Tawayen Sheba
1 Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra’ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.”
2 Sai dukan Isra’ilawa suka janye jiki daga wurin Dawuda, suka bi Sheba, ɗan Bikri, amma mutanen Yahuza suka manne wa sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.
3 Da Dawuda ya koma gidansa a Urushalima, kwarakwaran nan nasa guda goma waɗanda ya bar su tsaron gida ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya yi ta lura da su, amma bai shiga wurinsu ba. Haka suka zauna a keɓe, suna zaune kamar gwauraye.
4 Sa’an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mini mutanen Yahuza kafin kwana uku, kai kuma ka zo tare da su.”
5 Sai Amasa ya tafi ya kira mutanen Yahuza, amma ya makara, bai zo a lokacin da aka ƙayyade masa ba.
6 Dawuda kuma ya ce wa Abishai, “Sheba ɗan Bikri fa, zai ba mu wuya fiye da Absalom, sai ka ɗauki mutanena, ka bi sawunsa, don kada ya ci garuruwa masu garu har ya tsere mana.”
7 Sa’an nan mutanen Yowab, wato Keretiyawa da Feletiyawa, da dukan jarumawa, suka bi bayan Abishai. Suka fita daga Urushalima don su bi sawun Sheba, ɗan Bikri.
8 Sa’ad da suke a babban dutsen Gibeyon, Amasa ya zo ya tarye su. A lokacin nan Yowab yana saye da rigar yaƙi, ya sha ɗamara, yana kuma rataye da takobi a ɗamararsa. Da ya gabato, sai takobin ya faɗi.
9 Yowab ya ce wa Amasa, “Abokina kana lafiya?” Yowab kuma ya kama gemun Amasa da hannun dama don ya sumbace shi.
10 Amma Amasa bai lura Yowab yana da takobi a hannunsa ba. Yowab kuwa ya kirɓa masa takobin a ciki sau ɗaya, sai hanjin Amasa ya zuba ƙasa, ya mutu.
Sa’an nan Yowab da Abishai ɗan’uwansa suka bi sawun Sheba, ɗan Bikri.
11 Sai ɗaya daga cikin samarin Yowab ya tsaya kusa da gawar Amasa ya ce, “Duk wanda yake son Yowab da duk wanda yake goyon bayan Dawuda, ya bi Yowab.”
12 Gawar Amasa kuwa ta birkiɗe da jini tana a tsakiyar hanya. Da mutumin ya ga yadda dukan mutane suka tsaya, sai ya kawar da ita daga tsakiyar hanya zuwa cikin saura, ya rufe ta da tufa, gama dukan wanda ya ga gawar, sai ya ja, ya tsaya.
13 Sa’ad da aka kawar da ita daga kan hanya, dukan mutane kuwa suka bi Yowab domin su bi sawun Sheba ɗan Bikri.
14 Sai Sheba ya bibiya kabilan Isra’ila, har ya kai Abel-bet-ma’aka. Dukan dangin Beri kuwa suka taru suka bi shi zuwa cikin garin.
15 Dukan mutanen da suke tare da Yowab kuma suka zo suka kewaye shi cikin Abel-bet-ma’aka. Suka tula ƙasa a jikin garun garin, daidai da tsayinta, waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe garun.
16 Sai wata mace mai hikima ta yi kira daga cikin garin, ta ce, “Ji mana! A faɗa wa Yowab, ya zo nan, ina so in yi magana da shi.”
17 Da ya zo kusa da ita, sai macen ta ce, “Kai ne Yowab?”
Ya ce, “I, ni ne.”
Ta ce masa, “Ka kasa kunne gare ni.”
Ya ce, “Ina sauraronki.”
18 Ta ce, “A dā sukan ce, ‘A nemi shawara a Abel,’ gama a can ake raba gardama.
19 Garinmu lafiyayye ne, amintacce ne kuma a cikin Isra’ila. Me ya sa kake so ka hallaka garin? Kana so ka rushe abin da yake na Allah?”
20 Yowab ya ce, “Allah ya sawwaƙe! Ba zan lalatar ko in hallakar da birninku ba.
21 Ba haka ba ne, ni dai ina neman mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu, wanda ake ce da shi Sheba, ɗan Bikri. Shi ne ya tayar wa sarki Dawuda. Shi kaɗai za ku ba ni, ni kuwa zan janye daga garin.”
Macen kuwa ta ce wa Yowab, “To, za a jefar maka kansa ta kan garu.”
22 Macen ta tafi wurin dukan mutanen garin da wayo. Su kuwa suka yanke kan Sheba, ɗan Bikri, suka jefa wa Yowab. Sa’an nan Yowab ya busa ƙaho, suka janye daga garin. Kowa ya tafi gidansa. Yowab kuma ya koma Urushalima wurin sarki.
Fādawan Dawuda
23 Yowab shi ne shugaban dukan sojojin Isra’ila, Benaiya, ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato masu tsaro.
24 Adoniram shi ne shugaban aikin gandu, Yehoshafat, ɗan Ahilud, shi ne marubuci.
25 Shewa shi ne magatakarda. Zadok da Abiyata su ne firistoci.
26 Aira mutumin Yayir shi ne mashawarcin Dawuda.