An Keɓe Dawuda ya Zama Sarki
1 Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra’ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin ‘ya’yansa maza ya zama sarki.”
2 Sama’ila kuwa ya ce, “Ƙaƙa zan yi wannan? Gama idan Saul ya ji zai kashe ni.”
Sai Ubangiji ya ce, “Ka tafi da ɗan maraƙi, ka ce, ka zo ne ka miƙa wa Ubangiji hadaya.
3 Ka gayyaci Yesse zuwa wurin hadayar, zan nuna maka abin da za ka yi. Za ka zuba wa wanda na nuna maka mai.”
4 Sama’ila ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa, ya tafi Baitalami, inda dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Maigani, wannan ziyara lafiya kuwa?”
5 Ya ce, “I, lafiya lau. Na zo ne in miƙa wa Ubangiji hadaya, sai ku tsarkake kanku, ku zo mu tafi wurin yin hadaya tare.” Ya kuma sa Yesse da ‘ya’yansa maza su tsarkake kansu, su je wurin hadayar.
6 Da suka isa wurin hadayar, Sama’ila ya ga Eliyab, ɗan Yesse, sai ya zaci shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa.
7 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
8 Sa’an nan Yesse ya kira Abinadab ya wuce a gaban Sama’ila. Amma Sama’ila ya ce, “Ubangiji kuma bai zaɓi wannan ba.”
9 Sa’an nan Yesse ya sa Shimeya ya zo. Sama’ila kuma ya ce, “Ubangiji bai zaɓi wannan ba.”
10 Ta haka Yesse ya sa ‘ya’yansa maza, su bakwai, suka zo a gaban Sama’ila. Sama’ila kuwa ya ce wa Yesse, “Ubangiji bai zaɓi waɗannan ba.”
11 Sai ya tambayi Yesse, “Ko kana da sauran waɗansu ‘ya’ya maza?”
Yesse ya ce, “Da sauran autan, ga shi kuma, yana wurin kiwon tumaki.”
Sama’ila ya ce masa, “Sai ka aika a taho da shi, gama ba zan koma ba, sai ya zo.”
12 Yesse kuwa ya aika aka taho da shi. Ga shi kuwa kyakkyawa ne, idanunsa suna sheƙi. Sai Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Tashi ka zuba masa man keɓewa, shi ne sarkin.”
13 Sama’ila ya ɗauki man zaitun, ya zuba masa a gaban ‘yan’uwansa. Ruhun Ubangiji ya sauko da iko a kan Dawuda tun daga wannan rana zuwa gaba. Sama’ila kuwa ya tashi, ya koma Rama.
Dawuda Ya Kaɗa wa Saul Garaya
14 Yanzu kuwa Ruhun Ubangiji ya rabu da Saul, sai Ubangiji ya sa mugun ruhu ya azabtar da shi.
15 Barorin Saul kuwa suka ce masa, “To, ga shi yanzu, Ubangiji ya sa mugun ruhu na azabtar da kai.
16 Saboda haka muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo mutum gwanin kiɗan garaya, domin sa’ad da mugun ruhun nan da Allah ya sa maka, ya hau kanka, sai ya kaɗa maka garayar don ya sauka.”
17 Saul kuwa ya ce wa barorinsa. “To, sai ku samo mini mutum gwanin kiɗa, ku kawo mini shi.”
18 Sai wani daga cikin samarin ya amsa, ya ce, “Na san wani ɗan Yesse mutumin Baitalami. Shi gwanin kiɗan garaya ne, jarumi ne kuma, mayaƙi, mai lafazi, kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”
19 Sai Saul ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse, ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka, Dawuda, mai kiwon tumakinka.”
20 Yesse kuwa ya yi wa jaki labtu da abinci, da salkar ruwan inabi, da ɗan akuya, ya aiki Dawuda ɗansa, ya kai wa Saul.
21 Sa’an nan Dawuda ya zo wurin Saul, ya kama aiki. Saul kuwa ya ƙaunaci Dawuda ƙwarai, har Dawuda ya zama mai ɗaukar masa makamai.
22 Sa’an nan Saul ya aika wa Yesse cewa, “Ina so Dawuda. Ka bar shi ya zauna nan ya yi mini aiki.”
23 Tun daga ran nan zuwa gaba, a duk lokacin da mugun ruhun nan da Allah ya sa masa ya hau kansa, sai Dawuda ya ɗauki garaya, ya kaɗa masa. Sa’an nan mugun ruhun ya sauka, sai Saul ya wartsake.