FAR 2

1 Da haka aka gama yin sama da duniya, da rundunansu.

2 A kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa wanda ya yi. Ya kuwa huta a kan kwana na bakwai daga dukan aikinsa da ya yi.

3 Domin haka Allah ya sa wa kwana na bakwai albarka, ya tsarkake shi, don a cikinsa Allah ya huta daga dukan aikin da ya yi na halitta.

4 Waɗannan su ne asalin sama da duniya sa’ad da aka halicce su.

A ranar da Ubangiji Allah ya yi duniya da sama,

5 a sa’an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar,

6 amma sai ƙāsashi yake tasowa daga ƙasa ya shayar da fuskar ƙasa duka.

7 Sa’an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.

Gonar Aidan

8 Ubangiji Allah kuwa ya dasa gona a Aidan, wajen gabas, a can ya sa mutumin da ya siffata.

9 Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.(Far 3.22,24; W. Yah 2.7; 22.2,14,19; Eze 47.12

10 Wani kogi kuma ya malalo daga Aidan ya shayar da gonar, daga nan kuwa ya rarrabu ya zama kogi huɗu.

11 Sunan na fari Fishon, shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.

12 Zinariyar ƙasan nan kuwa kyakkyawa ce. Akwai kuma duwatsu masu daraja a wurin.

13 Sunan kogi na biyu Gihon, shi ne wanda yake malala kewaye da ƙasar Kush.

14 Sunan kogi na uku Taigiris ne, wanda yake malala gabashin Assuriya. Kogi na huɗu kuwa Yufiretis ne.

15 Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta.

16 Ubangiji Allah ya yi wa mutumin umarni, ya ce, “Kana da ‘yanci ka ci daga kowane itace da yake a gonar,

17 amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.”

18 Sa’an nan sai Ubangiji Allah ya ce, “Bai kyautu mutumin ya zauna shi kaɗai ba, zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

19 Haka nan fa, daga cikin ƙasar, Ubangiji ya siffata kowace dabba ta cikin saura da kowane tsuntu na sararin sama, ya kawo su wurin mutumin, ya ga yadda zai kiraye su, duk abin da mutumin ya kirayi mai ran kuwa, sunansa ke nan.

20 Mutumin ya bai wa dabbobi duka suna, da tsuntsayen sararin sama, da kowace irin dabba da take cikin saura, amma ba a sami mataimaki wanda ya dace da mutumin ba.

21 Sai Ubangiji Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin. Lokacin da yake barci Ubangiji Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya cike wurin da nama,

22 haƙarƙarin nan kuwa da Ubangiji Allah ya cire daga mutumin ya yi mace da shi, ya kuwa kawo ta ga mutumin.

23 Sai mutumin ya ce, “Yanzu dai wannan ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne kuwa daga namana, za a kira ta mace, don daga cikin mutum aka ciro ta.”

24 Domin haka mutum yakan rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuwa manne wa matarsa, sun zama ɗaya.

25 Da mutumin da matarsa dukansu biyu a tsiraice suke, ba su kuwa ji kunya ba.