Ubangiji Ya Kira Sama’ila
1 Yaron nan Sama’ila yana yi wa Ubangiji aiki a hannun Eli. A lokacin nan Ubangiji bai cika yin magana da mutane ba, ba safai kuma ake samun wahayi ba.
2 Wata rana da dare Eli wanda ya kusa makancewa har ba ya iya gani sosai, yana kwance a masujada.
3 Fitilar Ubangiji kuwa tana ci. Sama’ila kuma yana kwance a masujada inda akwatin alkawarin Allah yake.
4 Ubangiji kuwa ya kira Sama’ila. Sama’ila ya ce, “Na’am.”
5 Ya sheƙa zuwa wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”
Amma Eli ya ce masa, “Ban kira ka ba, koma ka kwanta.” Sai Sama’ila ya koma ya kwanta.
6 Ubangiji ya sāke kiran Sama’ila. Sama’ila ya tashi ya tafi wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”
Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”
7 (Sama’ila dai bai san Ubangiji ba tukuna, gama Ubangiji bai riga ya fara magana da shi ba.)
8 Ubangiji kuma ya kira Sama’ila sau na uku. Sai kuma Sama’ila ya tashi ya nufi Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”
Sa’an nan Eli ya gane Ubangiji ne yake kiran yaron,
9 saboda haka Eli ya ce wa Sama’ila ya koma ya kwanta, idan an sāke kiransa sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.” Sama’ila kuwa ya koma ya kwanta.
10 Ubangiji kuma ya zo ya tsaya, ya yi kira kamar dā, ya ce, “Sama’ila! Sama’ila!”
Sama’ila ya amsa ya ce, “Ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.”
11 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Zan yi wa Isra’ilawa wani abu, duk wanda ya ji kuwa zai razana.
12 A ranar zan cika abin da na faɗa game da Eli da iyalinsa daga farko har zuwa ƙarshe.
13 Na fāɗa masa zan hukunta gidansa har abada saboda ‘ya’yansa sun faɗi mugayen maganganu a kaina. Eli kuwa ya sani, amma bai kwaɓe su ba.
14 Domin haka na faɗa da ƙarfi, cewa laifin gidan Eli ba za a yi kafararsa da sadaka, ko da hadaya ba har abada.”
15 Sama’ila ya kwanta har safiya, sa’an nan ya buɗe ƙofofi. Amma ya ji tsoron faɗa wa Eli wahayin.
16 Amma Eli ya kira shi, ya ce, “Ya ɗana, Sama’ila.”
Sama’ila ya ce, “Ga ni.”
17 Eli ya tambaye shi, ya ce, “Me Ubangiji ya faɗa maka? Kada ka ɓoye mini. Allah zai hukunta ka idan ka ɓoye mini abin da ya faɗa maka.”
18 Sama’ila kuwa ya faɗa masa kome da kome, bai ɓoye masa kome ba. Sai Eli ya ce, “Ai, Ubangiji ne, bari ya yi abin da ya yi masa daidai.”
19 Sama’ila fa ya yi girma, Ubangiji yana tare da shi. Dukan maganarsa kuwa Ubangiji yana cika ta.
20 Dukan mutanen Isra’ila fa daga wannan kusurwar ƙasa zuwa wancan, sun tabbata Sama’ila annabin Ubangiji ne.
21 Ubangiji kuma ya yi ta bayyana a Shilo inda ya bayyana kansa ga Sama’ila, ya kuma yi magana da shi. Duk lokacin da Sama’ila ya yi magana dukan mutanen Isra’ila suna kasa kunne.