FAR 31

Yakubu ya Gudu daga wurin Laban

1 Yakubu ya ji ‘ya’yan Laban suna cewa, “Yakubu ya kwashe dukan abin da yake na mahaifinmu, daga cikin dukan abin da yake na mahaifinmu kuma ya sami dukiyarsa.”

2 Yakubu kuma ya ga ba shi da farin jini a wurin Laban kamar dā.

3 Ubangiji ya ce wa Yakubu, “Ka koma ƙasar kakanninka da danginka, ni kuwa ina tare da kai.”

4 Saboda haka Yakubu ya aika a kirawo Rahila da Lai’atu zuwa cikin saura inda garkensa yake,

5 ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni.

6 Kun sani na yi wa mahaifinku barantaka da dukan ƙarfina,

7 duk da haka mahaifinku ya cuce ni, ya yi ta sassauya ladana har sau goma, amma Allah bai ba shi ikon zambatata ba.

8 In ya ce, ‘Dabbare-dabbare, su ne ladanka,’ duk garken sai ya haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce ‘masu sofane ne ladanka,’ sai garken duka ya haifi masu sofane.

9 Ta haka Allah ya kwashe dukiyar mahaifinku ya ba ni.

10 “A lokacin ɗaukar cikin garke, cikin mafarki na ta da idanuna, na kuwa gani cikin mafarkin, bunsuran da suke hawan garken, masu sofane, da dabbare-dabbare da roɗi-roɗi ne.

11 Sai mala’ikan Allah ya ce mini a cikin mafarki, ‘Yakubu,’ sai na ce, ‘Ga ni.’

12 Ya kuwa ce, ‘Ta da idanunka ka gani, dukan bunsuran da suke hawan awaki masu sofane ne, dabbare-dabbare da roɗi-roɗi, gama na ga dukan abin da Laban yake yi maka.

13 Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa dutsen mai, ka kafa shi al’amudi, ka kuma rantse mini. Yanzu fa tashi ka fita daga cikin ƙasan nan, ka koma ƙasar haihuwarka.’ ”

14 Rahila da Lai’atu suka amsa masa, “Akwai wani rabo, ko gādon da ya rage mana a cikin gidan mahaifinmu?

15 Ba ga shi ma, sai kamar baƙi yake ɗaukarmu ba? Gama ya sayar da mu, yana kuwa morar kuɗin da aka bayar dominmu.

16 Dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga wurin mahaifinmu, tamu ce da ‘ya’yanmu, yanzu fa, kome Allah ya faɗa maka, sai ka yi.”

17 Sai Yakubu ya tashi, ya ɗauki ‘ya’yansa, da matansa a bisa raƙumansa,

18 ya kora shanunsa duka, da dukan bisashen da ya samu, da shanu da suke nasa, waɗanda ya samu a Fadan-aram a ƙasar Mesofotamiya, zuwa ƙasar Kan’ana wurin mahaifinsa Ishaku.

19 Amma a sa’an nan Laban ya riga ya tafi ya yi wa tumakinsa sausaya, sai Rahila ta sace gumakan gidan mahaifinta.

20 Yakubu kuwa ya yaudari Laban Ba’aramiye da bai sanar da shi zai gudu ba.

21 Ya gudu da dukan abin da yake da shi, ya tashi ya haye Yufiretis, ya miƙe zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.

Laban ya Bi Sawun Yakubu

22 Sa’ad da aka sanar da Laban, cewa Yakubu ya gudu da kwana uku,

23 sai ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi sawunsa har kwana bakwai, yana biye da shi kurkusa har zuwa ƙasar Gileyad ta tuddai.

24 Amma Allah ya zo wurin Laban Ba’aramiye cikin mafarki da dad dare, ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.”

25 Sai Laban ya ci wa Yakubu. A yanzu Yakubu ya riga ya kafa alfarwarsa a ƙasa ta tuddai, Laban da danginsa kuma suka yi zango a ƙasar Gileyad ta tuddai.

26 Laban ya ce wa Yakubu, “Me ka yi ke nan, da ka cuce ni, ka gudu da ‘ya’yan matana kamar kwason yaƙi?

27 Me ya sa ka gudu a ɓoye? Ka cuce ni, ba ka kuwa faɗa mini ba, ai, da na sallame ka da farin ciki, da waƙe-waƙe, da kiɗa, da garaya.

28 Don me ba ka bari na sumbaci ‘ya’yana mata da maza na yi bankwana da su ba? Kai! Ka yi aikin wauta.

29 Ina da iko in yi maka lahani, amma Allah na mahaifinka, ya yi magana da ni a daren jiya, yana cewa, ‘Ka kula fa kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.’

30 Amma yanzu, ka gudu domin kana kewar gidan mahaifinka ƙwarai, amma don me ka sace mini gumakana?”

31 Yakubu ya amsa wa Laban, ya ce, “Domin na ji tsoro ne gama na yi zaton za ka ƙwace ‘ya’yanka mata ƙarfi da yaji.

32 Ga duk wanda ka iske gumaka a wurinsa, a kashe shi. Yanzu a nan gaban danginmu, ka nuna abin da nake da shi wanda yake naka, ka ɗauka.” Ashe, Yakubu bai sani Rahila ce ta sace su ba.

33 Laban ya shiga alfarwar Yakubu, da ta Lai’atu, da na kuyangin nan biyu, amma bai same su ba. Sai ya fita daga alfarwar Lai’atu, ya shiga ta Rahila.

34 Ashe, Rahila ta kwashe gumakan ta zuba su cikin sirdin raƙumi, ta zauna a kansu. Laban ya wawaka alfarwar duka, amma bai same su ba.

35 Sai ta ce wa mahaifinta, “Kada ubangijina ya yi fushi da ban iya tashi ba, don ina al’adar mata ne.” Ya kuwa bincike, amma bai sami gumakan ba.

36 Yakubu ya husata, ya yi wa Laban faɗa, ya ce wa Laban, “Wane laifi na yi, mene ne zunubina da ka tsananta bina?

37 Ko da yake ka wawaka dukan kayayyakina, me ka samu na gumakanka a ciki? A tabbatar a nan yau a gaban dangina da danginka, su yanke shari’a tsakanina da kai.

38 Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba.

39 Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna.

40 Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci.

41 A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin ‘ya’yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma.

42 Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”

Yarjejeniya Tsakanin Yakubu da Laban

43 Sa’an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “’Ya’ya mata, ‘ya’yana ne, ‘ya’yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan ‘ya’ya mata nawa, ko kuma ga ‘ya’yan da suka haifa?

44 Zo mana mu ƙulla alkawari, da ni da kai, bari ya zama shaida tsakanina da kai.”

45 Saboda haka Yakubu ya ɗauki dutse ya kafa shi al’amudi.

46 Yakubu ya ce wa iyalinsa, “Ku tattara duwatsu.” Sai suka ɗauki duwatsu, suka tsiba, suka kuwa ci abinci kusa da tsibin.

47 Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed.

48 Laban ya ce, “Wannan tsibi shaida ce tsakanina da kai yau.” Saboda haka ya sa wa wurin suna Galeyed.

49 Laban kuma ya kira wurin Mizfa, gama ya ce, “Ubangiji ya kiyaye tsakanina da kai sa’ad da muka rabu da juna.

50 Idan ka wulakanta ‘ya’yana mata, ko kuma ka auri wata mata banda ‘ya’yana mata, ko da yake babu kowa tare da mu, ka tuna, Allah shi ne mashaidi tsakanina da kai.”

51 Sai Laban ya ce wa Yakubu, “Dubi wannan tsibi da al’amudi, wanda na kafa tsakanina da kai.

52 Wannan tsibi, shaida ce, al’amudin kuma shaida ce ba zan zarce wannan tsibi zuwa wurinka ba, kai kuma ba za ka zarce wannan tsibi da wannan al’amudi zuwa wurina don cutarwa ba.

53 Allah na Ibrahim da Nahor, Allah na mahaifinsu, ya shara’anta tsakaninmu.” Saboda haka Yakubu ya rantse da martabar mahaifinsa Ishaku.

54 Yakubu kuwa ya miƙa hadaya a bisa dutsen, ya kirawo iyalinsa su ci abinci, suka kuwa ci abinci suka zauna dukan dare a bisa dutsen.

55 Da sassafe, Laban ya tashi ya sumbaci jikokinsa, da ‘ya’yansa mata, ya sa musu albarka. Sa’an nan ya tashi ya koma gida.