FAR 20

Ibrahim da Abimelek

1 Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi zuwa wajen karkarar Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. A lokacin da Ibrahim yake baƙunci a Gerar,

2 ya ce, matarsa Saratu ‘yar’uwarsa ce. Sai Abimelek Sarkin Gerar ya aika, aka ɗauko masa Saratu.

3 Amma Allah ya zo wurin Abimelek cikin mafarki da dad dare ya ce masa, “Mutuwa za ka yi saboda matar da ka ɗauko, gama ita matar wani ce.”

4 Abimelek bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ubangiji, za ka hallaka marar laifi?

5 Ba shi ya faɗa mini, ‘Ita ‘yar’uwata ce’ ba? Ba ita kanta kuma ta ce, ‘Shi ɗan’uwana ne’ ba? Cikin mutunci da kyakkyawan nufi na aikata wannan.”

6 Allah ya ce masa cikin mafarki, “I, na sani ka yi wannan cikin mutunci, ai, ni na hana ka ka aikata zunubin, don haka ban yarda maka ka shafe ta ba.

7 Yanzu fa, sai ka mayar wa mutumin da matarsa, gama shi annabi ne, zai yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In kuwa ba ka mayar da ita ba, ka sani hakika za ka mutu, kai, da dukan abin da yake naka.”

8 Abimelek ya tashi da sassafe, ya kira barorinsa duka ya kuma faɗa musu waɗannan abubuwa duka. Mutanen kuwa suka ji tsoro ƙwarai.

9 Abimelek kuwa ya kira Ibrahim, ya ce masa, “Me ke nan ka yi mana? Wane laifi na yi maka, da za ka jawo bala’i mai girma haka a kaina da mulkina? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba.”

10 Abimelek kuma ya ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan abu?”

11 Ibrahim ya ce, “Na yi haka, domin ina zaton babu tsoron Allah ko kaɗan a wannan wuri, shi ya sa na zaci, kashe ni za a yi saboda matata.

12 Banda haka nan ma, hakika ita ‘yar’uwata ce, ‘yar mahaifina amma ba ta mahaifiyata ba ce. Na kuwa aure ta.

13 A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawace yawace, na ce mata, ‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan’uwanki ne.’ ”

14 Abimelek ya ɗauki tumaki da takarkarai, da bayi mata da maza, ya ba Ibrahim, ya kuma mayar masa da matarsa Saratu.

15 Abimelek kuwa ya ce, “Ga shi, ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda ya yi maka daɗi.”

16 Ga Saratu kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ɗan’uwanki azurfa guda dubu, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa, cewa ba ki da laifi.”

17 Ibrahim ya yi addu’a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa.

18 Gama dā Allah ya kulle mahaifar dukan gidan Abimelek saboda Saratu matar Ibrahim.