Natan Ya Tsauta wa Dawuda
1 Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.
2 Basaraken yana da garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu.
3 Amma talakan ba shi da kome sai ‘yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi renonta, ta yi girma a wurinsa, tare da ‘ya’yansa. Takan ci daga cikin ɗan abincinsa, ta kuma sha daga cikin abin shansa, ta kwanta a ƙirjinsa. Ta zama kamar ‘ya a gare shi.
4 Wata rana basaraken ya yi baƙo, amma bai yarda ya kamo daga cikin garkensa ya yanka wa baƙon ba, sai ya kamo ‘yar tunkiyar talakan nan, matalauci, ya yanka wa baƙon da ya zo wurinsa.”
5 Dawuda ya husata ƙwarai a kan mutumin, ya ce wa Natan, “Hakika mutumin da ya yi haka ya cancanci mutuwa.
6 Sai kuma ya biya diyyar ‘yar tunkiya riɓi huɗu, domin ya aikata mugun abu na rashin tausayi.”
7 Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin. In ji Ubangiji Allah na Isra’ila, ‘Na naɗa ka Sarkin Isra’ila, na cece ka daga hannun Saul.
8 Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra’ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka.
9 Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka.
10 Domin haka takobi ba zai rabu da gidanka ba, domin ka raina ni, ka ɗauki matar Uriya Bahitte ta zama matarka.
11 Na rantse zan sa wani daga cikin iyalinka ya far maka da tashin hankali. A idonka zan ba da matanka ga wani mutum. Zai kwana da su da rana katā.
12 Kai, a ɓoye ka yi naka zunubi, amma zan sa a yi maka a gaban dukan mutanen Isra’ila da rana katā.’ ”
13 Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”
Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.
14 Amma domin ka ba da ƙofa ga magabtan Ubangiji su zarge shi, wato saboda abin da ka aikata, ɗan da za a haifa maka zai mutu.”
15 Sa’an nan Natan ya tafi gida.
Ɗan Dawuda Ya Mutu, aka Haifi Sulemanu
Ubangiji kuwa ya sa ciwo ya kama yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda.
16 Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare.
17 Sai fādawansa suka zo suka kewaye shi, don su tashe shi daga ƙasa, amma bai yarda ba, bai kuma ci abinci tare da su ba.
18 An kwana bakwai sai yaron ya mutu. Fādawansa suka ji tsoron faɗa masa rasuwar yaron. Suka ce wa junansu, “Ga shi, tun lokacin da yaron yake da rai mun yi masa magana, amma bai kasa kunne gare mu ba, yaya za mu iya faɗa masa rasuwar yaron? Zai yi wa kansa ɓarna.”
19 Da Dawuda ya ga fādawansa suna raɗa da juna, sai ya gane lalle yaron ya rasu. Ya tambaye su, ya ce, “Yaron ya rasu ne?”
Suka amsa cewa, “I, ya rasu.”
20 Sai Dawuda ya tashi daga ƙasa, ya yi wanka, ya shafa mai, ya sake tufafinsa, ya tafi ɗakin sujada, ya yi sujada, sa’an nan ya koma gidansa ya ce a kawo abinci. Suka kawo masa abinci ya ci.
21 Fādawansa suka ce masa, “Me ka yi ke nan? Ka yi azumi, ka yi kuka saboda yaron tun yana da rai, amma da yaron ya rasu ka tashi, ka ci abinci.”
22 Ya ce musu, “Tun yaron yana da rai, na yi azumi da kuka, ina cewa wa ya sani, ko Ubangiji zai yi mini jinƙai, ya bar yaron da rai?
23 Amma yanzu ya rasu, me zai sa kuma in yi azumi? Zan iya koma da shi ne? Ni zan tafi wurinsa, amma shi ba zai komo wurina ba.”
24 Sa’an nan Dawuda ya yi wa Batsheba, matarsa, ta’aziyya. Ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Ta haifa masa ɗa. Ya raɗa masa suna Sulemanu. Ubangiji kuwa ya ƙaunace shi,
25 ya kuma umarci annabi Natan ya raɗa wa yaron suna Yedideya, wato ƙaunataccen Ubangiji.
Dawuda ya ci Rabba da Yaƙi
26 Yowab kuwa ya yi yaƙi da Rabba ta Ammonawa, yana kuwa gab da cin birnin.
27 Sai ya aiki manzanni wurin Dawuda ya ce, “Na yaƙi Rabba, na kama hanyar samun ruwansu.
28 Yanzu ka tara sauran sojoji ka fāɗa wa birnin, ka ci shi da kanka. Gama ba na so in yi suna da cin birnin.”
29 Saboda haka sai Dawuda ya tara sauran sojoji duka, ya tafi Rabba, ya yi yaƙi da ita, ya kuwa ci birnin.
30 Sarkinsu, wato Milkom, yana da kambi na zinariya a kansa, nauyinsa ya kai talanti ɗaya na zinariya yana kuma da duwatsu masu daraja cikinsa. Dawuda kuwa ya ɗauke kambin daga kan sarkin ya sa a nasa. Sa’an nan ya kwaso ganima mai ɗumbun yawa daga cikin birnin.
31 Ya kuma kamo mutanen da suke cikin birnin, ya sa su su yi aiki da zartuka, da faretani, da gatura. Ya kuma sa su yi tubula. Haka Dawuda ya yi da dukan biranen Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan sojojinsa suka koma Urushalima.