An Kashe Ish-boshet
1 Da Ish-boshet, ɗan Saul, ya ji labari Abner ya mutu a Hebron, sai gabansa ya faɗi. Dukan mutanen Isra’ila kuma suka tsorata.
2 Shi ɗan nan na Saul yana da shugabanni biyu na ‘yan hari, su ne Ba’ana da Rekab, ‘ya’yan Rimmon na ƙasar Biliyaminu daga Biyerot, (gama an lasafta Biyerot cikin yankin ƙasar Biliyaminu.
3 Mutanen Biyerot sun gudu zuwa Gittayim inda suke zaman baƙunci har wa yau.)
4 Jonatan, ɗan Saul kuwa, yana da ɗa, sunansa Mefiboshet, amma gurgu ne. Yana da shekara biyar sa’ad da aka kawo labarin mutuwar Saul da Jonatan daga Yezreyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi, ta sheƙa a guje. A sa’ad da take gudu sai ya faɗo, sanadin gurguntakar ke nan.
5 Rekab da Ba’ana ‘ya’yan Rimmon suka tafi gidan Ish-boshet da tsakar rana, a lokacin da yake shaƙatawa.
6 Rekab da Ba’ana kuwa, suka laɓaɓa, suka shiga kamar suna neman alkama.
7 Da suka shiga gidan, sai suka iske shi yana kwance a ɗakin kwanansa. Suka buge shi, suka kashe shi, suka datse kansa. Suka ɗauki kansa suka bi ta hanyar Araba, suka yi tafiya dare farai.
8 Suka kai wa Dawuda kan Ish-boshet a Hebron. Suka ce wa sarki Dawuda, “Ga kan Ish-boshet ɗan maƙiyinka, Saul, wanda ya nemi ranka. Ubangiji ya rama wa sarki a kan Saul da zuriyarsa yau.”
9 Amma Dawuda ya ce wa Rekab da Ba’ana, ‘ya’yan Rimmon, mutumin Biyerot, “Na rantse da Ubangiji wanda ya fanshe ni daga kowace masifa,
10 sa’ad da wani ya kawo mini labari cewa, ‘Saul ya mutu,’ mutumin ya yi tsammani albishir ne ya kawo mini, sai na kama shi na kashe shi a Ziklag. Ladan da na ba shi ke nan saboda labarinsa.
11 Balle fa ku da kuke mugayen mutane, da kuka kashe adali a gadonsa, a cikin gidansa, ba sai in nemi hakkin jininsa a hannunku ba, in kawar da ku daga duniya?”
12 Sai Dawuda ya umarci samarinsa su kashe su. Suka datsa hannunsu da ƙafafunsu, suka rataye su a gefen tafkin Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-boshet suka binne a cikin kabarin Abner a Hebron.