FAR 29

Yakubu Ya Isa Gidan Laban

1 Yakubu kuwa ya ci gaba da tafiyarsa, har ya kai ƙasar Mesofotamiya.

2 Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba.

3 A sa’ad da garkunan suka tattaru a wurin, makiyayan sukan kawar da dutsen daga bakin rijiyar, su shayar da su, sa’an nan su mayar da dutsen a wurinsa, a bisa bakin rijiya.

4 Yakubu ya ce musu, “’Yan’uwana, daga ina kuka fito?”

Suka ce, “Daga Haran muke.”

5 Sai ya ce musu, “Kun san Laban ɗan Nahor?”

Suka ce, “Mun san shi.”

6 Ya ce musu, “Lafiyarsa ƙalau?”

Suka ce, “I, lafiya ƙalau yake, ga ma Rahila ‘yarsa, tana zuwa da bisashensa!”

7 Ya ce, “Ga shi kuwa, da sauran rana da yawa, lokacin tattaruwar dabbobi bai yi ba, me zai hana ku shayar da tumakin, ku sāke kai su wurin kiwo?”

8 Amma suka ce, “Ba za mu iya ba, sai sauran garkunan duka sun taru, sa’an nan a kawar da dutsen daga bakin rijiyar, sa’an nan mu shayar da garkuna.”

9 Kafin ya rufe baki, sai ga Rahila ta zo da bisashen mahaifinta, gama ita take kiwonsu.

10 Sa’ad da Yakubu ya ga Rahila, ‘yar Laban kawunsa, da bisashen, sai Yakubu ya hau ya kawar da dutsen daga bakin rijiyar, ya shayar da garken Laban, kawunsa.

11 Yakubu kuwa ya sumbaci Rahila, ya fara kuka da ƙarfi.

12 Ya faɗa mata shi dangin mahaifinta ne, shi kuma ɗan Rifkatu ne, sai ta sheƙa ta faɗa wa mahaifinta.

13 Sa’ad da Laban ya sami labari a kan Yakubu ɗan ‘yar’uwarsa, sai ya sheƙo ya tarye shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kawo shi a gidansa. Yakubu ya labarta wa Laban al’amura duka.

14 Laban ya ce masa, “Hakika, kai ƙashina ne da namana!” Yakubu ya zauna wata guda tara da Laban.

Yakubu Ya Yi wa Laban Barantaka domin Rahila da Lai’atu

15 Laban kuwa ya ce wa Yakubu, “Don kana dangina, za ka yi mini barantaka a banza? Ka faɗa mini, nawa zan biya ka?”

16 Laban dai yana da ‘ya’ya mata biyu, sunan babbar Lai’atu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.

17 Lai’atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya.

18 Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin ‘yarka Rahila.”

19 Laban ya ce, “Gara in ba ka ita da in ba wani dabam, zauna tare da ni.”

20 Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar ‘yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.

21 Yakubu ya ce wa Laban, “Ba ni matata domin in shiga wurinta, domin lokacin da muka shirya ya cika.”

22 Sai Laban ya tattara mutanen wurin duka, ya yi biki.

23 Amma da maraice, ya ɗauki ‘yarsa Lai’atu ya kawo ta wurin Yakubu, Yakubu ya shiga a wurinta.

24 (Laban ya ba ‘yarsa Lai’atu Zilfa ta zama kuyangarta).

25 Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai’atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”

26 Laban ya ce, “A nan wurinmu ba a yin haka, a aurar da ƙarama kafin ‘yar fari.

27 Ka jira, bayan kwana bakwai na lokacin auren sun wuce, sa’an nan za mu ba ka Rahila saboda barantakar da za ka yi mini shekara bakwai nan gaba.”

28 Yakubu kuwa ya yi haka ɗin, ya cikasa makon, sa’an nan Laban ya aurar masa da ‘yarsa Rahila.

29 (Laban ya ba ‘yarsa Rahila Bilha, kuyangarsa, ta zama kuyangarta).

30 Sai Yakubu ya shiga wurin Rahila, amma ya fi ƙaunar Rahila da Lai’atu. Ya yi wa Laban barantaka waɗansu shekara bakwai kuma.

An Haifa wa Yakubu ‘Ya’ya

31 Sa’ad da Ubangiji ya ga ana ƙin Lai’atu, ya buɗe mahaifarta, amma Rahila bakarariya ce.

32 Lai’atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra’ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”

33 Ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Saboda Ubangiji ya ji ana ƙina ya ba ni wannan ɗa kuma,” ta kuwa raɗa masa suna Saminu.

34 Sai kuma ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Yanzu, a wannan karo mijina zai shaƙu da ni , domin na haifa masa ‘ya’ya uku maza.” Saboda haka ta raɗa masa suna Lawi.

35 Har yanzu kuwa ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta raɗa masa suna Yahuza. Daga nan sai ta daina haihuwa.