Ramuwa don Gibeyonawa
1 A zamanin Dawuda aka yi yunwa shekara uku bi da bi. Dawuda kuwa ya roƙi Ubangiji. Sai Ubangiji ya ce masa, “Akwai alhakin jini a kan Saul da gidansa, domin ya kashe Gibeyonawa.”
2 (Gibeyonawa dai ba mutanen Isra’ila ba ne, su Amoriyawan da suka ragu ne, waɗanda Isra’ilawa suka rantse musu, cewa, ba za su kashe su ba. Amma Saul, saboda kishin da yake yi domin mutanen Isra’ila da Yahuza, ya nema ya kashe su duk.)
3 Dawuda kuwa ya kira Gibeyonawa ya ce musu, “Me zan yi muku, da me zan yi kafara, domin ku sa wa mutanen Ubangiji albarka?”
4 Gibeyonawa suka amsa suka ce, “Ba zancen azurfa ko zinariya yake tsakaninmu da Saul ko da gidansa ba. Ba kuma wani mutum muke so mu kashe daga cikin Isra’ila ba.”
Dawuda kuma ya tambaye su ya ce, “To, me kuke so in yi muku?”
5 Suka ce wa sarki, “Mutumin da ya karkashe mu, ya yi niyyar hallakar da mu, don kada mu kasance tare da Isra’ilawa ko’ina a cikin karkararsu.
6 Sai ka ba mu ‘ya’yansa maza bakwai domin mu rataye su a gaban Ubangiji a Gibeya a kan dutsen Ubangiji.”
Sarki kuwa ya ce, “To, zan bayar.”
7 Amma sarki ya ware Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, saboda rantsuwar da yake tsakaninsa da Jonatan, ɗan Saul.
8 Sai sarki ya sa aka kamo masa Armoni da Mefiboshet, ‘ya’yan Saul waɗanda Rizfa, ‘yar Aiya, ta haifa masa, da ‘ya’ya maza biyar na Adriyel, ɗan Barzillai, mutumin Abelmehola, waɗanda matarsa Merab ‘yar Saul ta haifa masa.
9 Sarki kuwa ya bai wa Gibeyonawa su. Sai suka rataye su a kan dutse a gaban Ubangiji. Su bakwai ɗin nan suka hallaka gaba ɗaya. An kashe su a farkon kakar sha’ir.
10 Rizfa kuwa, ‘yar Aiya, ta ɗauki algarara ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutsen. Ta zauna a wurin tun daga farkon kaka har zubar ruwan damuna da ya bugi gawawwakin. Ba ta bar tsuntsaye su sauka a kansu da rana ba, ko namomin jeji da dare.
11 Sa’ad da aka sanar wa Dawuda abin da Rizfa, ‘yar Aiya, ƙwarƙwarar Saul ta yi,
12 Dawuda ya tafi ya kwaso ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan daga wurin mutanen Yabesh a Gileyad. (Gama suka sace su daga dandalin Bet-sheyan, a inda Filistiyawa suka rataye su, a ranar da suka kashe Saul a Gilbowa.)
13 Daga can ne ya kwaso ƙasusuwan Saul da na Jonatan, suka kuma tattara ƙasusuwan waɗanda aka rataye.
14 Aka binne ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan a kabarin Kish, tsohon Saul, a Zela a ƙasar Biliyaminu. Aka aikata dukan abin da sarki ya umarta. Bayan haka Allah ya ji addu’arsu a kan ƙasar.
Abishai Ya Ceci Dawuda daga Ƙaton Mutum
15 Ana nan sai Filistiyawa suka kai wa Isra’ilawa yaƙi. Dawuda kuwa ya gangara tare da jama’arsa, suka yi yaƙi da Filistiyawa. Dawuda kuwa ya gaji.
16 Sai Ishbi-benob, ɗaya daga cikin Refayawa, gwarzayen nan, wanda nauyin mashinsa ya yi shekel ɗari uku na tagulla, yana kuma rataye da sabon takobi, ya zaci zai iya kashe Dawuda.
17 Abishai ɗan Zeruya kuwa, ya kawo wa Dawuda gudunmawa. Ya faɗa wa Bafilisten, ya kashe shi. Jama’ar Dawuda kuwa suka sa ya yi musu alkawari ba zai ƙara binsu zuwa wurin yaƙi ba. Suka ce, “Kai ne begen Isra’ila, ba mu so mu rasa ka.”
Jarumawan Dawuda sun Kashe Ƙattin Mutane
18 Bayan wannan kuma suka sāke yin yaƙi da Filistiyawa a Gab. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin gwarzayen.
19 Suka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gab, sai Elhanan, ɗan Yayir, mutumin Baitalami, ya kashe ɗan’uwan Goliyat na Gat, wanda girman gorar māshinsa ta yi kama da dirkar masaƙa.
20 An kuma yi wani yaƙi a Gat, inda aka sami wani ƙaton mutum wanda shi cindo ne, hannuwa da ƙafafu, wato yana da yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi kuma daga cikin zuriyar gwarzayen mutanen ne.
21 Sa’ad da ya nuna wa Isra’ilawa raini, Jonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda, ya kashe shi.
22 Waɗannan gwarzaye huɗu sun fito daga zuriyar gwarzayen Gat ne. Dawuda da mutanensa suka kashe su.