EZRA 1

Umarnin Sarki Sairus Yahudawa su Koma

1 Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.

2 Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza.

3 Duk wanda yake na mutanensa da yake nan Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima ta ƙasar Yahuza don ya sāke gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne Allah wanda ake masa sujada a Urushalima.

4 A duk inda akwai wani Bayahude, sai mutanen wurin su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da dabbobi, tare da waɗansu kyautai na yardar rai saboda Haikalin Ubangiji wanda yake a Urushalima.”

Komowar Kamammu zuwa Urushalima

5 Shugabannin gidajen kakanni na Yahuza kuwa, da na Biliyaminu, da firistoci, da Lawiyawa, da duk wanda Ubangiji ya taɓa shi, suka tashi don su tafi su sāke gina Haikalin Ubangiji wanda yake a Urushalima.

6 Dukan waɗanda suke kewaye da su, suka taimake su da azurfa, da zinariya, da kayayyaki, da dabbobi, da abubuwa masu daraja, da kyautai na yardar rai.

7 Sarki Sairus kuma ya fito da kayayyakin Haikalin Ubangiji, waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga Urushalima ya ajiye su a haikalin gumakansa.

8 Sairus Sarkin Farisa ya sa ma’aji, Mitredat, ya fito da kayayyakin, ya ƙidaya wa Sheshbazzar, shugaban Yahuza.

9 Yawan kayayyakin ke nan, kwanonin zinariya guda talatin, da kwanonin azurfa guda dubu (1,000), da wuƙaƙe guda ashirin da tara,

10 da finjalai na zinariya guda talatin, da tasoshi na azurfa ɗari huɗu da goma, da waɗansu kayayyaki guda dubu (1,000).

11 Jimillar kayayyakin duka, na zinariya da na azurfa, dubu biyar da arbaminya (5,400). Sheshbazzar ya tafi da waɗannan kayayyaki duka tare da kamammun da suka komo daga Babila.