FAR 18

An Alkawarta Haihuwar Ishaku

1 Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ibrahim kusa da itatuwan oak na Mamre, a lokacin da yake zaune a ƙofar alfarwarsa da tsakar rana.

2 Da ya ɗaga idonsa, ya duba sai ga mutum uku suna tsaye a gabansa. Da ya gan su, sai ya sheƙa da gudu daga ƙofar alfarwar, don ya tarye su. Ya yi ruku’u,

3 ya ce, “Ya Ubangiji, in na sami tagomashi a gabanka, kada ka wuce gidana. A shirye nake in yi muku hidima.

4 Bari a kawo ɗan ruwa ku wanke ƙafafunku, ku shaƙata a gindin itace,

5 ni kuwa in tafi in kawo ɗan abinci, don rayukanku su wartsake, bayan haka sai ku wuce, tun da yake kun biyo ta wurin baranku.”

Sai suka ce, “Madalla! Ka aikata bisa ga faɗarka.”

6 Ibrahim kuwa ya gaggauta zuwa cikin alfarwa wurin Saratu, ya ce, “Ki shirya mudu uku na gari mai laushi da sauri, ki cuɗa, ki yi waina.”

7 Sai Ibrahim ya sheƙa zuwa garke, ya ɗauki maraƙi, matashi mai kyau, ya ba baransa, ya kuwa shirya shi nan da nan.

8 Ya ɗauki kindirmo da madara, da maraƙin da ya shirya, ya ajiye a gabansu, ya tsaya kusa da su a gindin itacen a sa’ad da suke ci.

9 Suka ce masa, “Ina Saratu matarka?”

Ya ce, “Tana cikin alfarwa.”

10 Baƙon ya ce, “Na yi maka alkawari matarka Saratu za ta haifi ɗa a wata na tara nan gaba. Zan sāke zuwa a lokacin.” Saratu kuwa tana ƙofar alfarwa, a bayansu, tana kasa kunne.

11 Ga shi kuwa, Ibrahim da Saratu sun tsufa, sun kwana biyu, gama Saratu ta daina al’adar mata.

12 Sai Saratu ta yi dariya a ranta, tana cewa, “Bayan na tsufa mai gidana kuma ya tsufa sa’an nan zan sami wannan gatanci?”

13 Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya, har da ta ce, ‘Ashe zan haifi ɗa, a yanzu da na riga na tsufa?’

14 Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”

15 Amma Saratu ta yi mūsu, tana cewa, “Ai, ban yi dariya ba,” Gama tana jin tsoro.

Ya ce, “A’a, hakika kin yi dariya.”

Ibrahim ya Yi Roƙo don Saduma

16 Sai mutanen suka tashi daga wurin, suka fuskanci Saduma, Ibrahim kuwa ya yi musu rakiya ya sallame su.

17 Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin aikatawa?

18 Ga shi kuwa, Ibrahim zai ƙasaita ya zama al’umma mai iko, sauran al’umman duniya duka za su sami albarka ta dalilinsa.

19 Gama na zaɓe shi don ya umarci ‘ya’yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari’a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.

20 Sai kuma Ubangiji ya ce, “Tun da yake kuka a kan Saduma da Gwamrata ya yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni ƙwarai,

21 zan sauka in gani ko sun aikata kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”

22 Sa’an nan mutanen suka juya daga nan, suka nufi Saduma, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Ubangiji.

23 Sai Ibrahim ya matso kusa, ya ce, “Ashe, za ka hallaka adali tare da mugun?

24 Da a ce, akwai masu adalci hamsin cikin birnin, za ka hallaka wurin, ba za ka yafe su saboda masu adalcin nan hamsin waɗanda suke cikinsa ba?

25 Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”

26 Sai Ubangiji ya ce, “In na sami adalai hamsin a cikin birnin Saduma, zan yafe wa dukan wurin sabili da su.”

27 Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka.

28 Da a ce za a rasa biyar daga cikin adalai hamsin ɗin, za ka hallaka birnin duka saboda rashin biyar ɗin?”

Sai ya ce, “Ba zan hallaka shi ba in na sami arba’in da biyar a wurin.”

29 Ya kuma sāke yin masa magana, ya ce, “Da a ce za a sami arba’in a wurin fa?”

Ya amsa ya ce, “Sabili da arba’in ɗin ba zan yi ba.”

30 Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan yi magana. Da a ce za a sami talatin a wurin fa?”

Ya amsa, “Ba zan yi ba, in na sami talatin a wurin.”

31 Ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji. Da a ce za a sami ashirin a wurin fa?”

Ya amsa ya ce, “Sabili da ashirin ɗin ba zan hallaka shi ba.”

32 Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan sāke yin magana, sau ɗayan nan kaɗai. Da a ce za a sami goma a wurin fa?”

Ya amsa ya ce, “Sabili da goma ɗin ba zan hallaka shi ba.”

33 Ubangiji kuwa ya yi tafiyarsa, bayan ya gama magana da Ibrahim. Ibrahim kuwa ya koma gida.