Dawuda Ya Gudu daga wurin Saul
1 Sa’an nan Dawuda ya tafi wurin Ahimelek, firist, a Nob. Ahimelek kuwa ya fita da rawar jiki domin ya tarye Dawuda, ya ce masa, “Me ya sa kake kai kaɗai, ba wani tare da kai ba?”
2 Dawuda ya ce masa, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya aiko ni in yi. Jama’ata kuwa na riga na shirya inda zan sadu da su.
3 Yanzu me kake da shi? Sai ka ba ni abinci malmala biyar ko wani abu da kake da shi a nan.”
4 Firist ɗan ya ce wa Dawuda, “Ba ni da abinci don kowa da kowa, sai dai gurasa ta ajiyewa. Zan iya in ba ka muddin dai samarin sun keɓe kansu daga mata.”
5 Dawuda ya ce masa, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena suka keɓe kansu a koyaushe suka tashi ‘yar tafiya, balle fa yanzu da muka fito yin wani abu musamman.”
6 Firist ɗin kuwa ya ba Dawuda tsattsarkan abinci na ajiya, gama ba wani abinci a wurin, sai gurasar ajiyewa kaɗai wadda akan kawar, a sāke sa wata mai ɗumi a ranar da aka kawar da ita.
7 A ranar kuwa akwai wani mutum daga cikin barorin Saul, wanda aka tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom ne. Shi ne shugaban masu kiwon garkunan Saul.
8 Dawuda kuwa ya ce wa Ahimelek, “Kana da mashi ko takobi a nan kusa? Gama ban zo da takobina ko wani makami ba, domin ka sani sha’anin sarki na gaggawa ne.”
9 Firist ya ce, “Ga takobin Goliyat, Bafiliste wanda ka kashe a kwarin Ila, a naɗe da zane a bayan falmaran. Idan kana so ka ɗauka, sai ka ɗauka, gama banda shi, ba wani takobi a nan.”
Dawuda kuwa ya ce, “Ai, ba wanda ya fi wannan, sai ka ba ni shi.”
10 Sai Dawuda ya tashi, yana gudu ke nan daga wurin Saul. Ya tafi wurin Akish, Sarkin Gat.
11 Fādawan Akish kuwa suka ce masa, “Ashe, wannan ba shi ne Dawuda, sarkin ƙasar ba? Ba a kansa suka raira waƙa cikin raye-rayensu suna cewa, ‘Saul ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai’?”
12 Da Dawuda ya ji waɗannan maganganu, sai ya tsorata ƙwarai da Akish Sarkin Gat.
13 Ya mai da kansa kamar mahaukaci a gabansa. Ya yi zane-zane a ƙyamaren ƙofofin garin. Ya bar yau na bin gemunsa.
14 Akish kuwa ya ce wa fādawansa, “Ashe, mutumin mahaukaci ne? Don me kuka kawo shi wurina?
15 Na rasa mahaukata ne da za ku kawo mini wannan mutum ya yi ta hauka a gabana? Wannan mutum ne zai shiga gidana?”