1 Gidan Saul da gidan Dawuda suka daɗe suna yaƙi da juna. Ƙarfin gidan Dawuda ya yi ta ƙaruwa, amma na gidan Saul ya yi ta raguwa.
‘Ya’ya Maza da aka Haifa wa Dawuda a Hebron
2 ‘Ya’ya maza da aka haifa wa Dawuda a Hebron ke nan, Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa ɗan farinsa, Amnon.
3 Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma’aka ‘yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.
4 Haggit ta haifa masa ɗansa na huɗu, Adonaija. Abital ta haifa masa ɗansa na biyar, Shefatiya.
5 Matarsa Egla ta haifa masa ɗansa na shida, Itireyam. Dukan waɗannan a Hebron ne aka haife su.
Abner ya Bi Dawuda
6 Abner ya ƙasaita sosai a gidan Saul a lokacin da ake yaƙi tsakanin jarumawan Saul da na Dawuda.
7 Saul yana da ƙwarƙwara mai suna Rizfa, ‘yar Aiya. Sai Ish-boshet ya ce wa Abner, “Me ya sa ka kwana da ƙwarƙwarar tsohona?”
8 Abner ya husata saboda wannan magana, ya ce, “Kana zato ni maci amanar ƙasa ne? Kana tsammani ina wa ƙasar Yahuza aiki ne? Tun da farko ina ta nuna alheri ga gidan Saul, tsohonka, da ‘yan’uwansa, da abokansa, ban kuwa ba da ka a hannun Dawuda ba. Amma ga shi, yau ka zarge ni da laifin kwartanci game da wannan mata.
9 Allah ya la’anta ni, idan ban yi wa Dawuda abin da Ubangiji ya rantse masa ba,
10 wato in mayar wa Dawuda da sarautar gidan Saul. In kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila da kan Yahuza tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba.”
11 Ish-boshet kuwa bai ce wa Abner uffan ba, don yana jin tsoronsa.
12 Sai Abner ya aiki manzanni zuwa wurin Dawuda a Hebron, ya ce, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi mini alkawari, ni kuwa zan goyi bayanka, in sa dukkan Isra’ilawa su bi ka.”
13 Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi maka alkawari a kan wannan sharaɗi, ba za ka ga fuskata ba sai ka kawo mini matata, Mikal, ‘yar Saul, sa’ad da za ka zo wurina.”
14 Sa’an nan Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-boshet, ɗan Saul, ya ce, “Ka ba ni matata, Mikal, wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari ta Filistiyawa.”
15 Sai Ish-boshet ya aika aka ƙwato Mikal daga wurin mijinta, Falti, ɗan Layish.
16 Mijinta ya bi ta yana ta kuka har zuwa Bahurim. Sai Abner ya ce masa ya koma, ya kuwa koma.
17 Abner ya shawarci dattawan Isra’ila, ya ce, “Dā ma can kuna so Dawuda ya sarauce ku.
18 To, yanzu sai ku yarda ya sarauce ku, gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta hannun bawana, Dawuda, zan ceci jama’ar Isra’ila daga hannun Filistiyawa, da na dukan abokan gābansu.’ ”
19 Abner kuma ya yi magana da mutanen Biliyaminu, sa’an nan ya tafi ya faɗa wa Dawuda a Hebron abin da dukan Isra’ilawa da dukan kabilar Biliyaminu suka ga ya yi kyau, su yi.
20 Abner tare da mutum ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda kuwa ya yi musu liyafa.
21 Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Zan tashi in tafi in tattara wa ubangijina sarki dukan Isra’ilawa, domin su yi alkawari da kai, kai kuma ka sarauce su yadda kake so.” Dawuda kuwa ya sallami Abner, ya tafi lafiya.
An Kashe Abner
22 Sai ga barorin Dawuda da Yowab sun komo daga hari. Sun kawo ganima mai yawa. Abner kuwa ya riga ya tafi, gama Dawuda ya riga ya sallame shi, ya tafi lafiya.
23 Da Yowab da sojojin da suke tare da shi suka iso, sai aka faɗa masa cewa, “Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya bar shi ya tafi lafiya.”
24 Sai Yowab ya tafi wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka, me ya sa ka bar shi ya tafi lafiya?
25 Ka sani Abner ɗan Ner ya zo ya ruɗe ka ne, ya san fitarka da shigarka, ya kuma san dukan abin da kake yi.”
26 Da Yowab ya fita daga wurin Dawuda, sai ya aiki manzanni su bi bayan Abner. Suka komo da shi a rijiyar Sira, amma Dawuda bai sani ba.
27 Sa’ad da Abner ya komo Hebron, sai Yowab ya raɓa da shi wajen ƙofar garin kamar zai gana da shi, sai ya soke shi a ruwan ciki, ya fāɗi ya mutu, saboda alhakin jinin ɗan’uwansa, Asahel.
28 Daga baya sa’ad da Dawuda ya ji, sai ya ce, “Ni da mulkina baratattu ne a gaban Ubangiji daga alhakin jinin Abner ɗan Ner har abada.
29 Allah ya sa alhakin jinin ya faɗa kan Yowab da dukan gidan ubansa. Ya sa kada a rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko wanda yake dogara sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko wanda ba shi da abinci, a gidan Yowab.”
30 Ta haka Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner saboda ya kashe ƙanensu, Asahel, a wurin yaƙi a Gibeyon.
31 Dawuda kuwa ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku kyakketa tufafinku, ku sa tsummoki, ku yi makoki domin Abner.” Sarki Dawuda kuwa ya bi bayan makara.
32 Suka binne Abner a Hebron. Sarki ya ta da murya ya yi kuka a kabarin Abner. Dukan mutane kuma suka yi kuka.
33 Sarki ya yi wannan makoki domin Abner, ya ce,
“Don me Abner zai mutu kamar wawa?
34 Hannuwansa ba a ɗaure suke ba,
Ƙafafunsa kuma ba a dabaibaye suke ba.
Ya mutu kamar wanda mugayen mutane suka kashe.”
Dukan mutane suka yi kuka kuma saboda shi.
35 Mutane kuwa suka zo su ba Dawuda magana, ko ya ci abinci tun rana ba ta faɗi ba. Amma Dawuda ya rantse ya ce, “Allah ya buge ni in mutu nan, idan na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta faɗi.”
36 Da mutanen suka lura, sai suka yarda da abin da sarki ya yi, suka kuma ji daɗin kowane abu da sarki ya yi.
37 A wannan rana dukan mutanen Dawuda da dukan mutanen Isra’ila suka gane, ashe, ba nufin Dawuda ba ne a kashe Abner ɗan Ner.
38 Sarki ya ce wa fādawansa, “Ba ku sani ba, basarake ne, babban mutum ne kuma ya faɗi a cikin Isra’ila yau?
39 Yau na raunana, ko da yake ni sarki ne naɗaɗɗe. Waɗannan mutane, ‘ya’yan Zeruya, sun fi ƙarfina, Ubangiji ya sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata.”