Waƙar Nasarar Dawuda
1 Wannan waƙa Dawuda ya raira wa Ubangiji sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun Saul da dukan sauran abokan gābansa, ya ce,
2 “Ubangiji ne mai cetona,
Shi ne ƙaƙƙarfar kagarata.
3 Allahna, shi ne kāriyata,
Ina zaune lafiya tare da shi.
Yana kāre ni kamar garkuwa,
Yana tsare ni, ya kiyaye ni.
Shi ne mai cetona.
4 Na yi kira ga Ubangiji,
Ya cece ni daga abokan gābana.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
5 Gama raƙuman ruwa na mutuwa sun kewaye ni,
Raƙuman ruwa na hallaka suna gangarawa ta kaina.
6 Mutuwa ta ɗaure ni da igiyoyinta da ƙarfi,
Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
7 A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji,
Na yi kira ga Allah domin taimako.
Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata,
Ya kasa kunne ga kukana na neman taimako.
8 “Sa’an nan duniya ta yi tangaɗi, ta girgiza,
Harsashin sararin sama ya yi makyarkyata, ya raurawa, saboda fushin Allah.
9 Hayaƙi ya fito daga kafafen hancinsa,
Harshen wuta mai cinyewa da garwashi mai ƙuna daga bakinsa.
10 Ya jā sararin sama baya ya sauko,
Da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.
11 Ya hau kerub, ya tashi sama,
Ya yi tafiya ta fikafikan iska.
12 Ya rufe kansa da duhu,
Gizagizai masu kauri cike da ruwa suna kewaye da shi,
13 Garwashi mai ci daga tsawar walƙiya a gabansa.
14 “Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama
Aka kuma ji muryar Maɗaukaki.
15 Ya harharba kibau, ya warwatsa magabtansa,
Da walƙiyoyin tsawa ya sa su gudu.
16 An bayyana ƙarƙashin teku a fili,
An tone tussan duniya,
Lokacin da Ubangiji ya yi wa abokan gāba tsautawa,
Ya yi musu ruri cikin fushi.
17 Daga Sama Ubangiji ya miƙo ya ɗauke ni,
Ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.
18 Ya kuɓutar da ni daga waɗanda suke ƙina,
Daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina!
19 Sa’ad da nake cikin wahala sun auka mini,
Amma Ubangiji ya kiyaye ni.
20 Ya taimake ni ya fisshe ni daga hatsari,
Ya cece ni domin yana jin daɗina.
21 “Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina,
Ya sa mini albarka domin ba ni da laifin kome.
22 Gama na kiyaye dokar Ubangiji,
Ban yi wa Allahna tayarwa ba.
23 Na kiyaye dukan dokokinsa,
Ban yi rashin biyayya ga umarnansa ba.
24 Ya sani ni marar laifi ne,
Na kiyaye kaina daga aikata mugunta.
25 Domin haka ya sāka mini bisa ga adalcina,
Gama ya sani ba ni da laifi.
26 “Kai, ya Ubangiji, amintacce ne ga waɗanda suke da aminci,
Nagari ne kuma ga waɗanda suke cikakku.
27 Mai Tsarki ne kai ga waɗanda suke tsarkaka,
Amma kana gāba da waɗanda suke mugaye.
28 Kakan ceci masu tawali’u,
Amma kakan ƙasƙantar da masu girmankai.
29 “Ya Ubangiji, kai ne haskena,
Kana haskaka duhuna.
30 Ka ba ni ƙarfi don in auka wa abokan gābana,
Da iko domin in murƙushe tsaronsu.
31 “Allahn nan cikakke ne ƙwarai,
Maganarsa tabbatacciya ce!
Kamar garkuwa yake
Ga dukan masu neman kiyayewarsa.
32 Ubangiji shi kaɗai ne Allah,
Allah ne kaɗai madogararmu.
33 Allahn nan shi ne mafaka, mai ƙarfi ne a gare ni,
Ya sa hanyata ta zama lafiyayyiya.
34 Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa,
Ya kiyaye ni a kan duwatsu.
35 Ya horar da ni domin yaƙi,
Domin in iya tausa baka mafi ƙarfi.
36 “Ya Ubangiji, ka kiyaye ni, ka cece ni,
Taimakonka ya sa na zama babba.
37 Ka hana a kama ni,
Ban kuwa taɓa faɗuwa ba.
38 Na runtumi abokan gābana, na kuwa hallaka su,
Ban tsaya ba sai da na kore su.
39 Na fyaɗa su ƙasa, ba su iya tashi ba,
Suna kwance warwar a ƙafafuna.
40 Ka ba ni ƙarfi domin yin yaƙi,
Nasara kuma a kan abokan gābana.
41 Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana,
Na hallaka waɗanda suke ƙina.
42 Suka nemi taimako, amma ba wanda zai cece su,
Suka yi kira ga Ubangiji, amma bai amsa musu ba.
43 Na murƙushe su, sun yi laushi kamar ƙura,
Na tattake su kamar caɓi a kan tituna, na kuwa watsar da su.
44 “Ka cece ni daga jama’ata mai tawaye,
Ka sa in yi mulkin al’ummai,
Mutanen da ban san su ba sun zama bayina.
45 Baƙi sun zo suna rusuna mini,
Sa’ad da suka ji ni suka yi mini biyayya.
46 Zuciyarsu ta karai,
Suka fito daga kagararsu suna rawar jiki.
47 “Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga mai tsaronsa!
Allah ne ƙaƙƙarfan Mai Cetona! Ku yi shelar girmansa!
48 Ya ba ni nasara a kan abokan gabana,
Ya sa mutane a ƙarƙashin mulkina,
49 Ya kuɓutar da ni daga hannun maƙiya.
Kai, ya Ubangiji, ka ba ni nasara a kan maƙiyana,
Ka tsare ni daga mutane masu zafin hali.
50 Domin wannan zan yi yabonka cikin al’ummai,
Zan raira yabbai gare ka.
51 Allah ya ba sarkinsa manya manyan nasarori,
Ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shi wanda ya zaɓa,
Wato ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”