Karfin Zuciyar Jonatan
1 Wata rana Jonatan, ɗan Saul, ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye mu je sansanin Filistiyawa a wancan hayi.” Amma bai faɗa wa mahaifinsa ba.
2 Saul kuwa yana zaune a karkarar Gibeya a gindin itacen rumman a Migron. Mutum wajen ɗari shida suna tare da shi.
3 Ahaija ɗan Ahitub kuma, ɗan’uwan Ikabod, wato jikan Eli, firist na Ubangiji, yana Shilo, yana sāye da falmaran. Mutane kuma ba su sani ba, ashe Jonatan ya tafi wani wuri.
4 A tsakanin mashigin dutse inda Jonatan yake so ya bi zuwa sansanin Filistiyawa, akwai dutse mai tsayi a kowane gefe. Sunan ɗaya Bozer, ɗayan kuma Sene.
5 Ɗaya dutsen yana wajen arewa a gaban Mikmash, ɗayan kuma yana daga kudu a gaban Geba.
6 Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin ‘yan kaɗan.”
7 Sai mai ɗaukar masa makamai ya ce, “Ka yi abin da yake a zuciyarka, ga shi, ina tare da kai, gama ina goyon bayanka, kamar yadda zuciyarka take haka kuma tawa.”
8 Sa’an nan Jonatan ya ce, “Za mu haye zuwa wurin mutanen, mu nuna kanmu gare su.
9 Idan sun ce mana, ‘Ku dakata har mu zo wurinku,’ to, sai mu tsaya cik, ba za mu tafi wurinsu ba.
10 Amma idan sun ce, ‘Ku haura zuwa wurinmu,’ to, sai mu haura, gama wannan alama ce, wato Ubangiji ya bashe su a hannunmu.”
11 Sai su biyu suka tafi suka nuna kansu ga sansanin Filistiyawa. Da Filistiyawa suka gan su, sai suka ce, “Ku duba, Ibraniyawa suna fitowa daga cikin ramummuka inda suka ɓuya.”
12 Sai suka kira Jonatan da mai ɗaukar makamansa, suka ce, “Ku hauro zuwa wurinmu, mu faɗa muku wani abu.”
Jonatan kuwa ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Ka biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra’ilawa.”
13 Sa’an nan Jonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukar makamansa kuwa yana biye da shi. Jonatan ya fāɗa wa Filistiyawa, ya yi ta kā da su, mai ɗaukar makamansa kuma ya bi bayansa yana ta karkashe su.
14 A wannan karo na farko Jonatan da mai ɗaukar makamansa suka kashe mutum wajen ashirin a wani fili mai fāɗi kamar rabin kadada.
15 Dukan Filistiyawan da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa.
16 Da matsara na Saul a Gibeya ta Biliyaminu suka duba, sai ga taron Filistiyawa ya watse, kowa ya nufi wajensa, suna tafiya barkatai.
17 Saul ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ƙidaya mutane yanzu don ku ga wanda ya fita daga cikinmu.” Da aka ƙirga mutanen sai aka tarar Jonatan da mai ɗaukar makamansa ba su nan.
18 Sai Saul ya ce wa Ahaija, “Kawo akwatin alkawarin Allah a nan.” Gama a wannan lokaci akwatin Allah yana hannun Isra’ilawa.
19 Sa’ad da Saul yake magana da firist ɗin, sai hargowa a sansanin Filistiyawa ta yi ta ƙaruwa, Saul kuwa ya ce wa firist, “Janye hannunka.”
20 Sa’an nan Saul da mutanen da suke tare da shi suka taru, suka tafi su yi yaƙi. Sai suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna ta yaƙi da junansu. Aka yi babbar yamutsewa.
21 Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi su zuwa sansani, suka koma wajen Isra’ilawan da suke tare da Saul da Jonatan.
22 Waɗanda kuma suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, da suka ji labari Filistiyawa suna gudu, suka fito suka fafare su.
23 Haka Ubangiji ya ceci Isra’ilawa a ranan nan. Yaƙin kuwa ya kai har gaba da Bet-awen.
Abin da Ya Faru bayan Yaƙin
24 A ran nan kuwa Isra’ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.
25-26 Da dukan mutane suka shiga kurmi, sai ga zuma ko’ina, amma ba wanda ya lakata da yatsa ya sa a baka, domin mutane suna tsoron la’anar Saul.
27 Amma Jonatan bai ji barazanar da mahaifinsa ya yi wa jama’a ba, sai ya lakaci saƙar zuma da kan sandansa ya sa a hannu ya kai baka, sa’an nan idanunsa suka buɗe.
28 Sai wani daga cikin jama’a ya ce, “Ai, mahaifinka ya yi wa mutane barazana da rantsuwa cewa, ‘La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana.’ ” Mutane kuwa suka tafke.
29 Jonatan kuwa ya ce, “Lalle mahaifina ya wahalar da jama’a! Dubi yadda na wartsake sa’ad da na ɗanɗana ‘yar zuman nan.
30 Da yaya zai zama yau da a ce mutane sun ci abinci sosai daga ganimar abokan gābansu, wadda suka samo! Ai, da kisan da aka yi wa Filistiyawa ya fi haka.”
31 Filistiyawa sun sha ɗibga a wannan rana, tun daga Mikmash har zuwa Ayalon. Isra’ilawa suka tafke da yunwa.
32 Sai suka yi warwason ganima, suka kwashe tumaki, da shanu, da maruƙa, suka yanyanka su, suka ci naman ɗanye.
33 Sai aka faɗa wa Saul, “Ga shi, mutane suna yi wa Ubangiji laifi, suna cin nama ɗanye.”
Saul kuwa ya ce, “Kun ci amana. Ku mirgino babban dutse a nan wurina.”
34 Sa’an nan ya ce, “Ku tafi ku faɗa wa jama’a duka, su kawo takarkarai da tumaki a nan, su yanyanka su, su ci a nan, don kada su yi wa Ubangiji zunubi da cin nama ɗanye.” Sai dukansu suka kawo takarkaransu a wannan dare, suka yanyanka a wurin.
35 Saul kuwa ya gina wa Ubangiji bagade. Shi ne bagade na farko da ya gina wa Ubangiji.
36 Sa’an nan Saul ya ce, “Mu tafi, mu fallasa Filistiyawa da dare har wayewar gari, kada ko mutum ɗaya daga cikinsu ya tsira.”
Sai suka ce masa, “Ka yi abin da ka ga ya yi maka kyau.” Amma firist ɗin ya ce, “Bari mu yi tambaya ga Allah.”
37 Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, ya ce, “In runtumi Filistiyawa? Za ka bashe su ga Isra’ilawa?” Amma Ubangiji bai amsa masa a wannan rana ba.
38 Sai Saul ya ce wa shugabanni, “Ku zo nan dukanku don mu bincike, mu san zunubin da aka yi a yau.
39 Hakika, duk wanda ya yi laifin za a kashe shi, ko da Jonatan ne, ɗana.” Amma ba wanda ya ce kome.
40 Ya kuma ce, “Dukanku ku tsaya waje ɗaya, ni kuma da Jonatan, ɗana, mu tsaya waje ɗaya.”
Sai jama’ar suka ce wa Saul, “Ka yi abin da ya yi maka kyau.”
41 Sa’an nan Saul ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, me ya sa ba ka amsa mini ba a wannan rana? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Jonatan, ya Ubangiji Allah na Isra’ila, ka nuna mana.” Sai amsa ta nuna Jonatan da Saul ne, jama’a kuwa suka kuɓuta.
42 Sa’an nan Saul ya ce, “A jefa kuri’a tsakanina da ɗana Jonatan.” Kuri’a kuwa ta fāɗa a kan Jonatan.
43 Sa’an nan Saul ya ce wa Jonatan, “Ka faɗa mini abin da ka yi!” Jonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana ‘yar zuma ne da na lakata da kan sandan da yake hannuna, ga ni, a shirye nake in mutu.”
44 Sai Saul ya ce, “Allah ya yi mini abin da ya fi haka, idan ba a kashe ka ba, Jonatan.”
45 Amma jama’a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra’ila, a ce za a kashe shi? Kai, a’a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba.
46 Sa’an nan Saul ya komo daga runtumar Filistiyawa, suka koma yankin ƙasarsu.
Mulkin Saul da Iyalinsa
47 Sa’ad da Saul ya ci sarautar Isra’ila, ya yi yaƙi da dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi. Ya yi yaƙi da Mowabawa da Ammonawa, da Edomawa, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya yi yaƙi ya sami nasara.
48 Ya yi aikin jaruntaka, ya bugi Amalekawa, ya ceci Isra’ilawa daga hannun dukan waɗanda suka taso musu.
49 ‘Ya’yan Saul, maza ke nan, Jonatan, da Yishwi, da Malkishuwa. Yana kuma da ‘ya’ya mata biyu, Merab, ‘yar fari, da Mikal.
50 Sunan matarsa kuwa Ahinowam ‘yar Ahimawaz. Sunan shugaban rundunansa kuwa Abner ne, ɗan Ner, kawunsa.
51 Kish mahaifin Saul, da Ner mahaifin Abner, ‘ya’yan Abiyel ne.
52 Saul ya yi ta yaƙi mai zafi da Filistiyawa dukan zamanin da yake sarauta. Idan Saul ya ga ƙaƙƙarfan mutum, ko jarumi, sai ya sa shi cikin sojansa.