Amnon da Tamar
1 Absalom, ɗan Dawuda, yana da kyakkyawar ƙanwa, sunanta Tamar. Ana nan Amnon ɗaya daga cikin ‘ya’yan Dawuda, ya ƙaunace ta.
2 Amnon ya matsu har ya fara ciwo saboda Tamar ƙanwarsa. Ita kuwa budurwa ce, ba shi yiwuwa Amnon ya yi wani abu da ita.
3 Amma Amnon yana abuta da Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda. Yonadab kuwa yana da hila.
4 Sai ya ce masa, “Ya ɗan sarki, me ya sa kake damuwa kowace rana? Ba za ka faɗa mini ba?”
Sai Amnon ya ce masa, “Na jarabtu ne da Tamar ƙanwar ɗan’uwana Absalom.”
5 Yonadab kuwa ya ce masa, “Kwanta a gadonka ka yi kamar kana ciwo, lokacin da mahaifinka ya zo domin ya duba ka, sai ka ce masa, ‘A bar ƙanwata Tamar ta zo ta ba ni abinci, ta riƙa shirya abincin a idona, don in gani in kuma riƙa ci daga hannunta.’ ”
6 Amnon kuwa ya kwanta, ya yi kamar yana ciwo.
Sa’ad da sarki ya zo duba shi, sai Amnon ya ce wa sarki, “Ina roƙo a sa ƙanwata, Tamar, ta zo ta toya mini waina a inda nake, ta riƙa ba ni da hannunta ina ci.”
7 Sai Dawuda ya aika gida, wurin Tamar, ya ce, “Tafi gidan Amnon wanki, ki shirya masa abinci.”
8 Tamar kuwa ta tafi gidan wanta Amnon, inda yake kwance. Sai ta ɗauki ƙullu, ta cuɗa, ta toya waina a idonsa.
9 Ta juye wainar daga kaskon yana gani, amma ya ƙi ci. Ya ce wa waɗanda suke cikin ɗakin su fita. Su kuwa suka fita.
10 Sa’an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a cikin ɗakin kwanana, ki riƙe mini in ci.” Sai ta ɗauki wainar da ta yi, ta kai wa Amnon, wanta, a ɗakin kwana.
11 Amma da ta kawo kusa da shi don ya ci, ya kama ta, ya ce, “Zo in kwana da ke ƙanwata.”
12 Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra’ila, kada ka yi halin dabba.
13 Ni kuwa ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuwa za ka zama ɗaya daga cikin riƙaƙƙun sakarkarin mutane na cikin Isra’ila. Ina roƙonka ka yi magana da sarki, gama ba zai hana ka ka aure ni ba.”
14 Amma Amnon bai ji maganarta ba. Da yake ya fi ta ƙarfi, sai ya yi mata faɗe.
15 Bayan haka sai Amnon ya ƙi ta da mummunar ƙiyayya, har ƙiyayyar ta fi yawan ƙaunar da ya yi mata. Ya ce mata, “Tashi, ki fita.”
16 Sai ta ce masa, “A’a wana, muguntar koran nan da kake yi mini, ta fi ta wadda ka riga ka yi mini.”
Amma bai kasa kunne gare ta ba.
17 Sai ya kira baran da yake yi masa hidima, ya ce, “Fitar da matan nan daga gabana, ka rufe ƙofa.”
18 Tamar kuwa tana saye da doguwar riga mai hannuwa, gama haka gimbiyoyi budurwai suke ado. Baran Amnon kuwa ya fitar da ita, ya kulle ƙofar.
19 Tamar ta baɗe kanta da toka, ta keta doguwar rigarta mai hannuwa wadda ta sa, ta rufe fuska da hannu, ta tafi tana ta kuka da ƙarfi.
20 Absalom wanta ya tambaye ta, ya ce, “Ko Amnon wanki ya ɓata ki? To, yi shiru, ƙanwata, shi wanki ne, kada ki damu da yawa.” Tamar kuwa ta zauna a kaɗaice a gidan Absalom wanta.
21 Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai.
22 Amma Absalom bai tanka wa Amnon da wata magana ta alheri ko ta mugunta ba, gama yana ƙin Amnon saboda ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.
Absalom Ya Rama Ya Gudu
23 Bayan shekara biyu cif, sai Absalom ya sa a yi masa sausayar tumaki a Ba’al-hazor, wadda take kusa da Ifraimu. Ya kuma gayyaci dukan ‘yan’uwansa, wato ‘yan sarki.
24 Ya kuma tafi wurin sarki, ya ce masa, “Ranka ya daɗe, ga shi, ina sausayar tumakina, ina roƙonka, ka zo, kai da fādawanka tare da ni.”
25 Amma sarki ya ce wa Absalom, “A’a ɗana, ba ma tafi duka ba, don kada mu nawaita maka.” Absalom ya dāge cewa, sai sarki ya je, amma duk da haka sarki bai tafi ba, sai dai ya sa masa albarka.
26 Sa’an nan Absalom ya ce, “Idan ba za ka tafi ba, ina roƙonka ka bar Amnon ɗan’uwana ya tafi tare da mu.”
Sarki ya ce, “Don me zai tafi tare da kai?”
27 Amma Absalom ya dāge har sarki ya yarda. Amnon da dukan ‘ya’yan sarki suka tafi tare da shi.
28 Absalom ya umarci barorinsa, ya ce, “Ku lura sa’ad da Amnon ya bugu da ruwan inabi, in na ce, ‘Bugi Amnon’, sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro, gama ni na umarce ku, sai dai ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka.”
29 Haka kuwa barorin Absalom suka kashe Amnon yadda Absalom ya umarta. Sauran ‘ya’yan sarki kuwa suka tashi, kowa ya hau alfadarinsa, ya gudu.
30 Sa’ad da suke kan hanya labari ya kai kunnen Dawuda. Aka ce, “Absalom ya kashe dukan ‘ya’yan sarki, ba wanda ya tsira daga cikinsu.”
31 Sai sarki ya tashi ya keta rigunansa, ya kwanta a ƙasa. Dukan barorinsa kuma da suke tsaye a wurin suka kyakketa rigunansu.
32 Amma Yonadab, ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda, ya ce, “Ranka ya daɗe, ba fa dukan ‘ya’yan sarki aka kashe ba. Amnon ne kaɗai aka kashe ta umarnin Absalom, gama ya ƙudura wannan tun daga ranar da Amnon ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.
33 Don haka, kada shugabana sarki ya damu, cewa, an kashe dukan ‘ya’yan sarki, gama Amnon ne kaɗai aka kashe.”
34 Absalom kuwa ya gudu.
Sa’an nan sojan da yake tsaro a wannan lokaci ya ga ɗumbun mutane suna tahowa daga hanyar Horonayim, wajen gefen dutse.
35 Sai Yonadab ya ce wa sarki, “Waɗannan ‘ya’yan sarki ne yake zuwa, kamar yadda na faɗa.”
36 Yana gama magana ke nan, sai ga ‘ya’yan sarki sun iso. Suka yi ta kuka da ƙarfi. Sarki kuma da dukan fādawansa suka yi kuka mai tsanani.
37 Amma Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai, ɗan Ammihud, Sarkin Geshur. Dawuda kuwa ya yi makokin Amnon ɗansa kwana da kwanaki.
38 Absalom ya shekara uku a Geshur.
39 Sai zuciyar sarki ta koma kan Absalom, gama ya haƙura a kan Amnon da yake ya riga ya rasu.