Goliyat Yana Cakunar Isra’ilawa
1 Sai Filistiyawa suka tattaru a Soko ta Yahuza, suka kafa sansani a tsakanin Soko da Azeka, a Efes-dammim.
2 Saul kuma da mutanen Isra’ila suka tattaru, suka kafa sansani a kwarin Ila, suka jā dāga don su yi yaƙi da Filistiyawa.
3 Filistiyawa suka jeru a tudu guda, Isra’ilawa kuwa a ɗaya tudun. Kwari yana tsakaninsu.
4 Akwai wani jarumi, sunansa Goliyat, ya fito daga sansanin Filistiyawa. Tsayinsa kamu shida da rabi.
5 Yana sa kwalkwali na tagulla a kansa, yana kuma saye da sulke na tagulla wanda nauyinsa ya fi shekel dubu biyar (5,000).
6 Ya sa safa ta tagulla a ƙafafunsa, yana kuma da mashi na tagulla saɓe a kafaɗarsa.
7 Gorar mashinsa ta yi kama da dirkar masaƙa. Nauyin ruwan mashinsa na baƙin ƙarfe shekel ɗari shida ne. Mai ɗaukar masa garkuwa yana tafe a gabansa.
8 Goliyat ya ta da murya da ƙarfi, ya yi kira ga rundunar Isra’ila, ya ce, “Don me kuka fito ku jā dāgar yaƙi? Ai, ni Bafiliste ne, ku kuwa barorin Saul! Ku zaɓi mutum guda daga cikinku ya gangaro nan wurina.
9 Idan ya iya yaƙi da ni, ya kashe ni, to sai mu zama bayinku, amma idan na fi ƙarfinsa, na kashe shi, sai ku zama bayinmu, ku bauta mana.”
10 Ya ƙara da cewa, “Na raina rundunan Isra’ila yau. Ku ba ni mutumin da zan yi yaƙi da shi.”
11 Sa’ad da Saul da dukan Isra’ilawa suka ji maganganun da Bafilisten nan yake faɗa, sai suka karaya, suka tsorata ƙwarai.
Dawuda a Sansanin Saul
12 Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da ‘ya’ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul.
13 Manyan ‘ya’yansa maza uku sun tafi yaƙi tare da Saul. Sunan babban ɗan, Eliyab, na biye da shi kuma, Abinadab, na ukun kuwa Shimeya.
14 Dawuda shi ne auta. Sa’ad da manyan ‘yan’uwansa uku suka tafi tare da Saul wurin yaƙi,
15 Dawuda yakan koma Baitalami lokaci lokaci domin kiwon tumakin mahaifinsa.
16 Goliyat yana ta tsokanar Isra’ilawa safe da maraice, har kwana arba’in.
17 Wata rana ke nan, sai Yesse ya ce wa Dawuda, ɗansa, “Ka ɗauki wannan tumammen hatsi, da malmalar abinci goma, ka kai wa ‘yan’uwanka da sauri a sansanin.
18 Ga waɗannan dunƙulen cuku goma, ka kai wa shugaba na mutum dubu. Ka dubo lafiyar ‘yan’uwanka, ka kawo mini labari.
19 Da Saul, da ‘yan’uwanka, da dukan mazajen Isra’ila suna kwarin Ila, suna yaƙi da Filistiyawa.”
20 Kashegari sai Dawuda ya tashi tun da sassafe, ya bar tumaki a hannun wani makiyayi, ya ɗauki guzurin, ya tafi kamar yadda mahaifinsa, Yesse, ya umarce shi. Ya isa sansani daidai lokacin da runduna suke fita tana kirari na jān dāgar yaƙi.
21 Isra’ilawa da Filistiyawa suka jā dāga, runduna gāba da runduna.
22 Sai Dawuda ya bar abin da ya kawo a wurin mai jiran kaya, ya sheƙa zuwa bakin dāga domin ya gai da ‘yan’uwansa.
23 Sa’ad da yake magana da su, sai ga Goliyat, jarumin Filistiyawa na Gat, ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya yi maganganu irin na dā. Dawuda kuwa ya ji.
24 Sa’ad da dukan mazajen Isra’ila suka ga mutumin, suka guje masa saboda tsoro.
25 Suka ce, “Kun ga mutumin nan da ya fito? Lalle ya fito ne don ya nuna mana raini. Duk wanda ya kashe shi, sarki zai arzutar da shi, ya ba shi ‘yarsa aure, ya kuma ‘yantar da gidan mahaifinsa cikin Isra’ila.”
26 Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra’ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”
27 Mutane suka maimaita masa abin da sarki ya faɗa.
28 Lokacin da Dawuda yake magana da mutanen, sai Eliyab babban wansa ya ji, ya husata, ya ce wa Dawuda, “Me ya kawo ka nan? Wa ka bar wa ‘yan tumakin nan a jeji? Na san rigimarka da taurinkanka, ka zo ne don ka yi kallon yaƙi.”
29 Dawuda kuwa ya ce, “To, me kuma na yi, ba tambaya kawai na yi ba?”
30 Sai ya rabu da shi ya tafi wurin wani, ya sāke yin tambaya irin ta dā, mutane kuma suka ba shi amsa irin ta dā.
31 Sa’ad da waɗansu suka ji maganar da Dawuda ya yi, sai suka faɗa wa Saul. Shi kuwa ya aika a kira Dawuda.
32 Dawuda kuwa ya ce wa Saul, “Kada zuciyar kowa ta karai saboda wannan mutum, baranka zai tafi ya yi yaƙi da shi.”
33 Saul ya ce wa Dawuda, “Ba za ka iya yaƙi da wannan Bafiliste ba, gama kai ɗan saurayi ne, shi kuwa ya saba da yaƙi tun yana saurayi.”
34 Amma Dawuda ya ce wa Saul, “Ai, baranka makiyayin tumakin mahaifinsa ne, sa’ad da zaki ko beyar ya zo ya kama ɗan rago daga garken,
35 nakan bi shi in fāɗa masa, in ƙwato ɗan ragon daga bakinsa. Idan ya tasar mini da faɗa, sai in kama reronsa, in buge shi, in kashe shi.
36 Baranka ya taɓa kashe zaki da beyar, wannan arne zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, tun da yake ya raina rundunar Allah mai rai.
37 Ubangiji wanda ya cece ni daga dāgin zaki da na beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafiliste.”
Sa’an nan Saul ya ce wa Dawuda, “Tafi, Ubangiji ya taimake ka.”
38 Ya sa wa Dawuda kayan yaƙinsa, ya sa masa kwalkwalin tagulla a kansa, ya kuma sa masa sulke.
39 Da Dawuda ya sa kayan yaƙin, ya rataya takobi, ya fara tafiya, sai ya ji ba zai iya ba, domin bai saba da su ba. Sai ya ce wa Saul, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, gama ban saba da su ba.” Ya kuwa tuɓe su.
40 Sa’an nan ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya zuba a angararsa. Ya kuma riƙe majajjawarsa, ya tafi, ya fuskanci Bafilisten.
Dawuda Ya Kashe Goliyat
41 Bafilisten kuma ya nufo Dawuda, mai ɗaukar masa garkuwa yana gabansa.
42 Sa’ad da ya ga Dawuda, sai ya raine shi, gama Dawuda saurayi ne kawai, kyakkyawa.
43 Ya ce wa Dawuda, “Ni kare ne da za ka nufo da sanduna?” Ya zagi Dawuda da sunan allolinsu na Filistiyawa.
44 Ya kuma ce wa Dawuda, “Ya ka nan, ni kuwa in ba da namanka ga tsuntsayen sama da namomin jeji.”
45 Dawuda kuwa ya ce masa, “Kai, kana nufo ni da takobi, da mashi, da kēre, amma ni ina zuwa wurinka da sunan Ubangiji Mai Runduna, Allah na sojojin Isra’ila, wanda ka raina.
46 A yau Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan buge ka har ƙasa, in datse kanka, in ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namomin jeji, da haka duniya za ta sani lalle akwai Allah cikin Isra’ila.
47 Taron jama’ar nan kuma za su sani Ubangiji yakan yi ceto ba da takobi da mashi ba, gama yaƙi na Ubangiji ne, zai bashe ku a hannunmu.”
48 Goliyat kuwa ya fara gusowa ya gamu da Dawuda, sai Dawuda ya sheƙa zuwa bakin dāgar yaƙin don ya gamu da shi.
49 Sa’an nan Dawuda ya ɗauko dutse daga cikin angararsa, ya wurga, dutsen kuwa ya sami Goliyat a goshi, har ya lume. Goliyat kuwa ya faɗi rubda ciki.
50 Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara da Bafilisten. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.
51 Sa’an nan ya sheƙa zuwa wurin Bafilisten, ya zare takobin Bafilisten daga kubensa, ya datse masa kai da shi.
Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka gudu.
52 Mutanen Isra’ila da na Yahuza suka tashi suka runtumi Filistiyawa, suna ihu, har zuwa Gat da ƙofofin Ekron. Filistiyawan da aka yi wa rauni suka yi ta faɗuwa a hanya tun daga Shayarim, har zuwa Gat da Ekron.
53 Da Isra’ilawa suka komo daga runtumar Filistiyawa, suka wāshe sansanin Filistiyawa.
54 Dawuda kuwa ya ɗauki kan Bafilisten ya kawo Urushalima, amma ya ajiye kayan yaƙin Bafilisten a alfarwarsa.
An Kai Dawuda wurin Saul
55 Sa’ad da Saul ya ga Dawuda ya tafi ya yi yaƙi da Goliyat, ya ce wa Abner, sarkin yaƙinsa, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?”
Abner ya amsa, ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, ban sani ba.”
56 Sai ya ce, “Ka tambaya mini, wane ne uban saurayin nan.”
57 Da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai Abner ya kai shi wurin Saul, Dawuda yana ɗauke da kan Bafilisten.
58 Saul ya tambayi Dawuda, ya ce, “Saurayi, kai ɗan wane ne?”
Dawuda ya amsa, ya ce, “Ni ɗan baranka ne, Yesse, mutumin Baitalami.”