lokacin da Sama’ila ya ɗibar masa, amma Sama’ila bai iso Gilgal ba. Mutane suka yi ta watsewa suna barin Saul.
9 Sai Saul ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadayun salama.” Ya kuwa miƙa hadaya ta ƙonawa.
10 Yana gama miƙa hadayar ke nan, sai ga Sama’ila ya iso.
Saul kuwa ya fita don ya tarye shi, ya gaishe shi.
11 Sai Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?”
Saul ya amsa ya ce, “Don na ga mutane suna watsewa, suna barina, kai kuma ba ka zo daidai lokacin ba, ga kuma Filistiyawa sun tattaru a Mikmash.
12 Sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ni kuwa ban riga na roƙi Ubangiji ba,’ don haka ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa!”
13 Sama’ila kuwa ya ce wa Saul, “Ka yi wauta, ba ka kiyaye umarnin da Ubangiji Allahnka ya umarce ka da shi ba. Dā Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada.
14 Amma yanzu sarautarka ba za ta tabbata ba, gama Ubangiji ya riga ya sami mutum wanda yake so. Ubangiji ya riga ya naɗa shi ya zama sarkin jama’arsa, domin ba ka kiyaye umarnin Ubangiji ba.”
15 Sama’ila ya tashi daga Gilgal zuwa Gibeya ta Biliyaminu. Da Saul ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, ya tarar wajen mutum ɗari shida ne.
16 Sai Saul da ɗansa, Jonatan, da mutanen da suke tare da su suka zauna a Geba ta Biliyaminu. Filistiyawa kuwa suka kafa sansaninsu a Mikmash.
17 Sai runduna uku na mahara suka fito daga sansanin Filistiyawa. Runduna ɗaya ta nufi Ofra, zuwa ƙasar Shuwal.
18 Runduna guda kuma ta nufi Bet-horon, guda kuwa ta nufi iyakar da take fuskantar kwarin Zeboyim wajen jeji.
19 A wannan lokaci ba maƙeri a ƙasar Isra’ila duka, domin Filistiyawa sun hana Ibraniyawa su ƙera wa kansu takuba ko māsu.
20 Saboda haka kowane Ba’isra’ile yakan gangara zuwa Filistiyawa domin ya koɗa bakin garmarsa, da fartanyasa, da gatarinsa, da laujensa,
21 duk lokacin da za su koɗar bakin garma da fartanya sai su biya sulusin shekel ne, ladan koɗar gatari da shirya abin korar shanun noma sulusin shekel ne.
22 A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko mashi ba a cikin mutanen da suke tare da Saul da Jonatan. Amma Saul da ɗansa, Jonatan, suna da su.
23 Sai ƙungiyar sojojin Filistiyawa ta fita zuwa mashigin Mikmash.