Dawuda da Bat-Sheba
1 Da bazara lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, Dawuda ya aiki Yowab, da shugabannin sojojinsa, da sojojin Isra’ila duka. Suka tafi suka ragargaza Ammonawa, suka kuma kewaya Rabba da yaƙi. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.
2 Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka.
3 Sai ya aika a bincika ko wace ce wannan mata, ashe, ‘yar Ammiyel ce, matar Uriya Bahitte.
4 Dawuda kuwa ya aiki waɗansu manzanni suka kawo masa ita, ya kwana da ita. (A lokacin kuwa ta gama wankan haila ke nan.) Sa’an nan ta koma gidanta.
5 Matar kuwa ta yi juna biyu, sai ta aika a faɗa wa Dawuda, cewa, tana da ciki.
6 Dawuda kuwa ya aika wurin Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya Bahitte.” Yowab kuwa ya aika da Uriya wurin Dawuda.
7 Da Uriya ya iso, sai Dawuda ya tambaye shi labarin Yowab, da lafiyar jama’ar, da labarin yaƙin.
8 Ya kuma ce masa, “Ka tafi gidanka, ka wanke ƙafafunka.” Da Uriya ya fita daga gidan sarki, sarki ya ba da kyauta a kai masa.
9 Amma Uriya bai tafi gidansa ba, sai ya kwana a ƙofar gidan sarki tare da sauran barorin sarki.
10 Da aka faɗa wa Dawuda, cewa, Uriya bai tafi gidansa ba, Dawuda ya kira Uriya ya ce masa, “Ka dawo daga tafiya, me ya sa ba ka tafi gidanka ba?”
11 Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin alkawari, da mutanen Isra’ila, da na Yahuza, suna zaune a bukkoki. Shuganana Yowab, da barorinsa suna zaune a sansani a karkara, ƙaƙa ni zan tafi gidana in ci in sha, in kwanta da matata? Na rantse da ranka, ba zan yi haka ba.”
12 Dawuda kuma ya ce wa Uriya, “Ka kwana nan kuma yau, gobe in sallame ka.” Sai Uriya ya kwana a Urushalima a ran nan.
13 Kashegari kuma Dawuda ya kira shi liyafa. Ya zo, ya ci ya sha tare da shi, har Dawuda ya sa shi ya bugu. Amma da dare, sai ya tafi ya kwanta a shimfiɗarsa tare da sauran barorin sarki, amma bai tafi gidansa ba.
14 Da safe Dawuda ya rubuta wasiƙa, ya ba Uriya ya kai wa Yowab.
15 A wasiƙar ya ce wa Yowab, “Tura Uriya a gaba a inda yaƙin ya fi zafi, sa’an nan ku ja da baya, ku bar shi don a buge shi a kashe shi.”
16 Sa’ad da Yowab yake kama garin da yaƙi, sai ya sa Uriya a inda ya sani akwai jarumawan gaske.
17 Mutanen garin suka fito suka yi yaƙi da Yowab. Suka kashe waɗansu daga cikin sojojin Dawuda. Uriya Bahitte, shi ma aka kashe shi.
18 Sai Yowab ya aika aka faɗa wa Dawuda labarin yaƙin.
19-20 Ya ce wa manzo, “Bayan da ka gama faɗa wa sarki labarin yaƙin duka, idan sarki ya husata, har ya ce maka, ‘Me ya sa kuka tafi yaƙi kurkusa da garin? Ba ku sani ba za su tsaya a gefen garu daga ciki su yi harbi?
21 Wa ya kashe Abimelek ɗan Yerubba’al? Ba mace ce a TebEze ta jefe shi da ɗan dutsen niƙa ta kan garu daga ciki ta kashe shi ba? Me ya sa kuka tafi kusa da garu?’ Sai ka faɗa masa cewa, ‘Baranka, Uriya Bahitte, shi ma an kashe shi.’ ”
22 Manzon kuwa ya tafi ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Yowab ya ce.
23 Ya ce, “Abokan gābanmu sun sami sa’a a kanmu. Sun fito su gabza da mu a karkara, amma muka kore su zuwa cikin ƙofar garin.
24 Sai maharba suka tsaya a kan garu daga ciki suka yi ta harbin barorinka. Waɗansu daga cikin barorin sarki sun mutu. Baranka Uriya Bahitte shi ma ya matu.”
25 Dawuda ya ce wa manzon, “Je ka ka faɗa wa Yowab kada wannan abu ya dame shi, ai, takobi ba ya tarar wanda zai kashe. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku faɗa masa har ku ragargaza shi. Ka ƙarfafa Yowab.”
26 Sa’ad da matar Uriya ta ji labarin mutuwar mijinta, ta yi makoki dominsa.
27 Da kwanakin makokin suka ƙare, sai Dawuda ya aika aka kawo ta gidansa, ta zama matarsa, ta haifa masa ɗa. Amma Ubangiji bai ji daɗin mugun abin nan da Dawuda ya yi ba.