Dawuda Ya Ƙidaya dukan Jama’a
1 Ubangiji kuwa ya husata da Isra’ilawa. Ya kuwa zuga Dawuda a kansu, ya ce, “Tafi ka ƙidaya jama’ar Isra’ila da ta Yahuza.”
2 Sai sarki ya ce wa Yowab da shugabannin sojojin su tafi cikin dukan kabilan Isra’ila, tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, su ƙidaya mutanen don ya san yawansu.
3 Amma Yowab ya ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya sa mutanenka su ƙaru har sau ɗari fiye da yadda suke, har ubangijina sarki ya gani da idonsa, amma me ya sa sarki yake so ya yi wannan abu?”
4 Amma maganar sarki ta rinjayi ta Yowab da ta sauran shugabannin sojojin. Yowab kuwa da sauran shugabannin sojojin suka tashi daga gaban sarki suka tafi su ƙidaya mutanen Isra’ila.
5 Suka haye Urdun suka fara daga Arower, da garin da yake tsakiyar kwarin zuwa Gad, har zuwa Yazar.
6 Sa’an nan suka zo Gileyad da Kadesh cikin ƙasar Hittiyawa, daga nan suka tafi Dan-ja’an. Daga Dan-ja’an kuma suka ratsa zuwa Sidon.
7 Suka tafi kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa, da na Ƙan’aniyawa. Daga can suka tafi ƙasar kudu ta Yahuza a Biyer-sheba.
8 Da suka gama ratsa dukan ƙasar, sai suka komo Urushalima bayan wata tara da kwana ashirin.
9 Yowab kuwa ya ba sarki yawan jimillar mutanen da aka samu. A Isra’ila an sami mutanen da suka isa yin yaƙi, su dubu ɗari takwas (800,000). A Yahuza kuwa an sami mutum dubu ɗari biyar (500,000).
10 Bayan da Dawuda ya ƙidaya mutane, sai lamirinsa ya kā da shi, ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka gafarta mini, gama na yi wauta.”
11 Da Dawuda ya tashi da safe, sai Ubangiji ya yi magana da annabi Gad, wato annabin da yake tare da Dawuda, ya ce,
12 “Tafi ka faɗa wa Dawuda na ba shi abu uku don ya zaɓi ɗaya wanda za a yi masa daga cikinsu.”
13 Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kuwa kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gabanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu sai ka yi tunani, ka faɗi irin amsar da zan mayar wa Ubangiji da ya aiko ni.”
14 Dawuda kuwa ya ce, “Na shiga uku, gara in faɗa a ikon Ubangiji, gama shi mai rahama ne, da in faɗa a ikon mutum.”
15 Ubangiji kuwa ya aika da annoba a kan Isra’ila tun da safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade. Mutum dubu saba’in (70,000) suka mutu daga Dan zuwa Biyer-sheba.
16 Sa’ad da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima don ya hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake hallakar da mutanen, “Ya isa, ka janye hannunka.” Mala’ikan ya tsaya kusa da masussukar Arauna Bayebuse.
17 Da Dawuda ya ga mala’ika wanda yake hallakar da mutanen, sai ya ce wa Ubangiji, “Na yi laifi, na aikata mugunta, amma me waɗannan tumaki suka yi? Ina roƙonka, ka hukunta ni da gidan ubana.”
18 A ran nan Gad ya koma wurin Dawuda ya ce masa, “Ka haura ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna Bayebuse.”
19 Dawuda kuwa ya haura bisa ga umarnin Ubangiji ta bakin Gad.
20 Da Arauna ya waiga, ya ga sarki da fādawansa suna zuwa wurinsa, sai ya tafi ya tarye su. Ya tafi ya rusuna a gaban sarki har ƙasa,
21 ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, me ya kawo ka?”
Sai Dawuda ya ce, “Don in sayi masussukarka ne domin in gina wa Ubangiji bagade, domin a kawar wa mutanen da annobar.”
22 Arauna kuwa ya ce wa Dawuda, “Bari ubangijina, sarki, ya karɓa, ya yi abin da yake so. Ga shanun nan domin hadayar ƙonawa, ga kuma itacen sussuka da karkiya domin itacen hadayar.”
23 Dukan waɗannan Arauna ya ba sarki. Ya kuma ce wa sarki, “Ubangiji Allahnka ya karɓa.”
24 Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, saye zan yi daga gare ka da tamani. Ba zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da abin da ban yi wahalarsa ba.” Dawuda ya sayi masussukar da shanu a bakin shekel hamsin na azurfa.
25 Sa’an nan ya gina wa Ubangiji bagade a wurin. Ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa masa addu’o’i saboda ƙasar. Aka kawar wa Isra’ila da annobar.