Alkawarin Jonatan da Dawuda
1 Da Dawuda ya gama magana da Saul, sai zuciyar Jonatan ta saje da ran Dawuda. Jonatan kuwa ya ƙaunaci Dawuda kamar kansa.
2 Daga ran nan Saul ya riƙe Dawuda, bai bari Dawuda ya koma gidan mahaifinsa ba.
3 Jonatan kuma ya yi dawwamammen alkawari da Dawuda, domin shi, wato Jonatan, yana ƙaunar Dawuda kamar kansa.
4 Sai ya tuɓe rigarsa ya ba Dawuda, ya kuma ba shi jabbarsa, da takobinsa, da bakansa, da abin ɗamararsa.
5 Duk inda Saul ya aiki Dawuda, sai ya tafi, ya kuma ci nasara. Saboda haka Saul ya maishe shi shugaban sojoji. Dukan jama’a da barorin Saul kuma suka ji daɗi.
Saul Yana Kishin Dawuda
6 Sa’ad da sojoji suke komowa gida, bayan da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai mata daga kowane gari na Isra’ila suka fito domin su taryi sarki Saul. Suna raira waƙar farin ciki, suna rawa, suna kaɗa kuwaru da molaye.
7 Suka raira waƙa, suna cewa, “Saul ya kashe dubbai, amma Dawuda ya kashe dubun dubbai.”
8 Wannan waƙa ta ba Saul haushi, ya ce, “Sun ba Dawuda dubun dubbai, amma dubbai kawai suka ba ni, me kuma ya rage masa, ai, sai sarauta.”
9 Tun daga wannan rana Saul ya fara kishin Dawuda.
10 Kashegari Allah ya sa mugun ruhu ya sauka a kan Saul, sai ya yi ta maganganu a gidansa kamar mahaukaci, sai Dawuda ya yi ta kaɗa masa garaya kamar yadda ya saba yi. Saul kuwa yana riƙe da mashi.
11 Yana cewa a ransa, “Zan nashe shi in kafe shi da bango.” Sau biyu yana cakar Dawuda da mashi, amma Dawuda ya goce.
12 Saul ya ji tsoron Dawuda, gama Ubangiji yana tare da Dawuda, amma ya rabu da Saul.
13 Saboda haka Saul bai yarda Dawuda ya zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban dubu. Shi kuwa ya riƙa bi da su cikin kai da kawowa.
14 Dawuda kuwa ya yi ta yin nasara cikin ayyukansa duka, domin Ubangiji yana tare da shi.
15 Da Saul ya ga Dawuda yana yin nasara, sai ya ƙara jin tsoronsa.
16 Dukan mutanen Isra’ila da na Yahuza suka ƙaunaci Dawuda, domin yana kai da kawowa a cikinsu.
Dawuda Ya Auri ‘Yar Saul
17 Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ga Merab babbar ‘yata, zan ba ka ita ka aura, idan ka yi mini aikin jaruntaka, wato ka yi yaƙin Ubangiji.” (Gama Saul yana tsammani ta wannan hanya Filistiyawa za su kashe Dawuda, ba lalle sai shi da kansa ya kashe shi ba.)
18 Dawuda, ya ce wa Saul, “Wane ni ko iyalin mahaifina a cikin Isra’ila, har da zan zama surukin sarki?”
19 Amma sa’ad da lokaci ya yi da za a ba Dawuda Merab, ‘yar Saul, ya aura, sai aka aurar da ita ga Adriyel, mutumin Abel-mehola.
20 Mikal, ‘yar Saul kuwa, ta ƙaunaci Dawuda, sai aka faɗa wa Saul, shi kuwa ya yarda da haka.
21 Ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan ba shi ita don ta zamar masa sanadin da zai mutu ta hannun Filistiyawa.” Don haka sai Saul ya ce wa Dawuda a karo na biyu, “Yanzu dai za ka zama surukina.”
22 Sai Saul ya umarci fādawansa, ya ce, “Ku yi magana da Dawuda a ɓoye, ku ce masa, ‘Ga shi, sarki yana jin daɗinka, dukan fādawansa kuma suna ƙaunarka, yanzu sai ka zama surukin sarki.’ ”
23 Fādawan Saul kuwa suka faɗa wa Dawuda wannan magana. Sai Dawuda ya ce, “Zama surukin sarki ƙaramin abu ne a ganinku? Ga shi, ni talaka ne wanda ba sananne ba.”
24 Fādawan suka faɗa wa Saul abin da Dawuda ya faɗa.
25 Saul kuma ya ce, “Haka za ku faɗa wa Dawuda, ‘Sarki ba ya so ka ba da sadaki don auren, sai dai ka ba da loɓar Filistiyawa guda ɗari, domin ka ɗauki fansa a kan maƙiyan sarki.’ ” (Saul dai yana so Filistiyawa su kashe Dawuda kawai.)
26-27 Da fādawan suka faɗa wa Dawuda abin da Saul ya ce, sai Dawuda ya ji daɗi ƙwarai ya zama surukin sarki. Kafin lokacin da aka yanka masa ya yi, sai Dawuda ya tashi, ya tafi tare da mutanensa, suka kashe Filistiyawa ɗari biyu. Ya kawo loɓarsu duka, aka ba sarki, domin ya zama surukin sarki. Saul kuwa ya aurar da Mikal, ‘yarsa, ga Dawuda.
28-29 Da Saul ya gane lalle Ubangiji yana tare da Dawuda, Mikal ‘yarsa kuma tana ƙaunar Dawuda, sai ya ƙara jin tsoronsa, ya maishe shi maƙiyinsa na din din din.
30 Sarakunan Filistiyawa sukan zo da yaƙi. Idan sun zo, sai Dawuda ya yi nasara da su fiye da sauran shugabannin yaƙi na Saul. Wannan ya sa ya yi suna.