Dawuda da Ziba
1 Sa’ad da Dawuda ya wuce ƙwanƙolin dutsen kaɗan, sai ga Ziba baran Mefiboshet ya sadu da shi. Ya zo da jaki biyu ya yi musu labtu da gurasa dunƙule ɗari biyu, da zabibi ɗari, da sababbin ‘ya’yan itace guda ɗari, da salkar ruwan inabi.
2 Sarki kuwa ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo abubuwan nan?”
Ziba ya amsa, ya ce, “An kawo wa iyalin sarki jakuna su hau, da abinci, da ‘ya’yan itace, domin samari su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suke rafkewa a jejin su sha.”
3 Sarki kuma ya tambaye shi, “Ina ɗan ubangijinka?”
Sai Ziba ya ce, “Yana zaune a Urushalima, yana cewa, ‘Yanzu dai mutanen gidan Isra’ila za su mayar mini da sarautar tsohona.’ ”
4 Da jin haka sai sarki ya ce wa Ziba, “Dukan abin da yake na Mefiboshet ya zama naka.”
Ziba kuma ya rusuna ya yi godiya ya ce, “Bari in zama majidaɗin ubangijina, sarki.”
Dawuda da Shimai
5 Sa’ad da Dawuda ya kai Bahurim, sai ga wani mutum sunansa Shimai, ɗan Gera, daga iyalin gidan Saul, ya fito yana ta zagi.
6 Ya jajjefi Dawuda da fādawansa da duwatsu, da sauran jama’a, da dukan jarumawan da suke kewaye da shi.
7 Shimai ya yi ta zagi, yana cewa, “Tafi, tafi, kai mai kisankai, sakarai.
8 Ubangiji ya sāka maka saboda alhakin jinin gidan Saul, wanda ka hau gadon sarautarsa. Yanzu Ubangiji ya ba da sarautar ga Absalom, ɗanka. Duba, masifa ta auko maka, gama kai mai kisankai ne.”
9 Sai Abishai, ɗan Zeruya, ya ce wa sarki, “Ranka ya daɗe, don me za ka bar wannan kare yana ta zaginka? Bari in tafi in fille masa kai.”
10 Amma sarki ya ce masa, “Ba ruwanku, ku ‘ya’yan Zeruya. Idan yana zagi saboda Ubangiji ya sa shi, to, wa ya isa ya ce, ‘Don me kake yin haka?’ ”
11 Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi.
12 Watakila Ubangiji zai dubi azabata, ya sāka mini da alheri saboda wannan zagin da aka yi mini yau.”
13 Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu. Shimai kuwa yana biye da su ta gefen dutse, yana tafe, yana ta zagi, yana jifarsa da duwatsu, yana masa ature.
14 Sarki da dukan jama’ar da suke tare da shi suka isa Urdun a rafke. Sai suka shaƙata.
Absalom a Urushalima
15 Absalom kuwa ya zo Urushalima tare da dukan mutanen Isra’ila da suke tare da shi. Ahitofel kuma yana tare da shi.
16 Sa’ad da Hushai Ba’arkite, aminin Dawuda ya zo wurin Absalom, ya ce masa, “Ran sarki ya daɗe!”
17 Sai Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake yi wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”
18 Hushai ya amsa, ya ce, “Ba haka ba, ni dai zan zama na wanda Ubangiji, da wannan jama’a, dukan mutanen Isra’ila suka zaɓa. Zan zauna tare da mutumin da aka zaɓa.
19 Banda haka ma, wane ne ya kamata in bauta wa, in ba ɗan ubangidana ba? Kamar yadda na bauta wa tsohonka, haka kuma zan bauta maka.”
20 Sa’an nan Absalom ya juya wajen Ahitofel, ya ce, “To, ka kawo shawararka a kan abin da ya kamata mu yi?”
21 Ahitofel kuwa ya ce wa Absalom, “Ka shiga ka kwana, da ƙwarakwaran tsohonka waɗanda ya bar su su lura da gidan. Dukan Isra’ilawa za su sani ba shiri kuma tsakaninka da tsohonka. Dukan masu goyon bayanka kuma za su ƙara ƙarfafa.”
22 Sai suka kafa wa Absalom alfarwa a bisa kan soro, ya shiga ya kwana da ƙwaraƙwaran tsohonsa, a idon mutanen Isra’ila duka.
23 Shawarar da Ahitofel yake bayarwa a lokacin nan ta zama kamar faɗar Allah ce. Absalom duk da Dawuda, shawarar Ahitofel suke bi.