FAR 14

Abram Ya ‘Yanto Lutu

1 A zamanin Amrafel Sarkin Shinar, shi da Ariyok Sarkin Ellasar, da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim,

2 suka fita suka yi yaƙi da Bera Sarkin Saduma, da Birsha Sarkin Gwamrata, da Shinab Sarkin Adma, da Shemeber Sarkin Zeboyim, da kuma Sarkin Bela, wato Zowar.

3 Waɗannan sarakuna biyar suka haɗa kai don su kai yaƙi, suka haɗa mayaƙansu a kwarin Siddim, inda Tekun Gishiri take.

4 Shekara goma sha biyu suka bauta wa Kedarlayomer, amma suka tayar a shekara ta goma sha uku.

5 A shekara ta goma sha huɗu Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi suka zo suka cinye Refayawa cikin Ashterotkarnayim, da Zuzawa cikin Ham, da Emawa cikin Filin Kiriyatayim,

6 da kuma Horiyawa cikin dutsen nan nasu, wato Seyir, har zuwa Elfaran a bakin jeji.

7 Sai suka juya suka je Enmishfat, wato Kadesh, suka kuwa cinye ƙasar Amalekawa da kuma ta Amoriyawa waɗanda suka zauna cikin Hazazontamar.

8-9 Sai Sarkin Saduma, da Sarkin Gwamrata, da Sarkin Adma da Sarkin Zeboyim, da Sarkin Bela, wato Zowar, suka fita suka ja dāga da Kedarlayomer Sarkin Elam, da Tidal Sarkin Goyim, da Amrafel Sarkin Shinar, da Ariyok Sarkin Ellasar a kwarin Siddim, sarakuna huɗu gāba da biyar.

10 Akwai ramummukan kalo da yawa a kwarin Siddim. Da Sarkin Saduma da na Gwamrata suka sheƙa da gudu sai waɗansunsu suka fāɗa cikin ramummukan, sauran kuwa suka gudu zuwa dutsen.

11 Sai abokan gāba suka kwashe dukan kayayyakin Saduma da na Gwamrata, da abincinsu duka, suka yi tafiyarsu.

12 Suka kuma kama Lutu ɗan ɗan’uwan Abram, wanda yake zaune a Saduma, da kayayyakinsa, suka yi tafiyarsu.

13 Sai wani da ya tsere, ya zo ya faɗa wa Abram Ba’ibrane wanda yake zaune wajen itatuwan oak na Mamre, Ba’amore, ɗan’uwan Eshkol da Aner, waɗanda suke abuta da Abram.

14 Lokacin da Abram ya ji an kama danginsa wurin yaƙi sai ya shugabanci horarrun mutanensa, haifaffun gidansa, su ɗari uku da goma sha takwas, suka bi sawun sarakunan har zuwa Dan.

15 Da dad dare sai ya kasa jarumawansa yadda za su gabza da su, shi da barorinsa, ya kuma ɗibge su, ya kore su har zuwa Hoba, arewacin Dimashƙu.

16 Sai ya washe kayayyakin duka, ya kuma ƙwato ɗan’uwansa Lutu da kayayyakinsa da mata da maza.

Malkisadik ya Sa wa Abram Albarka

17 Sai Sarkin Saduma ya fita ya taryi Abram sa’ad da ya komo daga korar Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi, a Kwarin Shawe, wato Kwarin Sarki.

18 Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki.

19 Ya kuwa sa wa Abram albarka ya ce, “Shi wanda ya yi sama da ƙasa, Allah Maɗaukaki ya sa wa Abram albarka.

20 Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!” Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka.

21 Sai Sarkin Saduma ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanen, amma ka riƙe kayayyakin don kanka.”

22 Amma Abram ya ce wa Sarkin Saduma, “Na riga na rantse wa Ubangiji Allah Maɗaukaki, wanda ya yi sama da ƙasa,

23 cewa ba zan ɗauki ko da zare ɗaya ko maɗaurin takalmi ba, ko kowane abin da yake naka, domin kada ka ce, ‘Na arzuta Abram.’

24 A ni kaina ba zan ɗauki kome ba illa abin da samari suka ci, da rabon mutanen da suka tafi tare da ni. Sai dai kuma Aner, da Eshkol, da Mamre su ɗauki nasu rabo.”